Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 24/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Labarai da dumi-dumi, Babu tattaunawa da Amurka cikin ajandarmu ta zuwa Islamabad - Iran

    Kamfanin dillancin labaran Iran Tasnim ya ce a yanzu haka babu batun tattaunawa da Amurka cikin ajandar bulaguron ministan harkokin wajen Amurka zuwa Islamabad.

    Kafar yaɗa labaran ta ce Abbas Araghchi zai je Islamabad ne domin tattauna yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin amma da Pakistan.

  2. Dangote na shirin gina katafariyar matatar mai a gabashin Afirka

    Hamshaƙin attajirin nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya bayyana shirin gina katafariyar matatar man fetur da za ta iya tace ganga 650,000 a kowace rana a gabashin Afirka.

    Yayin da yake jawabi a wani babban taron masu ruwa da tsaki kan masana'antun Afirka, da ke gudana a birnin Nairobin Kenya, Dangote ya ce shirin wani mataki ne na bunƙasa masana'antu a nahiyar.

    Taron - wanda manyan shugabannin Afirka da masu zuba jari da masu ruwa da tsaki kan harkar masana'antu suka halarta - an shirya shi ne domin magance matsalolin makamashi a nahiyar.

    Dangote ya ce lokaci ya yi da Afirka za ta inganta masana'antunta an cikin gida, tare da rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙetare.

    “Muna fitar da ma'adinai ba tare da mun sarrafa su ba, abin da hakan ke nufi shi ne idan kana fitar da ma'adinanka kana asarar ayyuka ne, kuma idan kana shigo da abubuwa, tamkar kana shigo da talauci ne zuwa ƙasarka'', in ji Dangote

    Ya jaddada cewa bunƙasa masana'antu, musamman na tace mai da samar da taki da sauran abubuwan da ake samar wa daga man fetur, na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar talauci tare da samar da ayyuka a nahiyar.

    Samar da matatar a gabashin Afirka na cikin wani ɓangare na zuba jarin dala biliyan 40 da kamfaninsa zai yi daga nan zuwa 2030.

  3. Tinubu ya rantsar da Muttaqha Darma sabon ministan gidaje

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Dr Muttaqha Rabe Darma a matsain sabon ministan gidaje na ƙasar.

    Dr Darma - ɗan asalin jihar Katsina - ya maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa, wanda ya yi murabus a baya-bayan nan.

    An rantsar da sabon ministan ne a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja.

    Shugaba Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwarsa ga Dr Darma, saboda tarihin abubuwan da ya gabatar a baya.

    “Babu shakka ka yi abubuwa na yabo kan ayyukan da aka ɗora ka a baya, don haka ka cancani wannan sabon muƙami,'' a cewar Shugaba Tinubu.

    Dr Darma ya riƙe muƙamai daban-daban da baya da suka haɗa da babban sakataren asusun fasahar man fetur daga 2008 zuwa 2012.

    Ya kasance tsohon kwamishinan ma'aikatar ayyuka, gidaje da sufuri na jihar Katsina, sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan raya karkara na jihar ta Katsina.

  4. Steve Wikoff da Jared Kushner za su halarci tattaunawar Pakistan

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters da kafar yaɗa labaran CNN ta Amurka, sun ambato wasu jami'an Amurka na cewa wakilin Amurka a musamman, Steve Witkoff da surukin Shugaba Trump, Jared Kushner na kan kan hanyar Islamabad domin halartar sabon tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Duka kafofin labaran biyu na cewa wakilan za su gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi - wanda tuni aka tabbatar da cewa zai halarci tattaunawar.

  5. Gwamnatin Iran ta tabbatar da halartar tattaunawar Pakistan

    Gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi zai kama hanyar Islamabad, domin halartar tattaunawa da Amurka.

    Cikin wani saƙo da gwamnatin ƙasar ta wallafa a shafinsa na X, ta ce Araghchi zai yi bulaguro mai tsayi zuwa yankuna daban-daban ciki har da birnin Muscat na Oman da kuma Rasha domin tattauna yarjejeniyar haɗin gwiwa da ci gaban yankin da kuma batun kawo ƙarshen yaƙin ƙasar.

    Sai dai saƙon bai yi ƙarin haske game da tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin da ƙasar ke yi da Amurka ba.

  6. Matsalar jin ƙai na ƙara tsananta a Najeriya - MSF

    Kungiyar agaji ta MSF ta yi gargaɗin cewa ana fuskantar matsalar jin ƙai da ke ƙara ƙamari a arewa maso gabashin Najeriya.

    Ta ce hare-haren baya-bayan nan da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai suka kai a jihar Borno, sun raba fiye da mutum 500,000 da muhallansu.

