Mutanen Borno sun yi addu’oi sama da miliyan 41 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya domin neman kawo ƙarshen masifar da mayakan kungiyar Boko Haram suka jefa su a ciki.
Wata ƙungiya ce mai suna Borno Concerned Citizen wato ƴan jihar da suka damu da halin da take ciki ta jagoranci taron addu’o’in a ranar Lahadi.
Barista Zahra Maiduguri ɗaya daga cikin waɗanda suka jagoranci addu’o’in ta ce an yi saukar Al ƙur’ani da kuma addu’oi 41, 837,016 domin neman sauƙin masifar da jihar take ciki.
Daga cikin addu’o’in har da “Istigifari” miliyan 13,669,000 da “Ya Laɗifu” miliyan 10,688,00.
An kuma yi “Ya Kahharu” fiye da miliyan ɗaya da salatin Annabi da kuma salatil fati.
Baya ga addu’u’oin an kuma yanka dabbobin shanu da nufin yin sadaka domin Allah ya biya buƙata.
Ƙungiyar ta kunshi shugabanni na siyasa da na gargajiya da malaman addini da malaman Boko a jihar Borno.
Mayakan Boko Haram sun kwashe fiye da shekara goma suna kai hare-hare a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar dubban mutane da kana suka raba miliyoyin jama'a da gidajensu.
Harin Zabarmari inda ƙungiyar ta yi wa manoma yankan rago shi ne hari na baya-bayan nan mafi muni da Boko Haram ta kai a jihar Borno.