Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 23/04/2026

Taƙaitattu

  • Sojojin Najeriya sun kashe gomman ƴan bindiga da lalata jiragen ruwansu a Tafkin Chadi
  • Trump ne zai yanke shawara kan lokacin da za a ƙare yaƙin Iran- White House
  • Wane ne Sarki Sulaimanu, Sarkin Kano na farko a tarihi?
  • 'Yawan kuɗin takardun neman takara na APC illa ne ga cigaban ƙasa'
  • PSG na son Fernandes, Barca na harin Silva da Neto
  • Iran na da tarin sindarin uranium - amma me ya sa ba za ta iya mallakar makamin nukiliya ba?

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Isiyaku Muhammad

  1. Sojojin Amurka sun kama wani jirgin ruwan dakon mai da suka ce na ɗauke da man Iran

    Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce dakarun Amurka sun kama wani jirgin ruwan dakon mai a tekun Indian Ocean, da suka yi iƙirarin yana ɗauke da man Iran.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna sojojin suna dira kan jirgin daga cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu.

    Rundunar sojin Amurka ta ce ba a san jirgin ko ta wace ƙasa bace, amma wani shafin intanet da ke bibiyar jirage, ya nuna jirgin da tutar Guyana, kuma yana kan hanyar zuwa China.

    Wannan ne karo na biyu da Amurka ke ƙwace jirgin ruwa a wannan makon.

    Sojojin ruwan Amurkar sun kai hari kan wani jirgin Iran a ranar Lahadi, inda suka zarge shi da ƙoƙarin tsallake shingen da ta sanya.

  2. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƴan bindiga da dama a jihar Yobe

    Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta sun kashe wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai 24 a wani gumurzu da sukai da su a arewa maso gabashin ƙasar.

    Wani jami’i ya ce sojoji 2 sun jikkata, bayan da akai musu kwanton ɓauna da safiyar yau Alhamis a jihar Yobe.

    Ba a bayyana ƙungiyar da ke da alhakin kai harin ba.

    Sai dai Ƙungiyar Boko Haram ta ƙara kaimi wajen kai hare-hare a watannin baya-bayan nan, inda take kai hare-hare kan sansanonin soji da ƙauyuka a jihohin Borno da kuma Yobe.

    Jerin hare-haren da ƙungiyar ta kai na tsawon kusan shekaru 20 ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba sama da mutum miliyan 2 da muhallansu.

  3. Tinubu na neman sahalewar Majalisa domin karbo bashin dala miliyan 500 daga Jamus

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawan ƙasar ta amince da ciyo bashin fiye da dala miliyan 516 daga babban bankin Jamus (Deutsche bank) , domin aikin wani ɓangare na babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.

    A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Godswil Akpabio, Shugaban ƙasar ya ce an tsara aikin gina kilomita 100 na titin ne domin ya haɗa Arewa maso yammacin ƙasar da kudu maso yammaci, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

    A cewar sa, babbar hanyar za ta taso ne daga Illela a jihar Sokoto, ta bi ta jihohin Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun, ta kare a Badagry da ke Jihar Legas.

    A cewar wasiƙar, za a yi amfani da bashin wajen gina sashe na 1, rukuni na 1 da na biyu, mai nisan kilomita 120, cikin bakidaya kilomita 1,000.

    Za a biya bashin ne cikin shekaru 9, amma za a iya ƙara lamunin aƙalla shekaru uku.

    Shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni Majalisar ministocinsa ta amince da tsarin karɓo bashin, inda ya buƙaci majalisar Dattawan ta sanya bashin cikin tsarin karbo bashi na ƙasar.

    Wasiƙar shugaban ƙasar ta bayyana cewa babbar hanyar za ta taimaka wajen bunƙasa kasuwanci, da samar da isashen abinci, da haɗin kan ƙasa.

    Sanata Akpabio ya miƙa buƙatar ga kwamitin kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, kuma ana sa ran zai bayar da rahoto nan da mako guda.

  4. Tarayyar Turai za ta samar da tallafin fiye da Euro miliyan 200 ga Yammaci da tsakiyar Afirka

    Hukumar Tarayyar Turai ta sanar da bayar da tallafin jinƙai na Euro miliyan ɗari biyu da talatin da biyar domin tallafawa marasa ƙarfi a Yammaci da tsakiyar Afirka.

    Tallafin zai je ne ga mutanen da rikice rikicen da ake samu a yanzu suka shafa, da matsalar ƙarancin abinci, da waɗanda suka rasa muhallansa, da alummomin da ake rikici cikinsu, da waɗanda tallafi ke wuyar isa garesu.

    Najeriya za ta samu Euro miliyan 33,(fiye da Naira biliyan 52) domin taimakawa a fannin kiwon lafiya, da samar da abinci mai gina jiki a Arewa maso gabashi da Arewa maso Yammacin ƙasar.

