Tarihin Kano da jerin Sarakunanta daga 999 zuwa yau

..

Asalin hoton, MT SAFANA

Bayanan hoto, Ranar da Turawa suka ci Kano da yaki suka kafa tutar Birtaniya a daya daga kofofin shiga garin.
Lokacin karatu: Minti 5

Wannan makala ce da muka yi bayan da muka buƙaci ku aiko tambayoyinku a kan tarihin masarautar Kano a 2018. BBC ta ɗauki lokaci don samo amsar tambayoyin daga wajen masana tarihi na masarautar Kano.

Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a ƙasar Hausa a yammacin Afirka.

Tarihi ya nuna tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru tun zamanin jahiliyya kafin zuwan addinin Islama.

Masarautar ta taimaka wajen bunƙasa birnin Kano da Arewaci da ma Najeriya baki ɗaya.

Birnin na Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin Afirka ta yamma

Asalin Kalmar 'Kano'

Mutanen da suka fara zama a Kano maƙera ne da suka tashi daga garin Gaya domin neman ƙasa mai arziƙin tama, wadd za su sarrafa su yi ƙarfe da ita.

Mutanen sun yi dace da samun ƙasar mai ƙunshe da sinadarin tama, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta.

Wajen ya kuma kasance mai matuƙar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duwatsun su ne dutsen Dala da Goron Dutse da Fanisau da Jigirya da Magwan.

Akwai kuma koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Jakara, da kuma kogin Kano.

Hakan ya sa mutane da dama suka ringa yin kaura zuwa yankin domin zama.

Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin mafarauci da ake cewa Kano, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na Kano.

Farfesa Tijjani Muhammad Naniya wanda masanin tarihi ne ya ce har kawo yanzu masana ba su kai ga tantance lokacin da aka fara zama a yankin na Kano ba.

Sannan a cewarsa, masana ba su gama tantance mutanen wace Gaya ce suka fara zama a yankin na Kano ba. Ya ce akwai Gaya ta Kano da ta Nijar da kuma ta yankin Sakkwato.

Babu cikakken bayani kan lokacin da aka fara zama a yankin Kano, amma a cewar Dakta Naniya an taɓa gano wata maƙera a kusa da dutsen Dala da masana suka ce ta kai shekara 200 bayan Annabi Isa.

Hakan ya sa ake hasashen cewa garin Kano ya kafu kimanin shekaru 400 kafin addinin musulunci. Ma'ana a yanzu birnin ya kai shekara kusan 2000 da kafuwa.

Yaushe aka fara sarauta a Kano?

A lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama'a a karkashin mulkinsa.

Jama'ar da suke zaune a ƙauyuka kamar Dala da Goron Dutse da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna ƙarƙashin shugabanci ne na mutanen da suke tare da su.

Daga baya ne da garuruwan suka fara bunƙasa, sannan dangantaka tsakaninsu ke ƙara inganta a lokacin ne aka samu shugaba guda ɗaya da ya haɗa kan mutanen.

Barbushe da sarautar Kano

Barbushe, wani shahararren mafarauci ne da masana tarihi suka ce shi ne mutum na farko da ya haƙa ƙauyukan a ƙarƙashin ikonsa a lokaci guda.

Barbushe ne ya kuma kafa shugabancin Kano.

Masana tarihi na cewa Barbushe jika ne na kimanin 15 ga mutumin da ya fi shahara cikin wadanda suka fara zama a garin, kuma aka bai wa birnin sunansa wato Kano.

DaktaTijjani Naniya ya ce masana tarihi sun fi karkata ga cewa Barbushe shi ne mutumin da ya fara haɗa ƙauyukan Kano waje ɗaya ta fuskar shugabanci da kuma addini.

"A lokacinsa ne addinin bautar Tsumburbura ya shahara, kuma Barbushe shi ne babban bokan Tsumburbura. Sha'anin addini shi ne babban abin da ya fara haɗa kan mutanen Kano."

Bayan zamanin Barbushe da kimanin shekara 200 aka samu wasu mutane daga yankin Daura da suka ci Kano da yaƙi suka kafa sarauta a ƙarƙashin Bagauda a shekarar 999.

Gidajen sarautar Kano

..

Asalin hoton, Kassim Turaki

Bayanan hoto, Sarkin Kano Usman Ɗan Tsoho ya na jiran isowar Yarima Edward dan sarauniyar Ingila a ziyarar da ya kai zuwa Kano a 1925.

Masana sun haɗu cewa akwai gidaje da dama da suka yi mulkin Kano tun daga 999 zuwa yanzu.

Masanan sun ce tun daga kan Sarki Bagauda dan Bayajidda har kan sarkin Kano na ƙarshe kafin Fulani wato Sarki Alwali dukkanin su daga jini ɗaya suke.

Sai dai an ci gaba da samun sauye-sauye a tsarin shugabancin da kuma rungumar wasu sabbin abubuwa.

