BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Abin da Kotun Ƙoli ta ce kan rikicin Masarautar Kano
A wani zaman da ta yi a Abuja, kotun ta ƙoli ta ɗage zaman sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Afrilun 2027, wato kimanin shekara ɗaya daga yanzu.
Dole a samar da tsaro a Najeriya - Hafsan hafsoshi
Wannan shafi na kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa dangane da yaƙin Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 20/04/2026
Hanyoyi uku da suka rage wa Arsenal na lashe kofin Premier
Rashin nasarar da ƙungiyar ta yi da ci 2-1 ya sake jefa ta cikin babbar barazanar gaza lashe Kofin Premier da ta shafe fiye da shekara 20 tana ƙishirwarsa.
Da me Turkiyya za ta taimaka wa Najeriya ta fuskar tsaro?
Yarjejeniyar - wadda aka ƙulla tsakanin ministan tsaron Najeriya da takwaransa na Turkiyya - ta ƙunshi samar da babban sansanin bayar da horo ga dakarun Najeriya, kamar yadda shalkwatar tsaron Najeriya ta bayyana.
Yaran da aka haifa kusa da sansanin sojin Birtaniya a Kenya sun gano gaskiya kan mahaifansu
Wani lauya a Birtaniya James Netto da kuma wani Kelvin Kubai a Kenya, sun ce akwai kusan yara 100 da aka haifa kusa da sansanin sojin Birtaniya a Kenya.
Son yin takara ne a gaban 'yan ADC ba Najeriya ba - Shekarau
Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau, ya ce son yin takara ne a gaban jiga-jigan da ke jagorantar tafiyar ADC, ba wai bukatar ciyar da kasar gaba ba.
Mece ce manhajar Claude Mythos kuma wanne haɗari ke tattare da ita?
Manhajar Mythos za ta iya fin ɗan adam ƙoƙari kuma tana da kwarewa wajen tsaron intanet sai dai wannan ikirari da kamfanin Anthopic ya yi, ya haifar da tsoro a zukatan masu amfani da manhajojin kuɗi a duniya
Yaushe duniya za ta fuskanci sauyin yanayi na 'Super El Niño'?
Masana kimiyar sauyin yanayi sun yi gargarɗin cewa ka da a ruɗu da hasashen sauyin yanayi a watan Maris da Afrilu.
Har yanzu tsugune ba ta ƙare ba a yaƙin Iran - Netanyahu
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 19/04/2026
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 21 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 20 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 20 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 20 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Marco Rose ya amince zama sabon kocin Bournemouth
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 19 zuwa Juma'a 24 ga watan Afrilun 2026.
Man United da Real Madrid na zawarcin Emery, Arsenal da Chelsea na son Bergvall
Hankalin Manchester United da Real Madrid ya koma kan Kocin Aston Villa Unai Emery, ko da yake Villa na da kwarin gwiwa a kansa
Madrid na son dawo da Mourinho, Onyeka zai koma Conventry
Real Madrid na tunanin nada tsohon kocinta Jose Mourinho wanda ke jagorantar Benfica
Hanyoyin daidaita lokacin motsa jiki domin samun sakamako mafi kyau
Masu tashi da wuri, wato yan safe kenan ya kamata su motsa jiki da safe domin samun cikakken amfani, yayin da wadanda suke yan dare ne ya fi dacewa su motsa jiki da yamma, in ji masu bincike.
Liverpool za ta Fafata da Man U kan Wharton, Newcastle za ta sayar da Wissa
Liverpool ta bi sahun Manchester United a yunkurin dauko dan wasan Ingila Adam Wharton daga Crystal Palace, wadda ke son akalla fam miliyan 80 kan dan wasan .
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Wane ne fir'aunan da ya yi zamani da annabi Musa?
Littattafan addini na baya su ma ba su ambato sunan wannan "Fir'aunan" ba, wanda ya mulki Misra kuma ya yi rayuwa da Annabi Musa.
Yadda zargin sakaci ke janyo salwantar rayuka a asibitin Jami'ar Maiduguri
Jama'a a Najeriya na ci gaba da korafi kan zargin sakaci da aiki, da rashin kyakkyawar kulawar da ta dace ga majinyata a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri a jihar Barno, al'amarin da ake zargin yana jefa majinyatan cikin mawuyacin hali, har ma da kai wasunsu ga rasa rayukansu.
Wurare 5 da suke nuna tarihin cinikin bayi a Afirka
Tsananin azabar da aka sha lokacin cinikin bayi, musamman a yankunan baƙar fata na ƙara tabbatar da yadda bauta ta taka muhimmiyar rawa a tarihin nahiyar Afirka.
Wankan safe ko na dare: Wanne ya fi amfani?
Wanke muhimman wurare a jiki tare da yin wanka na wasu kwanaki a mako zai haifarwa da mutum rayuwa cikin ingantacciyar lafiya
Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026
Da gaske hasken waya na haifar da matsala ga bacci?
Yadda rage haske da maraice ya ke taimakawa wajen samun bacci cikin sauƙi
Yadda wasu kurame suka gudanar da aikin Hajji
A kowace shekara, miliyoyin mutane suna zuwa Saudiyya domin yin Umrah, wato ibadar da Musulmi ke iya yi a kowane lokaci, sabanin Hajji wanda wajibi ne sau ɗaya a rayuwa kuma yana gudana a watan karshe na kalandar Musulunci.
Da gaske matsalar tsaro ta fi ƙaruwa gabanin zaɓe a Najeriya?
Ƴan Najeriya na ta muhawara kan kalaman da shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya yi cikin wannan mako game da alaƙar matsalar tsaro da zaɓen ƙasar na 2027 da ke tafe.
Ina ce mashigar Malacca da ka iya haɗa Amurka da China yaƙi?
Kafin cimma yarjejeniyar da ta sa ƙasar Iran buɗe mashigar Hormuz, ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ruwa a duniya, hankalin duniya ya koma kan wata muhimmiyar mashigar.
''Ya kamata jama'a su rungumi tubabbun 'yan tada kayar baya''
Yayin da mutane da dama ke nuna fargabata kan mu'amala da tubabbun yan tada kayar bayan nan sama da 700 da gwamnatin Najeriya ta saki, wasu masana halayyar dan adam sun yi gargadin rashin jan su a jiki, na iya janyo su sake komawa ruwa.
Ina ce mashigar Hormuz da ƙasar Iran ta buɗe?
Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.
Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2026 da yawansa ya kai naira tiriliyan 68.32.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.

































































