Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 19 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Isiyaku Muhammed

  1. Bai kamata kasashen Musulmi su bar Iran ita kadai ba - Taliban

    Ministan harkokin 'yan gudun hijra na kasar Afghanistan, Mohammed Kabir, ya ce abin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya "abin takaici ne kwarai" kuma gwamnatinsu ta yi alawadai da hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai wa Iran.

    Ministan wanda ya bayyana hakan ya yi wani bikin Idin sallah karama wanda aka gayyaci jami'an diflomasiyya ciki har da jakadan Iran, ya ce dole ne kasashen Musulmai su nuna damuwarsu kan abin da ake yi wa Iran domin yaki ya shafi zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya da ma Musulunci.

    Da ma dai a ranar Talata sai da ministan harkokin wajen na Afghanistan, Amir Khan Muttaqi ya yi kira ga Iran da ta yaki kasashen Gabas ta Tsakiya wadanda ke mara wa Amurka baya.

  2. Ba za mu aike da sojoji zuwa Iran ba - Trump

    Donald Trump ya ci gaba da nanata cewa Amurka da Isra'ila sun gama da sojojin ruwa da na sama da jagororin Iran.

    "Mun gama da komai, in ji Trump sannan ya ci gaba da cewa "nasarar ta ma wuce abin da muka tsammata".

    Da kuma aka tambayi Trump ko yana da shirin aikewa da sojoji zuwa yankin sai ya amsa da cewa babu inda za mu kai sojojinmu.

    Koma dai Tump din yana da wannan shirin ya shaida wa dan jaridar cewa "ba zan fada maka ba".

  3. Chadi ta sake rufa bakin iyakarta da Sudan

    Ƙasar Chadi ta sake rufe iyakarta da Sudan bayan wani harin jirgi maras matuƙi ya kashe aƙalla mutum 17 a garin Tine na ƙasar.

    Jami'ai sun ce jirgin ya kai harin ne kan wani taron jana'iza jiya Laraba kuma sun ɗora alhakin hakan kan mayaƙan RSF da yake yaƙi da gwamnati.

    Rundunar dai ta musanta da hannunta a kai harin, kuma ma ta zargin rundunar sojan Sudan da kai harin.

    A yanzu shugaban mulkin soji na Chadi Mahamat Idris Deby, ya ba da umarnin rufe iyakar kuma ya tura jami'ai domin ganin irin barnar da harin ya haifar.

    Da ma dai an rufe iyakar a watan jiya bayan wani tashin hankali mai nasaba da yakin basasar Sudan ya yi sanadin mutuwar sojojin Chadi biyar.

  4. Hotuna sun nuna yadda harin Iran ya yi wa matatar man Isra'ila barna

    Wasu hotunan bidiyo da BBC Verify ya samu sun nuna yadda wuta da hayaki ke tashi a wasu sassan matatar mai ta Isra'ila da ke Haifa.

    A ranar Alhamis ne dai Iran ta harba makamai masu linzami kan matatar man a wani martani kan lalata kamfanin iskar gas na Iran da Isra'ila ta yi ranar Laraba.

    Isra'ila dai ta ce harin bai yi wata barnar a-zo-a-gani ba.

    Sai dai kuma masu fashin baki na cewa ikrarin na Isra'ila ba sabon abu ne kasancewa ta yi kaurin suna wajen rufe bayanai ta yadda jama'a za su yi tunanin kwata-kwata ba a yi mata barna.

    Matatar man ta Haifa dai wadda ke arewacin Isra'ila ita ce matatar mai mafi girma ga Isra'ila.

    Matatar na tace mai ganga 197,000 a kowace rana.

    Hare-haren mizayil daga Iran a watan Yunin 2025 lokacin yakin kwana 12 tsakanin Iran da Isra'ila, sun lalata matatar inda hakan ya tilasta Isra'ila rufe ta tare da shigar da wani bangare na man da take bukata.

  5. An kama mutum 97 da ke yi wa Isra'ila aiki a Iran

    Ma'aikatar tattara bayanan sirri ta kasar Iran a wata sanarwa da ta fitar ta ce ta kama akalla mutum 97 da ke yi wa Isra'ila aiki.

    Sanarwar ta ce sun so tayar da tarzoma da kuma yin kisa a ranar Laraba bisa fakewa da Amurka da Isra'ila amma kuma an gano su kuma an kama su dauke da makamai.

    Kamar yadda ma'aikatar ta ce an kuma gano wasu maboya guda biyar na makamai inda aka samu bama-bamai kirar gida da bindigogi kirar Kalashnikovs da kuma tarin alburusai.