    Za kuma a ware Euro miliyan 75 ga tsakiyar Sahel, da Euro miliyan 16 zuwa Kamaru, sai Euro miliyan 22 zuwa Jamhuriyar tsakiyar Afirka, Chadi kuma za ta samu Euro miliyan 72, Mauritania kuwa za ta samun tallafin kusan Euro miliyan 5.

    A cikin wata sanarwa da kwamishiniyar samar da daidaito ta hukumar Hadja Lahbib ta fitar, ta ce Yammaci da tsakiyar Afirka na fama da matsalolin jin ƙai waɗanda suka samo asali daga rikice rikicen da ake samu, da talauci, da yunwa, da rashin dai daito, da kuma matsalolin sauyin yanayi.

    A cewar sanarwar, Yammaci da tsakiyar Afirkan na fama da waɗannan ɗimbin matsalolin da ke buƙatar tallafin jinƙai.

  5. DSS ta gurfanar da El Rufai kan zargin tatsar bayanai daga wayar Nuhu Ribadu

    Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya (DSS) ta gurfanar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai, a gaban mai shari'a Joyce Abdulmalik a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

    DSS ta gurfanar da shi ne saboda zargin sa da hannu a tatsar bayanai daga wayar mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

    Hukumar ta DSS tana zargin El Rufain da yin kutse da gangan, wanda kuma ya saɓa wa doka kan wayar Ribadun, wanda ya saɓa wa sashe na 7 (b) da (c) na kundin kare bayanan ƙasa masu muhimmanci na 2024, wanda sashe 5(1) na dokar hana aikata laifuka ta intanet na 2024 da aka yi wa gyaran fuska ya tanaji hukunci kansa.

    Wanda ake zargin ya musanta laifukan da ake zargin sa da su, wanda ya sa lauyan masu shigar da ƙara, Oluwole Aladedoye (SAN) ya buƙaci kwanaki uku domin sauraron shari'ar.

    Bayan lauyoyin ɓangarorin biyun sun gabatar da jawabai, mai shari'a Joyce Abdulmalik ta dage sauraron shari'ar zuwa ranakun 18 da 19 da 20 na watan Mayu.

  6. An kashe mutum fiye da 500 a Tanzania bayan zaɓen shugaban ƙasa a bara - Bincike

    Wani kwamitin bincike da gwamnati ta kafa ya gano cewa an kashe fiye da mutum ɗari biyar a lokacin wata mummunar zanga zanga da ta biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na Tanzania a watan Oktoban bara.

    Sai dai tawagar masu binciken ta ce ba a iya tabbatar da rahotannin da aka yi ta yaɗawa cewa an binne gomman ƴan adawa a wasu manyan ƙaburbura ba.

    Ƴan jamiyyar adawa, waɗanda suka kauracewa zaɓen, sun ce an kashe dubban mutane a yayin da jam'ian tsaro ke ƙoƙarin shawo kan tashin hankalin.

    Majalisar ɗinkin duniya ta yi kiran a gudanar da cikkaken bincike, mai zaman kansa kan abin da ta kira tsantsar take haƙƙin biladama.

    Kwamitin binciken na gabatar da rahotonsa a Dar-es-Salaam.

  7. 'Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasɗinawa uku'

    Hukumomin lafiya a Gaza da hukumar tsaron farin kaya a zirin sun ce Falasɗinawa biyar, ciki har da yara uku sun mutu sakamakon hare-haren Isra'ila ta sama.

    Hukumomin Falasɗinu sun ce an kashe mutum biyar ɗin ne a kusa da masallaci a Beit Lahiya da ke arewacin Gaza a ranar Laraba.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari ne kan abin da ta ƙira ’ɗan ta'adda’ da ke kusanto sojojin ta, kuma ya kasance barazana gare su.

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce fiye da Falasɗinawa ɗari bakwai aka kashe, yayin da aka jikkata fiye da dubu biyu a hare haren Isra'ila tun bayan tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila a watan Oktoba.

  8. An mayar da gawar tsohon shugaban Zambia Edgar Lungu ƙasarsa

    Gwamnatin Zambia ta ce an dawo mata da gawar tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu, bayan watanni goma ana taƙaddama kan dawo da gawar daga Afirka ta Kudu.

    Gwamnatin Zambia na so a gudanar da janaizar girmamawa ga Mista Lungu a babban birnin ƙasar Lusaka, wani abu da iyalan sa suka nuna ƙin amincewa.

    Rahotanni sun bayyana cewa an ɗauki gawarsa ne daga wani wurin ajiyar gawa a daren Laraba ba tare da sanin iyalansa ba.

    Babban lauyan gwamnati na Zambia ya ce babbar Kotun Pretoria ce ta miƙa gawar mista Lungu ga gwamnati, bayan da iyalan sa suka yi watsi da batun ɗaukaka ƙarar da suka shigar na buƙatar a soke hukuncin cewa a binne tsohon shugaban ƙasar a Lusaka.

