Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Trump ke neman ɗauki daga ƙungiyar NATO a yaƙin Iran?
Shugaba Trump ya ce yana tattaunawa da ƙasashe da dama domin taimakawa wajen ƙwace ikon mashigin Hormuz a daidai lokacin da yaƙinsa da Iran ke ci gaba da illa ga tattalin arzikin duniya.
Sai dai Mista Trump ya yi gargaɗi ga ƙungiyar tsaro ta NATO idan har ba ta taimaki Amurka ba.
"NATO za ta fuskanci mummunar makoma," kamar yadda shugaban ya bayyana a wata hira da ya yi da jaridar Financial Times.
Shugaban ya sake yin kira ga ƙasashe su shiga ƙoƙarin tabbatar da buɗe mashigar Hormuz da yake yi domin ba jiragen ruwa damar tsallake shingen Iran.
Ya ce Amurka ta taimaka wa Ukraine a yaƙinta da Rasha, don haka yana tsammanin taimakon ƙasashen Turai kan babbar hanyar ruwa ta Hormuz da Iran ta toshe.
Rufe mashigar dai ya haifar tsadar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Mista Trump ya kuma ce zai jinkirta taron da zai yi da shugaban China Xi Jinping yayin da yake matsin lamba ga taimakon China domin bude mashigar.
Trump ya ce China da ƙasashen Turai da dama sun fi dogaro fiye da Amurka kan man da ke fitowa daga yankin Tekun Fasha.
"Waɗanda suka fi amfana da mashigin ne ya kamata su taimaka domin tabbatar da wani mugun abu bai faru ba a can," in ji Trump.
Ya shaida wa manema labarai cewa Amurka na tattaunawa da kusan ƙasashe bakwai domin neman taimakon su sa hannu wajen ceto mashigar Hormuz.
Tuni ƙasashen Japan da Australia suka ce ba za su tura sojojin ruwa ba. Amma Japan ta ce za ta fara fitar da rarar manta domin rage giɓin da na Iran ya haifar, duk da cewa ita ma ta dogara ne da man da ke fitowa daga yankin Gabas Ta Tsakiya.
Babu tabbas game da tsawon lokacin da yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran zai ɗauka da kuma tasirin da zai yi ga kasuwar mai a duniya, inda farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi a cikin makwanni biyun da suka gabata sakamakon ƙarancinsa.