Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace illa matakin INEC zai yi ga ADC?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 5
Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ɗauki wani matakin da ya haifar da cece-ku-ce a siyasar ƙasar, inda ta cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC tare da Abdulra'uf Aregbesola a matsayin sakatare janar na jam'iyyar.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Inec ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon umurnin kotu kan shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi'u Gombe.
Hukunci da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 12 ga watan Maris ɗin 2026, kotun ta nemi dukkannin ɓangarorin da su jira hukuncin babbar kotun tarayya.
Hukumar ta ce sakamakon hukuncin na kotun ɗaukaka ƙarar ne ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga lauyoyin ɓangarorin biyu masu taƙaddama da juna a kotu, inda ɓangaren David Mark ya nemi ka da ta amince da ɓangaren Nafi'u Gombe sannan shi ma lauyoyin Gombe suka nemi a cire sunan David Mark daga na'urarta ta jerin shugabannin jam'iyyun da Inec ta amince da su.
Sai dai jama'iyyar ADC ta yi watsi da matakin da hukumar INEC ɗin ta ɗauka, inda ta ce ba ta fahimci umurnin kotun ba, kuma ta yi zargin jam'iya mai mulki ta APC tana amfani da ita domin murƙushe ƴan'adawa a ƙasar.
Tuni wannan mataki ya haifar da zafafan kalamai daga ƴanƙasar, inda suka yi ta nuna ɓacin ransu kan matakin na INEC.
Yadda matakin zai shafi ADC
Masana shari'a da masu sharhi kan lamuran siyasa na ganin wannan babban ƙalubale ne ga dimokraɗiyyar ƙasar.
Farfesa Nasiru Aliyu SAN, babban lauya ne a Najeriya, ya ce hukumar INEC ta shiga tsaka mai wuya ne sakamakon samun umurnin kotuna biyu, masu cin karo da juna.
Ya ce Inec ta kafa hujja ne da hukuncin kotun da ke cewa "a koma yadda ake kafin wannan ƙara, kuma kada a taɓa komai" shi ya sa ta ɗauki matakin, tunda ko a lokacin da aka shigar da sunayensu akwai ƙara a kotu.
"Idan ka kai ƙara gaban kotu, da zai zama kamar riga mallam masallaci, sai kotu ta ce a dakata. Idan an ce ante bellum, a doka ana nufin kafin faruwar abu, to kuma an yanke wannan hukuncin ne kafin a wallafa sunan David Mark," in ji shi.
"Ita hukumar INEC ta samu kanta a tsaka mai wuya, domin idan ba ta bi umarnin kotu ba, zai kasance ta yi wa kotu karan tsaye."
Ya ce matakin zai shafi ADC saboda wa'adin zaɓen 2027 na ƙara matsowa, kuma idan ba ta warware lamarin ba za ta fuskanci ƙalubale babba.
Sai dai Farfesa Abubakar Umar Kari, malami a sashen nazarin harkokin siyasa a jami'ar Abuja, ya ce matakin ya zo da bazata, kuma zai yi illa sosai ga dimokradiyyar Najeriya ba ma iya jam'iyar ADC ba.
Ya ce matakin zai ƙara jefa shakku a zukatan ƴanƙasar, kuma ba lallai su aminta da hukumomin ƙasar ba, musamman a wannan lokacin da jam'iyar ke ƙara samun karɓuwa.
"Idan irin waɗannan abubuwa suna faruwa, zai sa shakku ƙwarai a zukatan ƴan Najeriya a kan cewa ko ma za a bari adawa ta wanzu, kuma ita siyasa ba ta haɓata, ba ta nasara sai da adawa" in ji Farfesa Kari.
Ya ce: "Duk ƙasashen da dimkraɗɗiya ta wanzu ta haɓaka.., akwai adawa ƙwarai da gaske. Wannan abu da ya faru ga jam'iyar ADC, idan ba a magance shi ba, zai yi illa ga da'awa da yunƙurin da ake yi na dasa adawa a Najeriya".
Abin da ya kamata ADC ta yi
Farfesa Kari ya ce abin da ya kamata ADC ta yi yanzu shi ne, ta yi saurin wayar da kan ƴanƙasar da nuna cewa ba ta razana ba, duk da yake matakin koma baya ne, amma ta yi gaggawar daukar mataki shari'a kafin lokaci ya ƙure.
