Za mu ƙarƙare yaƙin Iran nan da wata ɗaya - Amurka
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya shaida wa taron ministocin harkokin wajen kasashe masu karfin tattalin arziki G-7 cewa za a ci gaba da yakin da Amurka ke yi da Iran na tsawon makonni biyu zuwa hudu.
Da yake magana da manema labarai bayan taron, babban jami'in diflomasiyyar Amurkan ya ce zuwa wannan lokacin Amurka ta cike burukanta.
Tun da farko dai ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar sun fitar da wata sanarwa inda suka bukaci a sake bude mashigin Hormuz.