    Iyalan da suka tsere zuwa garin Pulka, kusa da iyakar Kamaru, yanzu suna zaune ne a sansanonin da suka cika maƙil, tare da ƙarancin abinci da ruwa da kuma tsafta.

    Mayaƙan Boko Haram da kuma wani ɓangare na ƙungiyar da ya balle, sun ƙara tsananta hare-hare a watannin baya-bayan nan, inda suke kai hari kan dakarun tsaro da fararen hula a arewacin Najeriya.

  7. Ba ma zumuɗin ƙulla alaƙar zaman lafiya da Iran - Pete Hegseth

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Heg-seth, ya ce Washington ba ta zumuɗi wajen kulla yarjejeniya zaman lafiya da Iran.

    Yayin da yake magana a wani taron manema labarai, ya yi gargadin cewa toshe mashigar Hormuz na ƙara tsananta, kuma lamarin na shafar duniya baki ɗaya. Ya ce makomar kawo ƙarshen taƙaddamar na hannun Iran.

    Wannan furuci na nuna yadda ake samun maganganu masu karo da juna daga Amurka, bayan da Shugaban ta Donald Trump ya ce ya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar, ba tare da wani wa'adi ba a farkon makon nan.

    Kafafen watsa labaran gwamnatin Iran sun ce ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Aragh-chi, na kan hanyarsa ta zuwa Pakistan, wadda ke shirin karɓar baƙuncin zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya.

  8. Sojojin Isra'ila na shirin kai wa Hezbollah hare-hare

    Sojojin Isra’ila sun fitar da gargadin gaggawa ga mazauna garin Deir-A-mes da ke kudancin Lebanon, inda suka ce suna shirin kai hare-hare kan mayakan Hezbollah da ake zargi suna a yankin.

    Garin Deir-A-mes na arewacin yankin mai tsaro da Isra’ila ta ayyana, inda dakarunta ke ci gaba da aiyukan su, duk da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni uku da aka amince da ita awanni kaɗan da suka gabata.

    Wakiliyar BBC ta ce Lebanon ta ce tana son fara tura dakarunta zuwa kudancin ƙasar domin ci gaba da kula da Iyakar yankin nan ta ke.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar, Paul Mor-cos, ya ce babban sharadin Beruit shi ne janyewar sojojin Isra’ila daga yankin.

    Sai dai Isra’ila na cewa dole ne ta ci gaba da kasancewa a yankin, domin hana ƙungiyar Hezbollah da Iran ke marawa baya harba makaman roka zuwa cikin ƙasarta.

  9. Peter Obi na neman ƙulla ƙawancen siyasa da arewa maso gabas

    Ɗantakarar neman kujerar shugabancin ƙasa a jam'iyyar LP a 2023, Peter Obi ya jagoranci wata bababr tawaga ta ƴan siyasar kudu maso Gabas domin ƙulla ƙawance da arewa maso gabas da sauran sassan Najeriya da manufar ciyar da ƙasar gaba.

    Mista Obi ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis a Bauchi bayan wata ganawa ta sirri da ya yi da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad da masu ruwa da tsaki dangane da ƙulla ƙawancen siyasa.

    Peter Obi dai yana ta zagaye a faɗin ƙasar domin ƙulla ƙawance yayin da kakar zaɓe ke ƙara ƙaratowa.

    A makon da ya gabata ne dai magoya bayan Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso suka kafa wata ƙungiya mai suna OK movement da ke son goyon baya ga takarar Obi da Kwankwaso a matsayin shugaba da mataimaki a jam'iyyar ADC.

  10. Sarki Sanusi ya soki yawan cin bashi da gwamnatin Najeriya ke yi

    Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya nuna damuwarsa dangane da yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da dogaro ga ciyo bashi duk da cire tallafin man fetur da ƙasar ta yi.

    Da yake jawabi a wani taro kan tattalin arziki a birnin Legas, ranar Juma'a, Muhammadu Sanusi ya yi gargaɗin cewa rashin alkilta kuɗi ka iya zagwanye cigaban da ake tunani za a samu sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙin da Najeriya ta yi.

    Sarki Sanusi wanda a baya ya yi kakkausar suka ga cire tallafin mai ya nanata cewa ba abu ne mai dorewa ba sannan ya soki yadda Najeriyar ta dogara kacokan a kan matatun mai na ƙasashen waje.

  11. Amurka na son ɗaukar matakin korar wasu ƙasashe daga NATO kan yaƙin Iran

    Rahotanni sun ce ma’aikatar tsaron Amurka, wato Pentagon, na nazarin wasu matakai na ladabtar da ƙasashen ƙungiyar tsaron na NATO, saboda rashin goyon bayansu ga yaƙin Amurka da Iran.