    Bugu da kari, wata sanarwar ta kuma ce an gano masu leken asiri 13 sannan an kama su a kudu maso gabashin Iran.

  6. Manyan kasashe shida sun amince su taimaka a bude mashigar Hormuz

    Wasu manyan kasashe shida sun amince da shiga domin yin duk abin da ya dace wajen tabbatar da sufuri da zirga-zirgar man da iskar gas a mashigar Hormuz da Iran ta rufe.

    A wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen suka fitar, Birtaniya da Faransa da Jamus da Japan da Italy da kuma Netherlands sun ce "mun yi maraba da irin jajircewar kasashen da suka assasa al'amarin sannan mun yi alawadai da harin da Iran ta yi kan jiragen ruwa na fararen hula a yankin”.

    Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da rahotanni ke cewa akalla jiragen ruwan dakon mai 3,200 ke tsaye cak suna jiran a bude musu hanya a mashigar ta Hormuz.

  7. Dole ne Iran ta dakata da kai mana hare-hare - Qatar

    Firaiministan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim bin Jaber Al Thani, ya ce yana kira ga jagororin kasar Iran da su dakata da kai musu hare-hare, inda ya kara da cewa babu abin da hakan zai haifar illa kara dagwalgwala al'amarin.

    Firaiministan ya kuma yi kira da kasar ta Iran da ta sassauta domin samo bakin zare warware matsalar.

    Wannan dai na zuwa ne yan sa'o'i kadan bayan Iran ta kai hare-haren ramuwar gayya kan kamfanin mai da na gas na kasar, martani a kan harin da Isra'ila ta kai wa kamfanin iskar gas na Iran din a ranar Laraba.

  8. Najeriya ta Birtaniya sun ƙulla yarjejeniyar gyara tashoshin Tincan da Apapa

    Firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer ya gana da Shugaban Najeriya Bola Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniyar babba kan sarrafa ƙarafa.

    A yarjejeniyar, Birtaniya za ta samar da tan 120,000 na ƙarafa domin gyara tashoshin jiragen ruwa biyu a Legas, a kwangilar da za ta laƙume fam miliyan 70.

    Sir Keir ya yaba da ziyarar ta Tinubu, wadda ita ce ta farko daga shugaban Afirka ta Yamma a shekara 37.

    A jiya Laraba ne Sarkin Ingila ya gana da Shugaban Najeriya da tawagarsa a Fadar Windsor Castle, inda sarkin ya yaba da alaƙa da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Tuni Birtaniya ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 746 domin haɓakawa da inganta tashoshin jiragen ruwa guda biyu Lagos Port Complex wato tashar Apapa da TinCan Island duka a Legas.

  9. Amurka na duba yiwuwar yaye takunkumi daga man kasar Iran

    Sakataren Baitil-malin Amurka, Scott Besan ya ce gwamnatin Amurka na duba yiwuwar dage takunkumi daga man fetur na kasar Iran wanda yanzu haka yake a jiragen ruwa a cikin teku.

    "Za mu yi amfani da gangunan danyen man kasar Iran wajen rage farashin mai a kasuwar duniya daga nan zuwa kwana 10 ko 14," in ji shi.

    Amurka dai ta kakaba wa kasar Iran takunkumi iri-iri na tsawon shekaru ciki har da na hana wasu kasashe sayen man kasar ta Iran.

    Ana kuma yi wa matakin kallon wani yanayi da Amurka ta samu kanta a ciki na gaba kura baya sayaki, inda ya zama tamkar dole ta bari kasashen duniya su sayi mai daga Iran domin gudun cigaba da tashin farashin danyen man a kasuwar duniya.

    A ranar Alhamis din nan dai farashin gangar danyen mai samfurin Brent a kasuwar duniya ta kai dala 112 tun bayan harin da Iran ta kai kamfanonin mai da na Iskar gas a Qatar, a wani martani dangane da harin kamfaninta na gas da Isra'ila ta yi a ranar Laraba.

    Mista Besant ya kuma bayyana fatan cewa a ganawar yau da za su yi da firaiministan Japan a Washington za a samu fahimtar juna tunda Japan tana da muradi na kai tsaye kan kare sufurin mai a yankin kasashen gwaf.

    Sai dai mista Besant ya musanta rahotannin da ke cewa kasar Iran na shirin "karbar na goro kafin su bar kasashe su wuce ta mashigar Hormuz" inda ya bayyana hakan da "rashin hankali" sannan kuma "abin dariya".

