Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 12 zuwa Juma'a 18 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Daga Jaridu

    Liverpool ce kan gaba a neman siyen ɗan wasan Bournemouth da Argentina,Marcos Sensi, da kwantaraginsa zai ƙare a wannan kaka. (i paper)

    Manchester City na dab da kamala tayin siyen ɗan wasan Feyenoord Givairo Read, sai dai Bayern Munich ita ma na harin ɗan wasan. (Sky Sports)

    Livepool na son ɗauko ɗan wasan Newcastle Anthony Gordon, da ɗan wasan Everton Iliman Ndiaye, a yunƙurinsu na ƙara inganta ƴan wasan gaban ƙungiyar a kaka mai zuwa. (Teamtalk)

    Tsohon ɗmai horar da Chelsea da Manchester United, Jose Mourinho na kan gaba cikin wanda Newcastle ke son ya maye gurbin Eddie Howe, idan har suka yanke shawarar sallamar mai horar da ƴan wasan ƙungiyar. (Talksport)

    Bournemouth na mataki na gaba wajen ɗaukar tsohon mai horar da ƴan wasan Borussia Dortmund da RB Leipzig Marco Rose, kasancewar ba ya tare da wata ƙungiyar a halin yanzu. (Telegraph - subscription required)

  2. Rosenior ya ce lokaci na neman ƙurewa Chelsea a Premier, Premier League

    Liam Rosenior ya amince cewa lokaci na ƙurewa Chelsea wajen neman gurbin shiga Champions League bayan da ta yi nasara ɗaya a wasanni bakwai baya a Premier League.

    Manchester United za ta kai ziyara Stamford Bridge ranar Asabar, a wasan da zai zama dole Chelsea ta yi nasara domin ganin ta kare a cikin koda ƴan biyar din farko ne.

    Chelsea tana ta shidan teburi da tazarar maki huɗu tsakani da Liverpool ta huɗu, kuma saura wasa shida suka rage a kakar nana.

    Shan kashi 3-0 a gida a hannun Manchester City a ranar Lahadi shi ne na uku a jere da ta yi rashin nasar a gasar, wanda ya jefa ƙungiyar da Rosenior ke jan ragama cikin gagrumin koma baya.

    Yanzu haka sama da makonni shida kenan tun bayan da Chelsea ta zura ƙwallo a gasar lig, lamarin da ke nuna irin matsalar da take ciki. Tsohon kocin RC Strasbourg da Hull City ya bayyana cewa za su ci gaba da sa kaimi domin Chelsea ta koma kaN GANIYA.

    Ana sa ran za a yi zanga-zangar daga magoya baya kafin wasan United, abin da ke nuna yadda alaƙa tsakanin magoya baya da ƙungiyar ta lalace tun bayan da kamfanin BlueCo ya karɓi ragamar Chelsea kusan shekaru huɗu da suka wuce.

  3. Al Waleed bin Talal zai mallaki kaso mafi tsoka a Al Hilal, Saudiyya

    Kamfanin Kingdom Holding, mallakin attajirin ɗan kasuwa Yarima Al Waleed bin Talal, ya kulla yarjejeniya mai karfi domin sayen kaso 70% na ƙungiyar ƙwallon kafa ta Al Hilal.

    Yarjejeniyar ta kimanta darajar jarin Al Hilal zuwa Riyal miliyan 1.4 (kimanin dala miliyan 373.20). An ce wannan mataki yana cikin dabarun kara yawan riba tare da mayar da jari cikin tattalin arzikin cikin gida.

    Tun daga watan Yuli a 2023, Kamfanin zuba jari PIF ne ke rike da mafi yawan hannun jari a Al Hilal, a matsayin wani bangare na shirin bunkasa ƙungiyar da kuma kara gudunmawar bangaren wasanni ga tattalin arzikin kasar.

