Najeriya ta zargi gwamnatin Mozambique da take haƙƙin ‘yan kasarta bayan kama su tare da tsare su, sannan daga bisani ta fitar da su daga ƙasar.
Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCOM) ta ce an kama mutanen tare da korarsu ba tare da bin ƙa’idojin doka ba, inda ta bayyana yadda aka yi musu a matsayin take haƙƙin ɗanadam da kuma karya dokokin ƙasa da ƙasa da ke kare baƙi.
Hukumar ta kuma ce jami’an Mozambique ba su tuntuɓi ofishin jakadancin Najeriya da ke Maputo ba, duk da ƙoƙarin da jami’an diflomasiyya suka yi na shiga tsakani.
Jami’an Mozambique sun ce kamen wani ɓangare ne na aikin yau da kullum na kula da shige da fice a babban birnin ƙasar, Maputo, amma ba su fitar da cikakken bayani kan zargin da Najeriya ke yi wa ƙasar ba.
Najeriya da Mozambique na da kyakkyawar alaƙar diflomasiyya tun shekaru da dama, inda suke haɗin gwiwa a ƙarƙashin ƙungiyar Tarayyar Afirka kan harkokin kasuwanci da gudun hijira da zaman lafiya a yankin.
Sai dai irin waɗannan al’amura na iya haifar da tsaiko a dangantaka, musamman ganin yadda Najeriya ke ƙoƙarin kare haƙƙin ‘yan kasarta a ƙasashen waje.
NiDCOM ta tabbatar da cewa daga cikin ‘yan Najeriya 42 da aka kama a farkon watan nan, an riga an fitar da 40 zuwa gida yayin da mutum biyu ke ci gaba da zama a Mozambique.
Mai magana da yawun NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya ce an kama mutanen ne a wuraren kasuwancinsu ba tare da la’akari da cewa suna da ingantattun takardun zama da aiki ba.
Ana sa ran ma’aikatar harkokin wajen Najeriya za ta ɗauki batun ta hanyoyin diflomasiyya, yayin da ake kira da a samar da kariya mai ƙarfi ga ‘yan Afirka da ke rayuwa da aiki a wasu ƙasashen nahiyar.