  10. Rundunar tsaron Amurka ta buƙaci ƙarin aƙalla fam miliyan 150 domin yaƙin Iran

    Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce Pentagon na buƙatar ƙarin kuɗaɗe daga lalitar gwamnatin ƙasar domin ci gaba da yaƙi a Iran.

    Ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambaya kan rahotan da ke nuna sun buƙaci kuɗaɗe a yaƙin, wanda Amurka da Isra'ila ke yi a Iran.

    Hegseth sai ya ce kuɗin da ake magana suna neman ƙari wato dala biliyan 200bn kimanin fam miliyan 150 ne, amma ya ƙara da cewa, "kuɗin ma zai iya haura haka."

    "Ana buƙatar kuɗi sosai domin kashe mugayen mutane," in ji Hegseth, sannan ya nanata cewa, "suna samun duk goyon bayan da suke buƙata."

  11. Har yanzu Iran na da sauran ƙarfi - Amurka

    Hukumomi a Amurka sun ce har yanzu Iran da sauran ƙarfin soji, kuma tana da ƙarfin da za ta iya ci gaba da kai hare-hare.

    Babban hafsatn tsaron ƙasar, Janar Dan Caine ne ya bayyana a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a taron manema labarai da sakataren tsaron Pete Hegseth ya kira.

    Da ake tambaye shi ko har yanzu na da sauran ƙarfin soji da za ta iya kai hare-hare, musamman a kan tashoshin makamashi a yankin Gulf duk da kusan mako uku da aka yi ana yaƙin.

    Sai Caine ya ce, "Iran ta fara yaƙin nan da makamai masu yawan gaske. Shi ya sa Amurka take yaƙin da gaske iya ƙarfinta."

    Ya ƙara da cewa Amurka za ta ci gaba da "farautarsu da kashe su," in ji shi, amma sai ya ƙara da cewa, "har yanzu Iran na da sauran ƙarfin soji."

  12. Najeriya ƙasa ce mai ƙarfin tattalin arziki - Sarki Charles

    Sarkin Ingila, Sarki Charles III, ya jinjina wa Najeriya, inda ya ce alaƙa tsakanin ƙasashen biyu na ƙara haɓaka ta ɓangaren tattalin arziki da fahimtar juna, sannan ya bayyana ƙasar a matsayin ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki.

    Sarki Charles ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabin maraba ga shugaban Najeriya Bola Tinubu da matarsa Oluremi Tinubu da sauran tawagarsa a Fadar Windsor Castle.

    Ya ce masarautarsa na godiya ga Tinubu da ya kai ziyarar a lokacin azumi, sannan ya yi waiwayen lokacin da ya ziyarci Najeriya a 2018.

    "A lokacin na gana da wasu sarakunan ƙasarka masu daraja irin su Sultan na Sokoto da Ooni na Ife da Sarkin Kano da sarakunan Warri da Onitsha. Na gane wa idona cewa ƙasar na samun gagarumin cigaba."

    A Birtaniya akwai mutane da dama ƴan asalin Najeriya, waɗanda suke zaune suna gudanar da harkokinsu na kasuwanci da wasu a ɓangaren kimiyya da shari'a da ƙirƙira da fasaha da aikin gwamnati, kuma suna samun nasara sosai.

    "Wannan ziyarar na ƙara nuna cewa Najeriya na ƙoƙarin sa hannu a cigaban Birtaniya, kamar yadda Birtaniya ke sa hannu domin cigaban Najeriya. Ƴan Najeriya sun kashe fam miliyan 178 a Birtaniya a 2024, sannan aƙalla mutum 251,000 ne suka je Najeriya daga Birtaniya, inda suma suka kashe kuɗaɗe masu yawa."

    "Alaƙar da ke tsakanin ƙasashenmu ta wanke ni ne in wanke ka, wadda dukkanmu muke samun riba, sannan kuma alaƙa ce daɗaɗɗiya."

    "Da yammacin na, mai girma shugaban ƙasa ni da kai mun gane wa idon abin koyi mai kyau a ganawarmu da jagororin addinai na Musulunci da Kiristanci na Birtaniya. Taron ya yi ma'ana sosai, musamman kan abin da Najeriya ta daɗe tana nunawa cewa mutane mabambanta addini za su iya rayuwa tare cikin zaman lafiya da lumana."

    Sarki Charles ya ƙara da cewa, "Kasarka na da ƙarfin tattalin arziki, tana da dimɓin tarihin al'adu da murya mai ƙarfi a diflomasiyya daga nahiyar da ke da muhimmanci sosai a duniya," in ji shi.

