Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata zargin da wani tsohon jami'inta Rotimi Olamilekan, ya yi na cewa sojojin ƙasar da kuɗin aljihunsu su ke sayen kayan sarki da sauran kayan aiki.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna yadda tsohon soja da aka sallama daga aiki yake nuna damuwa kan halin da ya ce sojin ƙasar ke ciki da rashin samun kulawar da ta kamata.
Sai dai a wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran rundunar sojin ƙasa na Najeriya, Appolonia Anele, ya fitar, ta ce iƙirarin ba gaskiya ba ne, inda ta jaddada cewa ana samar da kayan aiki yadda ya kamata ga jami'an.
Bayanin na zuwa ne bayan da aka sallami jami'in da ake kira da Soja Boi, sakamakon ɓullarsa a wani bidiyo da ya ke kira ga manyan ƴansiyasa a ƙasar su sanya ƴaƴansu aikin soji, da kuma yadda ya koka kan halin ko in kula da ake nuna musu.
A cikin hrar da aka yi da shi ya ce, tun daga kan takalmin da suke sanyawa, da kayan sarki, da hular kwano da rigar kariya daga harsashi, sai dai su saya daga albashinsu.
Game da batun albashi, rundunar sojin ta ce akwai albashi wadatacce da kuma wasu alawus-alawus da ake ba jami'an.
Amma ta ce, wasu jami'an na da damar amfani da kuɗinsu wajen sayen wasu kayayyakin da suke buƙata amma sai idan su ne suka ga damar yin hakan.
Rundunar ta buƙaci jama'a su yi watsi da zarge-zargen da ta ce suna ƙoƙarin rage ƙwarin gwiwa ne kawai da kuma aibu ga tsaron ƙasa.