    Al Hilal, wacce ta lashe gasar lig sau 19, tana matsayi na biyu a teburin Saudi Pro League da maki 68 daga wasanni 28, tana da tazarar maki takwas da Al Nassr, duk da cewa tana da kwantan wasa daya.

    Kammala wannan yarjejeniya zai dogara ne kan cika wasu sharudda da kuma samun amincewar hukumomi kamar yadda aka tanada a cikin yarjejeniyar.

  4. Ƙyaftin Silva zai bar Man City a karshen kakar nan, Manchester City

    Ƙyaftin ɗin Manchester City, Bernardo Silva, zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana, bayan kwantiraginsa ya ƙare.

    Ɗan wasan tawagar Portugal mai shekaru 31 ya zura ƙwallo 76 da bayar da 77 aka zura a raga a cikin wasa 451 da ya buga wa City tun bayan zuwansa daga AS Monaco a shekarar 2017.

    Nasarar da ya samu a lashe Carabao Cup a watan da ya gabata shi ne kofi na 15 da ya ɗauka tare da City, ciki har da cin uku rigis a 2022/23.

    Silva ya kuma taka rawar gani wajen taimaka wa City lashe Premier League da maki 100 a kakar 2017/18, da kuma lashe dukkan kofuna huɗu na gida a kakar 2018/19, sannan ya taimaka wajen lashe gasar lig sau huɗu a jere tsakanin 2021 zuwa 2024.

    Silva shi ne kaɗai ɗan wasa daga sabon zamanin Manchester City da yake cikin manyan ƴan wasa goma da suka fi buga wasanni a tarihin ƙungiyar din, kuma a yanzu yana matsayi na takwas da yin kan-kan-kan da Mike Summerbee.

    An naɗa shi ƙyaftin ɗin ƙungiyar ne bayan tafiyar Kevin De Bruyne a ƙarshen kakar da ta gabata, kuma ya lashe Premier League sau shida a cikin kakar wasa takwas da ya yi a City.

    A halin yanzu City tana matsayi na biyu a teburin Premier League, kuma za ta fafata da Southampton a wasan semi-final a FA Cup a ranar 25 ga Afrilu.

  5. Tsohon ɗan wasan Arsenal, Mamminger ya mutu, Arsenal

    Ƙungiyar Bundesliga ta sanar a ranar Alhamis cewa tsohon mai tsaron raga Alexander Manninger mai shekaru 48 ya mutu a wani sakon da ta wallafa a kafarta ta sada zumunta a X.

    Rahotanni daga Austria sun bayyana cewa motar Manninger ta yi karo da jirgin ƙasa a wata hanyar tsallaka layin dogo a yankin Nussdorf am Haunsberg a safiyar ranar Alhamis.

    Manninger, wanda ya buga wa tawagar ƙasarsa wasa 33, ya koma Arsenal a shekarar 1997 daga Grazer AK kan kuɗi fam 500,000. Ya buga wasa 64 a ƙarƙashin koci Arsène Wenger, inda ya lashe gasar Premier League a cikin shekaru biyar da ya yi kafin ya bar ƙungiyar zuwa Espanyol, sakamakon hamayaya a gurnin tsare raga da David Seaman da Richard Wright.

    Arsenal ma ta wallafa sako a X tana cewa: “Kowa a Arsenal ya kadu kuma ya yi matuƙar bakin ciki da rasuwar tsohon mai tsaron raga, Alex Manninger.

    Manninger ya kuma buga wasa a ƙungiyoyi da dama a Italiya kamar Torino, Bologna, Siena da Juventus, inda ya lashe kofin Serie A. Haka kuma ya taka leda a Augsburg a Jamus da kuma Liverpool na ɗan lokaci a gasar Ingila.

  6. Champions League - Karawar kusa da ƙarshe:

    • Atletico Madrid v Arsenal
    • Paris St-Germain v Bayern Munich

    Za a buga wasannin kusa da ƙarshe a ranakun 28 da 29 ga watan Afrilu da kuma 5 da 6 ga watan Mayu.