  13. Fatawar malaman Musulunci kan sallar Idi da Juma'a rana daya

  14. Najeriya da Birtaniya suna da kama da juna wajen samar da cigaba - Tinubu

    Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya tana kan irin tsarin samar da ci gaba ga ‘yan ƙasar kamar yadda Birtaniya ke kai.

    Tinubu ya faɗi hakan ne a lokacin da yake jawabi a Windsor Castle yayin wata ziyara da yake yi a Birtaniya domin amsa gayyatar Sarki Charles.

    Ya jinjina wa alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya na tsawon lokaci, inda ya nuna jin daɗinsa kan irin karramawar da aka masa a matsayin shugaban Najeriya na farko da ya yi jawabi a Windsor bayan shafe sama da shekaru 40 babu wani shugaban ƙasar da ya taɓa samun irin wannan gayyata.

    “Manufofin Najeriya da Birtaniya suna kamanceceniya da juna ta fuskar samar da ci gaba. Muna fatan inganta alaƙar mu da manufofi iri ɗaya,” in ji Tinubu.

    Shugaban Najeriyar ya kuma gode wa Birtaniya kan yadda ta ba shi mafaka a lokacin da suke gwagwarmayar tabbatar da dimokradiyya a ƙasar shekar sama da 20 da suka wuce.

    Ya bukaci ‘yan Najeriya da ke zaune a Birtaniya da su kasance ‘yan ƙasa na gari ta hanyar nuna kyawawan ɗabi’u tare da fatan zumuncin kasashen biyu ya ci gaba da ɗorewa..

    “A matsayin mu na daya daga cikin manyan kasashe a kungiyar Commonwealth, Najeriya na fatan bayar da gudunmawa mai inganci ga ci gaba da bunkasar wannan al'umma a duniya”.

  15. Birtaniya za ta ƙara kuɗin da ake kashewa a BBC

    A yau Alhamis ne ake sa ran gwamnatin Birtaniya za ta tabbatar da cewa za ta ƙara kuɗaɗen da ake bai wa sashen BBC na duniya, wato BBC World Service.

    Ƙarin kuɗin ya kai dala miliyan 44, wato sama da Naira biliyan saba’in da miliyan ɗari huɗu wanda za a rarraba cikin shekaru uku, kimanin ƙarin kashi takwas cikin ɗari fiye a abin da ake bayarwa a yanzu.

    Kashi ɗaya bisa uku na kudaden da BBC ke amfani da su dai ana samo su ne daga ofishin kula da harkokin waje na Birtaniya.

    Sauran kuwa ana tara su ne ta hanyar biyan lasisin talabijin da ƴan Birtaniya ke biya.

    BBC ta ce tana maraba da ƙarin, tana mai cewa hakan zai nuna cewa an yi na'am da ayyukanta, sannan ya taimaka wajen kasa inganta shirye shiryenta.

  16. Isra'ila ba za ta sake kai hari kan tashar iskar gas a Iran ba - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Israila ba za ta sake kai hari kan cibiyar samar da iskar gas ta South Pars ta Iran ba.

    Wakilin BBC ya ce a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump ya ce cikin fushi Isra'ilar ta kai hari kan cibiyar iskar gas ɗin, kuma Amurka da Qatar ba su da hannu ko wata masaniya a kan matakin na Isra'ila.

    Mista Trump ya kara da cewa sai dai abun kaico, Iran ba ta san wannan ba, inda ta runtse ido ta kai wa kamfanin man futer na Qatar hari.

    Ya gargaɗi Iran din kan kada ta sake kai cibiyoyin makamashi na Qatar, in kuwa ba haka ba sai sauya ra'ayinsa.

    Wata sanarwa da kamfanin makamashi na Qatar din ya fitar ta ce harin na Iran ya lalata wurare da dama na kamfanin.

  17. Iran ta kai hari a cibiyar makamashin Qatar

    Duk da gargaɗin da Trump, gidan talabijin na Iran ya ruwaito cewa dakarun juyin-juya-halin ƙasar sun sake kai hari kan cibiyar makamashin ta Ras Laffan d ake Qatar.

    Kamfanin makamashi na ƙasar ya tabbatar da cewa an harba makamai masu linzami da suka afkawa manyan wuraren sarrafa iskar gas da safiyar Alhamis ɗin nan.

    Rahotanni sun ce harin ya haddasa gobara tare da jawo gagarumar asara.

    Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Qatar ta ce an shawo kan biyu daga cikin gobara uku da suka tashi.

    Wannan na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bayan Isra'ila ta ƙaddamar da wani a tashar makamashin Iran, wanda Trump ya ce ba shi da masaniya a kai.

  18. Farawa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.

Trending Now