  9. Harin Isra'ila "da gan gan" a kudancin Lebanon ya hallaka wata ƴar jaridar ƙasar

    Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaƙi bayan an sake kashe wata 'yar jarida 'yar Lebanon a kudancin kasar.

    Wani harin Isra'ila ta sama ne ya samu Amal Khalil a lokacin da ake cewa tana kokarin tsira a wani gida.

    Jami'an Lebanon sun ce, da niyya Isra'ila ta kai harin kan 'yar jaridar.

    Firaministan ya ce sojin Isra'ila sun hana ma'aikatan agaji kaiwa ga wajen da suka kai harin.

    Ya ce kasarsa za ta kai batun gaban taruka na duniya.

    Sojin Isra'ila sun musunta kai hari kan 'yan jarida ko hana ma'aikatan agaji kai dauki wajen, kuma sun ce suna gudanar da bincike.

  10. Sojojin Najeriya sun kashe gomman ƴan bindiga da lalata jiragen ruwansu a Tafkin Chadi

    Rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabashin Najeriya, Operation haɗin kai, ta yi nasarar hallaka aƙalla ƴan bindiga talatin, tare da lalata jiragen ruwansu da dama, a yayin wani aiki da suka yi a kan Tafkin Chadi, kusa da yankin tsibirin Kaniram a jihar Borno.

    A cikin sanarwar da kakakin Operation Hadin Kai, Lt. Col Sani Uba ya fitar, sojojin sun kai harin ne cikin daren Talata zuwa safiyar Laraba.

    A cewar sa, ''Jiragen saman sojin rundunar sunyi sintiri tare da tabbatar da kasancewar jiragen ruwan ƴan ta'adda fiye da talatin da suke amfani da su wajen safarar kayayyaki a yankin.''

    Ya kuma ce bayan tabbatar da sun tantance su wane ne, kuma bisa dokokin aikin soji, jami'an rundunar sun kai hare hare ta sama wanda ya lalata jiragen, ya kuma kawo cikas ga ƙoƙarin sufurin kayayyaki.

    Uba ya kuma ce hare haren da suka biyo baya, sun kai su ne kan yan bindigar da ke ƙoƙarin tserewa, wanda ya kai ga kashe kusan mayaƙa 30.

  11. Afirka ta Kudu na bincike kan hare haren da ake kai wa ƴan Ghana a ƙasar

    Gwamnatin Ghana ta ce hukumomin Afirka ta Kudu sun kaddamar da bincike kan jerin hare-haren da ake kaiwa na ƙyamar baƙi a kan 'yan Ghana da ke zaune a Afirka ta Kudun.

    A kwanakin nan hotunan bidiyo da ke nuna yadda ake cin zarafin 'yan Ghana a Afirka ta Kudu sun yaɗu sosai.

    Harin kyamar baki abu ne mai sarkakiya - wanda matsala ta tattalin arziki, da yaɗa bayanai na ƙarya, da sauran wasu matsaloli ke kara rura wutarsa.

    Ana ta samun ƙaruwar zanga-zanga da tashin hankali, inda ake harar baƙi waɗanda ba 'yan ƙasar ta Afirka ta Kudu ba, yayin da ake shirin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi nan gaba cikin shekarar nan.

    A watan da ya gabata Najeriya ta yi kira ga 'yan kasarta da su yi kaffa-kaffa, sakamakon wata zanga-zanga kan baƙin haure da ta rikiɗe ta zama tashin hankali.

  12. Trump ne zai yanke shawara kan lokacin da za a ƙare yaƙin Iran- White House

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce babu wani wa'adi na kawo ƙarshen dakatar da buɗe wuta da Iran, wanda Donald Trump ya tsawaita ranar Talata da daddare.

    Sakatariyar yaɗa labaran fadar, Karoline Leavitt ta shaidawa manema labarai cewa shugaba Trump, zai yanke shawara kan lokacin da za a kare yakin.

    Haka kuma ta kafe cewa datse tashoshin jiragen ruwa na Iran da Amurka ta yi na samun nasara, ta hanyar yi wa tattalin arzikin Iran din abin da ta kira ''KANSHIN MUTUWA''.

    Wakiliyar BBC ta ce Amurka na fata ne na ganin datsewar da ta yi wa Mashigar Hormuz ta sa tattalin arzikin Iran ya jigata yadda hakan zai sa Iran din ta je teburin tattaunawar.

    Shugaban kasar Iran din Masoud Pezeshkian, ya bayyana wannan datsewa a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da suka haifar da tarnaki ga tattaunawar zaman lafiya.

    Ya ce kasarsa a shirye take a tattauna, amma ya zargi Amurka da - da kalamai na munafurci da ba sa karewa.

    A gefe guda kuma, Iran ɗin ta sha alwashin ba za ta sake buɗe Mashigar Hormuz ba.

  13. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafinmu na BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar yau Alhamis, inda yau ma kamar kullum za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za kuma ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa, da kuma kallon bidiyo.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.

Trending Now