Masarautar Kano ta rabu ne zuwa gidaje biyar kamar haka:

  • Gidan Bagauda
  • Gidan Rumfa
  • Gidan Kutumbi
  • Sarki Sulaiman
  • Gidan Ibrahim Dabo

Gidan Bagauda

  • Bagauda ɗan Bawo, Jikan Bayajidda 999-1063
  • Warisi ɗan Bagauda 1063-1095
  • Gijimasu ɗan Warisi 1095-1134
  • Nawata da Gawata 1134-1136
  • Yusa 1136-1194
  • Naguji 1194-1247
  • Guguwa 1247-1290
  • Shekarau 1290-1307
  • Tsamiya 1307-1343
  • Usmanu Zamnagawa 1343-1349

Gidan Rumfa

  • Muhammadu Rumfa 1463-1499
  • Abdullahi dan Rumfa 1499-1509
  • Muhammad Kisoki (1509-1565)
  • Yakubu 1565
  • Dauda Abasama 1564 ('Yan Kwanaki)
  • Abu-Bakr Kado 1565-1573
  • Muhammad Shashere 1573-1582
  • Muhammad Zaki 1582-1618
  • Muhammad Nazaki 1618-1623

Gidan Kutumbi

  • Muhammadu Alwali Kutumbi 1623-1643
  • Alhaji ɗan Kutumbi 1648-1649
  • Shekarau II 1649-1651
  • Muhammadu Kukuna 1651-1652
  • Soyaki 1652 (Ya yi mulki ne na wasu 'yan wattanni)
  • Muhammad Kukuna (An sake naɗa shi) 1652-1660
  • Bawa (1660-1670)
  • Daɗi (1670-1703)
  • Muhammad Sharif (1703-1731)
  • Kumbari (1731-1743)
  • Al-Hajj Kabe (1743-1753)
  • Yaji II (1753-1768)
  • Baba Zaki (1768-1776)
  • Dauda Abasama II (1776-1781)
  • Muhammad Alwali (1781-1805

Sarki Suleimanu ɗan AbaHama

  • Suleimanu dan AbaHama 1805-1819

Sarki Sulaimanu shi ne sarki na 44, amma shi ne sarki na farko a cikin sarakunan Fulɓe.

Lokacin da aka yi jihadi aka kori Sarki Alwali an naɗa Sulaimanu ne a matsayin Sarki na ɗaya a daular Fulani.

Gabanin naɗa shi, shi ne limamin manyan gidajen da suka haɗu suka yi jihadi. Kuma mafi karancin shekaru a cikinsu.

Ya yi sarautar Kano a tsakanin shekarar 1805 zuwa shekarar 1819 miladiyya kafin Allah ya kawo ƙarshen mulkinsa.

Sarki ne malamin addinin Musulunci, wanda masana tarihi suka bayyana cewa yana da sauƙin kai da amana da girmama mutane musamman ɗaliban ilimi da almajirai.

Gidan Dabo

  • Ibrahim Dabo dan Mahammadu 1819-1846
  • Usman Maje Ringim ɗan Ibrahim Dabo (1846-1855)
  • Abdullahi Maje Karofi ɗan Ibrahim Dabo (1855-1883)
  • Muhammadu Bello ɗan Ibrahim Dabo (1883-1893)
  • Muhammadu Tukur ɗan Bello (1893-1894)
  • Aliyu (Alu) Babba ɗan Abdullahi Maje Karofi (1894-1903)

Sarakunan Fulani bayan zuwan Turawa

..

Asalin hoton, M T Safana

Bayanan hoto, Ranar da Turawa suka ci Kano suka kafa tutar Birtaniya a daya daga kofofin shiga garin.
  • Muhammad Abbas Ɗan Maje Karofi (1903-1919)
  • Usman II dan Maje Karofi (1919-1926)
  • Abdullahi (Alhaji) Bayero Ɗan Abbas (1926-1953)
  • Muhammadu Sanusi I Ɗan Bayero (1954-1963)
  • Muhammad Inuwa Ɗan Abbas (1963 - Tsawon wata uku wasu na cewa wata 7 kacal ya yi)
  • Ado Bayero Ɗan Abdullahi Bayero (1963-2014)
  • Muhammadu Sanusi II 2014 - 2020
  • Aminu Ado Bayero - 2020 - 2024
  • Muhammadu Sanusi/Aminu Ado Bayero 2024 zuwa yau - (kotun ƙoli ta ce za ta yanke hukunci kan wane ne halastaccen Sarkin Kano a ranar 19 ga watan Afrilun 2027, sakamakon rikicin masarautar da ya ɓalle).

Sarakunan Kano da suka karɓi Musulunci

..

Asalin hoton, M T Safana

Bayanan hoto, Hoton da ke nuna tsohon cikin gidan sarkin Kano (Gidan Rumfa) jim kadan bayan zuwan turawa. An ɗauki hoton ne gabanin a fara sauye-sauye na zamani a gidan
  • Aliyu Yaji Ɗan tsamiya I 1349-1385
  • Bugaiya 1385-1390
  • Kanejeji dan Yaji 1390-1410
  • Umaru 1410-1421
  • Dauda I 1421-1438
  • Abdullah Burja 1438-1452
  • Dakauta 1452 ('Yan kwanki)
  • Atume 1452 ('Yan kwanki)
  • Yakubu dan Abdullahi 1452-1463