"Akwai matakai na doka da ya kamata [ADC] ta ɗauka, domin a ɗaga wannan hukuncin. Amma babban abin da ya kamata su yi tukuna, su tattaro kan ƴan Najeriya, su ma su yi farfadanda irin ta su, su mara musu baya," in ji Farfesa Kari.
Ya ƙara da cewa, su kansu gwamnatin Najeriya da hukumomi idan suka fahimci an samu haɗin kan ƴanƙasar, dole su janye ƙudurin nasu.
Farfesa Aliyu SAN, ya ce akwa buƙatar jam'iyar ADCn ta yi sulhu a wajen kotu idan har tana son cimma burinta.
"Suna buƙatar shawara ta siyasa, idan suna son su taimaki juna, kada su yi ci da zuci, su yiwa junansu asara, su koma su zauna a gida su warware matsalolin nan, in ba haka ba, wannan hukuncin kotun zai tafi da su," in ji Farfesa Aliyu SAN.
ADC ta mayar da martani
Faisal Kabir, jami'i ne a ofishin watsa labarai na jama'iyyar ta ADC bangaren David Mark, ya shaidawa BBC cewa dama tun a ranar Talata suka fitar da sanarwa cewa ''akwai wasu mutane a cikin wannan gwamnatin ta APC sun matsa wa shugaban hukumar zaɓe ka dolen dole sai ya kawo cikas a cikin shugabancin jam'iyyar ADC.''
Ya yi zargin cewa masu wannan matsin lamaba ga shugaban hukumar zaɓen sun yi nasarar shawo kansa bayan ɗaukar lokaci ana kai-komo, shiyasa har ya amince da cewa a yanzu ba zai yarda da shugabancin dukkan ɓangaroin biyu ba, har zuwa lokacin da za a kammala shari'a.
''Tun daga lokacin da aka ga mutane suna tururuwa suna shiga wannan jam'iyya tamu ta ADC, hankalin gwamnatin Tinubu ya tashi, ta san cewa ƴan Najeriya ba za su bari ta tsallake shekarar 2027 ba, duba da halin da suka sa Najeriya a ciki. Don haka wannan firgici ne da tsoro ya sa gwamnati ke ƙoƙarin lallai sai shugaba Tinubu ya rasa wanda zai kara da shi a zaɓen 2027.'' In ji Faisal Kabir.
Wane zaɓi ya rage wa ADC?
Yanzu haka dai ɓangaren David Mark na jam'iyyar ADC ya yi kira ga magoya bayan shi su kwantar da hankali yayin da jagororin su ke tattaunawa domin neman mafita.
Faisal Kabir ya ce ''wannan nasara ce, wannan ƙarfin gwiwa zai ƙara mana, kuma zai ƙara haɗa kan jagororinmu, kuma muna aiki tuƙuru domin tattabatar da cewa nan da ɗan lokaci kaɗan za mu faɗa masu mataki na gaba,''
Ya ƙara da cewa a yanzu ƙofar su a buɗe take domin zaƙulo mafita kan wannan batu, da kuma tabbatar da cewa sun kawar da gwamnatin APC a 2027.
''Tun bayan zaɓen 2023, wannan gwamnatin tun da ta zo kan mulki babu abin da ta mayar da hankali sai tabatar da cewa ta rusa jam'iyyun adawa. An rusa SDP, an rusa Labour an rusa jam'iyyar NNPP, an rusa PDP, yau kuma gashi jam'iyyar ADC wadda ita kaɗai ƴan Najeriya ke fatan ta ceto su, itama ana ƙoƙarin sai an rusa ta,'' in ji Faisal Kabir.
Yadda rikicin ADC ya samo asali
Rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ya kunno kai ne a watan Yulin 2025 lokacin da shugabannin jam'iyyar suka yi murabus, kuma David Mark ya zamo sabon shugaba na riƙon ƙwarya, inda aka zaɓi sauran ƴan kwamitin zartarwa babu hamayya.
Sai dai kuma tsohon mataimakin jam'iyyar, Nafi'u Gombe ya ƙalubalanci zaɓen inda ya dage cewa dole ne a samar da shugabanci ta hanyar da kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tsara.
Ya kuma garzaya kotu yana neman ta ayyana shi a matsayin shugaban ADC saboda a lokacin da shugabanninta suka yi murabus shi kadai ya rage, kuma a matsayin mataimakin shugaba mai baring ado, shi kundin mulki ya bai wa damar ɗarewa shugabancin kai tsaye.