Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Alex Babir, Ba'amurken da ake zargi da ingiza ƴan Najeriya su ɗauki makami?
Tun bayan bayyanar wani matashi ɗan Amurka mai suna Alex Babir ya na sukar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu bisa gazawarsa wajen daƙile kai wa al'ummar jihohin Benue da Plateau, ƴan Najeriya ke son sanin haƙiƙanin wane ne wannan matashi.
A cikin wani bidiyo maras tsayi, Alex ya kuma yi kira ga dandazon masu alhini na harin da aka kai musu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar da dama, inda ya nemi da su ɗauki makami domin kare kansu.
Barbir dai na cikin mutanen da ke da nuna damuwa da takaici dangane da abin da ya bayyana da yi wa "Kiristocin Najeriya kisan gilla", wani abu da dama ƴan Najeriya ciki har da mabiya addinin Kirista suke musantawa.
BBC ta yi nazari dangane da haƙiƙanin abin da ya faɗa da haƙiƙanin wane ne shi da kuma illar maganganun nasa.
Me ya faɗa?
A cikin ɗaya daga cikin bidyoyin da aka ga Alex, ya na jawabi ne ga wani dandazon mutane da ke jana'izar mutanen da aka kashe musu sakamakon wani hari da aka kai musu ranar Lahadi da ya yi sanadiyyar rasuwar aƙalla mutum 10.
"...waɗannan maharan Fulani ne kuma suna yin abin da suke yi ne a matsayin Jihadi...Kuma gwamnati ta na taimaka musu...saboda haka ya kamata ku tashi ku kare kanku...ina bindigoginku?, kamar yadda Alex ya faɗa ya na kewayawa fili sanye da gajeren wando.
A wani bidiyon kuma an ga matashin a gaban wata wuta da ke ciki.
"Yanzun nan suka kashe mutum 10. Kiristoci da ba su ji ba, ba su gani ba a ranar Lahadi. Tinubu, ka na ina a lokacin da ake kashe mutanenka cikin dare?"
"Ka na zaune a Aso Rock ba ka yin komai. Ka bar mutanenka ana kashe su."
Yaushe za a daina? Yaushe za ka saurari koken ƴan Najeriya Kiristoci? Babu yadda za a yi ka musanta kisan kiyashi. Ana kashe su, kuma ka ce babu matsala."
Wane ne Alex Babir?
Bayanai da BBC ta tattaro daga waɗanda suke bibiyar Alex da kuma masana harkokin tsaro, sun nuna cewa matashin ɗan ƙasar Amurka wanda ke gudanar da ayyukan jinƙai a Najeriya.
Bayanan sun nuna cewa sunansa Alex Daniel Barbir wanda aka haifa a ranar 17 ga watan Agustan 1997, a Lawrenceville da ke jihar Georgia ta Amurka.
Alex ya shahara a matsayin ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle sannan kuma ɗan ƙwallon ƙafa ne.
A 2018 ne Alex ya bar harkar wasan ƙwallon ƙafa sakamakon raunin da ya samu, inda ya koma Jami'ar Liberty University a tsangayar koyan aikin likitanci. Sai dai kuma ya sake komawa ƙwallon a 2020, inda ya samu wata babbar nasara.
Alex ya koma mai ayyukan jinƙai ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna "Tallafar waɗanda ake azabtarwa".
A yanzu haka, Alex Babir ya na aiki a matsayin mai ayyukan jinƙai a Najeriya.
Rahotanni sun ce Alex Babir ya taimaka wajen sake gina gidaje fiye da 35 da hare-hare a jihar Benue suka lalata sakamakon rikicin makiyaya da manoma a jihar.
'A soke bizarsa a fitar da shi daga Najeriya'
Malam Kabiru Adamu wanda masanin tsaro ne kuma shugaban kamfanin da ke nazarin al'amuran tsaro a yankin Sahel na Beacon Security and Intelligence Limited, ya ce al'amarin matashin ba ƙaramar barazana ba ce kuma dole ne a tashi tsaye.
"A ƙa'ida a lokacin da ake bayar da biza akwai dokokin da ke nuna cewa babu ruwan baƙo ɗan ƙasar waje da al'amuran da suka shafi cikin gida. Ya kamata hukumomi musamman sashin harkokin waje da na shigi da fici su shiga cikin wannan al'amarin a kira shi a gargaɗe shi. A nuna masa cewa dole ya bi ƙa'idojin da aka ba shi. Idan kuma ba haka ba sai a soke bizar a fitar da shi daga cikin ƙasa.
Ya kamata gwamnatin Najeriya ta nuna cewa ita ƙasa ce mai cin gashin kanta. Ba shakka muna da fahimtar cewa an yi kuskure bayar da kai a irin haɗakar da take yi tsakaninta da Amurka ba tare da yi wa ƴan ƙasa bayani ba, me yiwuwa shi ya bai wa irin su Alex damar yin abin da suke yi," in ji malam Kabiru Adamu.
Ina Alex yake?
Wani bidiyo da yake karakaina a shafukan sada zumunta ya nuna gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang yayin da yake jajanta wa al'ummar da suka rasa iyalansu da ƴan uwansu a hare-haren baya-bayan nan, ya ce Alex na hannun ƴan sanda duk da dai bai ambaci sunansa ba.
"Mun ji daɗi da ku ka yi haƙuri ba ku ɗauki doka a hannunku ba duk da abin da wani matashi ya rinƙa faɗi cewa ku ɗauki makamai ku kare kanku....yanzu haka yana hannun ƴansanda..," in ji Mutfwang.