Bayern na fargaba kan masu son ɗaukar Kane, Silva na son barin City

.

Asalin hoton, BBC Sport

Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Bayern Munich Uli Hoeness na kaffa-kaffa kan yadda ƙungiyoyin da ke taka leda a gasar ƙwararu a Saudiyya ke ci gaba da jan hankalin ɗan wasan gaban Ingila Harry Kane, a daidai lokacin da Bayern ɗin ke tattaunawa da ɗan wasan, kan tsawaita zaman sa a ƙungiyar har zuwa 2027. (Kicker - in German)

Ɗan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silava, ya shaida wa Manchester City aniyarsa ta shirinsa na barin ƙungiyar, idan kwantaraginsa ta ƙare a ƙarshen kakar wasanni. (Caught Offside)

Aston Villa, da Bayern Munich, da Chelsea da Liverpool na sa ido kan ɗan wasan bayan Crystal Palace Maxence Lacroix. (Teamtalk)

Liverpool da Newcastle United na son ɗaukar ɗan wasan Sporting ɗan asalin Colombia Luis Suarez. (Correio da Manha - in Portuguese)

Babu wata tattaunawa tsakanin ɗan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay, da ƙungiyoyin da ke taka leda a Saudiyya, a yayin da hankalinsa har yanzu ke Napoli da ke Italiya. (Fabrizio Romano)

Barcelona za ta tsawaita kwantarangin ɗan wasan gaba Poland Robert Lewandowski, da kwantaraginsa zai ƙare a kakar wassanin da ake, ciki har da rage masa albashi, da wasu haƙoƙi da za a ringa bashi na irin ƙwazon da yayi a wassanin da ya buga wa ƙungiyar. (Sport - in Spanish)

Juventus na duba yiwuwar ɗauko Lewandowski da ɗan wasan gaban Faransa Randal Kolo Muani, da ke buga wasa a matsayin ɗan wasan aro a Tottenham daga Paris St-Germain, zuwa ƙungiyar. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Chelsea da ɗan wasan bayan Faransa Malo Gusto, 22, sun ce Liam Rosenior shi ne gwarzon mai horar da ƙungiyar duk kuwa da sukar da ake yi masa kan rashin kataɓus ɗin da suka yi. (ESPN)

Inter Miami ta fara tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Brazil Casemiro kan yiwuwar komawa ƙungiyar don ci gaba da taka leda, yayin da zai bar Manchester United a ƙarshen kakar wasanni, sai dai akwai tayi da yake samun daga wasu manyan ƙungiyoyi a Turai da Saudiyya.