  7. Champions League - Sakamakon wasannin Laraba:

    • Bayern Munich 4-3 Real Madrid (6-4)
    • Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)
  8. ARSENAL TA KAI WASAN KUSA DA NA ƘARSHE A GASAR CHAMPIONS LEAGUE KAKA BIYU A JERE, Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)

    Ko akwai abin da zai sauya? Shin ya kamata ta yi farin ciki?

    Yanzu za ta fafata Athletico Madrid domin neman kaiwa matakin wasan ƙarshe.

  9. BAYERN MUNICH ta kai wasan kusa da ƙarshe

    An buga wasa mai ƙayatarwa amma a ƙarshe Bayern Munich ta kai matakin kusa da ƙarshe na gasar zakarun Turai ta Champions League, za ta kara da Paris St-Germain.

    Bayern Munich v Paris St-Germain (Wasan kusa da ƙarshe)

  10. ƘWALLO A RAGA! Bayern Munich 4-3 Real Madrid (Jimilla 5-4)

    Bayern ta kammala aiki!

  11. SHI KENAN! ARSENAL TA SHA!, Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)

    Arsenal ta tsallaka zuwa wasan kusa da na ƙarshe bayan tashi wasa 0-0.

    Arsenal dama ta zura ƙwallo ɗaya a gidan Sporing a makon da ya gabata.

    Arsenal ta kai wasan kusa da na ƙarshe kakar wasa biyu ke nan a jere.

    Atletico Madrid v Arsenal (Wasan kusa da ƙarshe)

  12. ƘWALLO A RAGA! Bayern Munich 3-3 Real Madrid (Jimilla 5-4), Luis Diaz

    Kaiiii! Wata ƙwallo mai kyawu a mintunan ƙarshe!

    Abin ba a cewa komai!

  13. Katin Kora: Real Madrid

    Akwai ƴan wasan Real da dama da suke kan siraɗin samun kati. Eduardo Camavinga ya yi fawul da yawa.

    Dama yana da katin gargaɗi kuma sai ya yi wa Harry Kane ƙeta, nan take aka ɗaga masa jan kati.

  14. AN ƘARA MINTI 4 A WASAN ARSENAL, Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)

    An yi ƙarin lokaci na minti 4 a wasan Arsenal da Sporting, idan babu wanda ya jefa ƙwallo shi kenan.

  15. , Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)

    Arsenal na ci gaba da riƙe ƙwallo saboda a tashi wasa a haka.

    Sporting ta matsa lamba tana danna Arsenal.

  16. , Bayern Munich 2-3 Real Madrid (4-4 jimilla)

    Antonio Rudiger ya kaɓe ƙwallo domin hana Jamal Musiala jefa ta a raga.

    Ya yi ƙoƙari.

  17. , Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)

    Saura minti biyar a tashi wasan Arsenal da Sporting.

    Ko Sporting ta ci kwallo ko kuma idan aka tashi haka shi ke nan ta tafi gida.

    Idan aka tashi a haka, Arsenal ta shiga matakin kusa da wasan ƙarshe.

  18. , Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)

    Magoya bayan Arsenal na ci gaba da cizon yatsa, sun ƙosa a tashi.

    Magoya bayan Sporting na ci gaba da samun ƙwarin gwiwa har yanzu.

  19. KATIN GARGAƊI, Bayern Munich 2-3 Real Madrid (4-4 jimilla)

    An ba ɗanwasan Madrid Eduardo Camavinga katin gargaɗi saboda ya riƙe rigar Jamal Musiala.

  20. , Arsenal 0-0 Sporting (Jimilla 1-0)

    Ana minti na 78: Sporting na ci gaba da matsa wa Arsenal lamba.

    Ana jefa ƙwallo ɗaya a raga lissafi ya dagule.

Trending Now