    Wani jami’in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, wani saƙon imel ya nuna takaicin da take ji kan yadda wasu ƙawayenta ke ƙin bayar da damar amfani da sansanoninsu, da kuma izinin zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyarsu.

    Daga cikin matakan har da yunƙurin dakatar da Spain daga NATO, da kuma duba yiwuwar sake nazarin amincewa da ikon Birtaniya kan tsibirin Foklands.

    A cewar wakilin BBC, wani jami’in NATO ya ce kundin yarjejeniyar ƙungiyar tsaron ta NATO bai tanadi dakatarwa ko korar mamba ba.

    A martaninta, Fadar Downing Street ta ce ikon mallakar tsibirin Foklands na hannun Birtaniya.

  12. Tarayyar Turai ta nemi a shigar da ƙwararru kan nukiliya a batun Iran

    Jami'ar tsare-tsaren ƙasashen waje na Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta ce haɗarin Iran ka iya ƙaruwa idan ƙwararru kan nukiliya ba a shigar da su cikin tattaunawar da ake yi da Iran ba.

    Da take magana yayin wani taron shugabannin na Turai a Cyprus, Kaja Kallas ta ce duk wata yarjejeniya da za a cimma ka iya samun tasgaro fiye da yarjejeniyar baya ta 2015

    "Idan dai tattaunawar ta taƙaita ga shirin nukiliya kuma ba tare da ƙwararru a fannin nukiliya ba to yarjejeniyar ka iya lalacewa fiye da ta baya," in ji Kallas.

    "Sannan kuma idan ba a magance batutuwan makamai masu linzami ba da tallafa wa ƙungiyoyi bamsu riƙe da bindiga to tarayyar Turai za ta fuskanci barazana daga Iran" kamar yadda ta ƙara bayani.

  13. Iran da Pakistan na tattauna batutuwan da suka shafi tsagaita wuta

    Ministan harkoki ƙasar Iran ya ce sun tattauna batutuwan da suka shafi tsagaita wuta da manyan jami'an ƙasar Pakistan, a daidai lokacin da Pakistan ɗin take shirye-shiryen karɓar baƙuncin tattaunawar ta Iran da Amurka.

    Abbas Araghchi, a wata sanarwa a Telegram ya fadi cewa ya tattauna da Ishaq Dar, mataimakin firaiministan Pakistan tare da ministan harkokin Pakistan da kuma Field Marshall Asim Munir.

    Ya ƙara da cewa sun yi maganganu dangane da "ci gaban yakin gabas ta Tsakiya mai alaƙa da batun tsagaita wuta.

    Aragchi bai fayyace ko yana magana ne dangane da batun tsagaita wutar Iran da Amurka ko kuma ta Isra'ila da Lebanon ko kuma duka biyun.

  14. A Najeriya yan majalisar dattawa sun yi karin haske kan bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta neman su amince masa ya karbo rancen bashin dala miliyan 516 daga Babban Bankin Jamus domin gudanar da aikin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.

    Shugaban ya miƙa buƙatar ne ta hanyar wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar Dattijan Godswill Akpabio, wanda shi kuma ya karanta ta yayin zaman da aka yi a jiya Alhamis.

    Wasu yanmjalisar dattawan sun nuna goyon baya ga buƙatar yayin da kuma wasu ke cewa an daɗe ana neman amincewar majalisa kan irin wannan buƙatar ta aikin babbar hanyar ta Sokoto zuwa Badagry a jihar Legas

  15. Shugaban Kenya na shan suka saboda ya ce ƴan Najeriya ba su iya turanci ba

    Shugaban Kenya William Ruto na shan suka a shafukan sada zumunta bayan wasu kalamai da ya yi na shaguɓe kan yadda ƴan Najeriya ke turanci. Ya ce idan ƴan Najeriya na turanci sai mutum ya nemi tafinta kafin ya gane abin da suke cewa.

    Yayin da yake yi wa ƴan Kenya mazauna Italiya jawabi a ranar Litini, Ruto ya ce: "Idan kana sauraren yadda ƴan Najeriya ke magana, ba za ka gane me su ke cewa ba - sai ka nemi wanda zai fassara maka," inda ya bugi ƙirjin cewa ƴan Kenya na daga cikin mutanen da suka fi iya magana turanci a duniya.

    Kalaman nasa na shan suka daga ƴan Najeriya da wasu ƴan Afrika da suka zargi shugaban Kenyan da cin fuskar ƙasar da take a Afrika.

  16. Ƙasashen Afirka za su fuskanci matsalar bashi

    Wani kamfanin bincike da nazari kan al'amuran da suka shafi kuɗaɗe da kimanta ƙarfin tattalin arziƙi na ƙasashen duniya mai suna S&P Global Ratings, ya yi gargaɗi cewa yawan bashin da ake bin ƙasashen Afirka na iya ta'azzara, idan har yakin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran ya tsawaita.

