Najeriya na ci gaba da shari’ar fiye da mutum 500 da ake zarginsu da hannu a hare-haren ‘yan ta-da-ƙayar-baya da suka janyo mutuwar dubban mutane, a ɗaya daga cikin shari’o’in ta’addanci mafi girma a ƙasar.
Ministan Shari’ar ƙasar, Lateef Fagbemi ya ce shari’ar ta fara ne da gurfanar da mutum 227 da ake zargi a gaban alƙalai guda goma.
Ana zargin waɗanda ake ƙarar da hannu wajen kai hare-hare akasari a sassan arewacin Najeriya, inda ayyukan tarzoma masu alaƙa da ‘yan ta-da-ƙayar-baya suka yi sanadin kashe fiye da mutum dubu biyu da raba ɗumbin wasu da gidajensu.
Sauran na fuskantar tuhume-tuhume a kan goyon bayan ‘yan ta-da-ƙayar-baya ta hanyar ba su kuɗaɗe da kai musu makamai da sauran kayan buƙatun rayuwa.
Ministan shari’ar ya ce girman wannan shari’a ya nuna ƙudurin gwamnatin Nijeriya na tabbatar da ganin an bi ƙa’ida yayin da ake ƙoƙarin ganin hukunci ya yi aiki a kan masu hannu a ayyukan ta’addanci.
An tsaurara matakan tsaro da suka haɗa da na sojoji da ‘yan sanda da jami’an leƙen asiri.
Masu sa-ido na duniya ciki har da ƙungiyoyin kare ‘yancin ɗan’adam da ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya sun hallara a kotun.
A ranar Talata ne aka yanke wa mutum biyar hukuncin ɗaurin shekaru daban-daban a gidan yari bayan sun amsa laifi kan tuhume-tuhumen da suka haɗar da sayar da dabbobi da kai kayan abinci da tsegunta bayanai ga ‘yan ta-da-ƙayar-baya.
Hukumomi sun ce za a ci gaba da shari’o’in kashi-kashi, lamarin da ke nuna cewa an kama hanyar ɗaukan wani ƙwaƙƙwaran mataki game da rikicin ta-da-ƙayar-bayan da ya daɗe yana tagayyara sassan Nijeriya.