Yaƙin Iran - An kai harin farko kan jirgin ruwa sama da kwana 10
Ƙungiyar Burtaniya da ke lura da amincin jiragen kasuwanci a teku (UKMTO) tace wasu jiragen ruwan yaƙin Iran biyu sun buɗe wuta kan wasu jiragen dakon mai a mashigar Hormuz, yayin da wani jirgin sunduƙai shima aka hare shi, sai dai ba a san wanda ya kai masa harin ba.
Kungiyar tsaron ta ba da rahoton kai hari kan jirgin ruwa ne a tekun Gulf a ranar 7 ga watan nan na Afrilu, yayin da wasu jirage suka hare shi waɗanda ba a san ko na wanene ba, abin da ya haifar da gobara a cikin jirgin.
A dai ranar kuma an sake kai wa wani jirgi hari, wanda shi ma ba a san wanda ya kai shi ba, a yankin kudancin tsibirin Kishi da ke Iran.
A ranar 1 ga watan Maris ne ƙungiyar UKMTO ta fara bayar da rahoton kai hari kan jirage.
A ranar 14 ga watan Afrilu ta ce an kai hare-hare 18 kan jirage daban-daban tsakankin mashigar Hormuz da Gilf da kuma tekun Oman.
Amma duka hare-haren da suka faru guda 30 ne ya zuwa yanzu in ji ta.