United na harin ƴan wasan Bournemouth biyu, Munich na son Gordon

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na sa ido kan ƴan wasan Bournemouth Junior Kroupi, da mai tsaron bayan Argentine Marcos Senesi. (Mail - subscription needed)

Bayern Munich na son ɗaukar ɗan wasan Newcastle Anthony Gardon. (Talksport)

Aston Villa sun nuna sha'awar ɗauko mai tsaron ragar IngilaJames Trafford. dan wasan ya shiga kwantaragi da Manchester United ne a kakar wasan da ta gabata, sai dai suka hanzarta maye gurbinsa da Gianluigi Donnarumma. (Mail)

Liverpool na son ɗauakr Bazoumana Toure a kakar wasa. Ɗan wasan mai shekaru 20 ya yi nasarar hayewa tare da Hoffenheim a kakar wasanin bana, da zai ƙara ingnata tsaron bayan Liverpool, da ke fama da koma baya. (TeamTalk)

Ɗan wasan baya na Liverpool Ibrahima Konate na dab da amincewa da sabuwar kwantaragin na ci gaba da zama a Anfield. Ana sa ran ɗan wasan zai bar ƙungiyar ne a kakar wasannin nan, sai dai ana kyautata zaton cewar zai iya tsawaita zamansa a kungiyar da shekaru huɗu. (RMC)

Ɗan wasan bayan Borussia Dortmund Nico Schlotterbeck, ya bayana farashi biyu wato Fam miliyan 43 da miliyan 52, amma ga ƙungiyoyi uku, da ke son daukar ɗan wasan, wanda suka haɗa da Liverpool da Real Madrid, sai dai banda Bayern Munich.(Bild - in German)

Napoli na son tsawaita kwantaragijn ɗan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay, gabanin kakar gasar cin kofin duniya.ɗan wasan ya zama ɗan gaban goshin Naples tun bayan da ya koma Manchester United a 2024. (Il Mattino - In Italian)

Ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, ya zama wajibi ya amince da tayin rage albashinsa, idan yana son komawa Borussia Dortmund, inda kwantaraginsa ya ƙare da Manchester United a kakar wasanin nan. (Mirror)

Bournemouth na duba yiwuwar ɗaukar mai horar da ƴan wasan Rayo Vakecano , da na Coventry City Frank Lampard, da na Ipswich Town Kieran Mckenna, a yunƙurin da suke yi na maye gurbin Andoni Iraola, da ke shirin barin ƙungiyar a ƙarshen kakar nan. (i Sport)

Ɗan wasa Marco Rose, da ya rasa aikinsa a Liepzig, na cikin jerin ƴan wasna da ke kan gaba wajen maye gurbin Iraola da ke Bournemouth. (Guardian)

Ɗan wasan Ipswich McKenna na cikin ƴan wasan da Bournemouth ke hari wajen ganin ya maye gurbin Iraola da ke shirin barin ƙungiyar a kakar nan, sai dai ana duba wasu daga cikin ƴan wasan. (Athletic)

Ɗan wasan baya na Argentine Cristian Romero, akwai yiwuwar ya buga wasan sa na ƙarshe da Tottenham Hotspur, sakamakon ƙungiyar na yiwa yan wasan su garanbawul idan suka ci gaba da zama a ƙungiyar. (Talksport)

Mai horar da ƴan wasan Coventry City Frank Lampard ya kagu ya ɗauko ɗan wasan gaba na Chelsea Jesse Derry a kakar wasa mai zuwa. (Talksport)