    Kamfanin ya ce bashin da ƙasashen na Afirka za su buƙata zai ƙaru ne matuka, a sakamakon tasirin yakin.

  17. Ghana ta koka da nuna ƙyamar mutanensu da ake a Afirka ta Kudu

    Gwamnatin Ghana ta ce mahukuntan Afirka ta Kudu sun fara gudanar da bincike kan wasu hare-haren nuna kyama da ake kai wa ƴan ƙasar mazauna Afirka ta Kudu.

    Hotunan bidiyo da ke nuna ana cin zarafin 'yan Ghana a Afirka ta Kudu sun karaɗe shafukan sada zumunta na Intanet a ƴan kwanakin nan.

    Hare-haren ƙyamar baƙi wani lamari ne mai sarƙaƙiya, wanda matsalolin tattalin arziƙi da labaran ƙarya da rashin fahimtar tarihi ke haifarwa.

    Ana dai samun ƙaruwar zanga-zanga da tashin hankali kan nuna ƙyama ga waɗanda ba ƴan asalin Afrika ta Kudu ba musamman a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ƙasar.

  18. Birtaniya ta ce ƴan China na sayar da bayanan sirrin jama'a

    Wani shirin tattara bayanai na lafiya na Birtaniya ya ɗora alhaki a kan masu bincike 'yan China marasa taka-tsantsan, kan yadda ake sayar da bayanan sirri na wajen mutum rabin miliyan da suka bayar da bayanansu bisa radin kansu.

    Ana dai sayar da bayanan ne a yanzu a wani shafin kasuwanci na intanet na China.

    Wata ƙungiyar agaji wadda ke gudanar da shirin tattara bayanan na Birtaniya ta gabatar da kanta ga hukumar da ke sa ido wajen kare bayanai ta Birtaniya.

    Shirin dai yana amfani da bayanan lafiya, na dubban mutane da na ƙwayoyin halittarsu na DNA, wajen inganta hanyoyin gano wasu cutuka masu tsanani da kuma magance su.

    Masu bincike a faɗin duniya na iya samun bayanan, amma bisa sharaɗi mai tsanani na tabbatar da kare sirri.

  19. Trump ya bayyana India da tambaɗaɗɗiyar ƙasa

    Gwamnatin India ta mayar da martani kan wasu kalamai da Shugaba Trump ya sake yaɗawa a shafin sada zumunta, kalaman da ke bayyana India a matsayin wata tambaɗaɗɗiyar ƙasa.

    Hukumomin Indiyar sun ce, kalaman ba su dace ba sam-sam kuma muzanci ne gare su.

    Ma'aikatar harkokin waje ta India ta ce kalaman ko alama ba su nuna irin ainahin alaƙar da ke tsakanin India da Amurka ba.

    Shugaban na Amurka ya yaɗa takardar bayanan wani shiri ne na siyasa wanda Micheal Savage ya gabatar, inda Savage din ya yi ƙorafi da cewa - duk jaririn da aka haifa a Amurka, nan take kai tsaye yake zama ɗan ƙasa, kuma wanda aka haifa ɗin nan sai ya shigo da gaba ɗayan 'yan uwansa daga China ko India ko kuma wata lalatacciyar ƙasa a duniya.

  20. BBC ta gano gidan da Jeffrey Epstein ke ajiye matan da yake lalata da su

    BBC ta bankado shedar da ke nuna cewa matan da Jeffrey Epstein, mutumin nan da aka kama da laifin lalata da ƙananan yara, ya riƙa ajiye su a gidaje daban-daban a birnin London, bayan da 'yansanda suka yanke shawara cewa ba za su bincike shi ba.

    Wakiliyar BBC ta ce, bincike a takardun da ma'aikatar sharia ta Amurka ta fitar, mun gano cewa yana biyan haya a aƙalla gidaje huɗu a London inda yake ajiye mata ɗaya daga cikin matan Virginia Giuffre.

    Ya kuma faɗa wa hukumar 'yansandan London a 2015 cewa - ta kasance wadda masu safarar mutane na ƙasa da ƙasa don lalata, wadda take da alaƙa da London, ta ci zarafi.

    A lokacin hukumar 'yansandan London din ba ta bude wani cikakken bincike ba kan lamarin, da cewa ba ita ce hukumar da ya kamata ta yi bincike ba.

    A yanzu ta ce, an shigar da ita tare da wasu hukumomin tsaron masu alaƙa ciki har da na Amurka, domin samun ƙarin bayanai don tabbatar da musayar bayanai a tsakaninsu.

Trending Now