Amurka ta fitar da bayanan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon
Wani bayani daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ya bayyana cikakkun bayanai kan yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki goma tsakanin Isra’ila da Lebanon da za a fara da karfe 5 na yamma agogon ƙasar a yau.
Amurka ta ce, bayan da ɓangarorin biyu suka gana a zahiri don tattaunawa a birnin Washington a wannan makon, "sun tabbatar da cewa ƙasashen biyu ba su yaƙi da juna, kuma suna da ƙudurin shiga tattaunawa ta gaskiya ta gaskiya, da Amurka ke jagoranta".
Ga wasu muhimman bayanai guda 6 daga ciki:
- Gwamnatin Isra'ila ta bayyana matakin tsagaita wutan a matsayin "abin fatan alheri"
- Za kuma a iya "faɗaɗa yarjejeniyar idan an fahimci juna" a yayin tattaunawar
- Duk da tsagaita wutar, Amurka ta sake nanata ƴancin Isra’ila na “ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare kai, a kowane lokaci, kan hare-haren da ake shirin kai mata ko ake kaiwa"
- Da zarar an fara tsagaita buɗe wuta, gwamnatin Lebanon "za ta ɗauki matakan da suka dace don taka wa Hezbollah burki, da sauran masu tada ƙayar baya masu ɗauke da makamai" a cikin ƙasarta.
- Ƙasashen sun amince da " alhakin Lebanon da ƴancinta na tabbatar da tsaron ƙasar"
- Isra'ila da Lebanon sun buƙaci Amurka da ta ci gaba da shiga tsakanin kasashen biyu a tattaunawar da ake yi, da nufin warware duk wasu batutuwan da suka rage