Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka fara shari'ar sojojin da ake zargi da kitsa kifar da gwamnatin Tinubu
Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta ce ta ƙaddamar da kotun soji wadda za ta yi shari'ar sojoji 36 da ake zargi da yunƙurin yin bore domin tuntsurar da gwamnatin ƙasar.
Shalkwatar tsaron ta fitar da wannan sanarwa ne a shafukanta na intanet, kimanin wata bakwai bayan ɓullar labarin cewa wasu gungun sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin shugaban ƙasar Bola Tinubu.
Tun farko a cikin wannan mako gwamnatin ta gurfanar da wasu mutum bakwai, waɗanda suka hada da tsofaffin sojoji da kuma fararen hula, bisa zargin su da hannu a yunƙurin juyin mulkin.
Najeriya ba ta fuskanci juyin mulki ba tun bayan komawa tsarin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
A cikin sanarwar da shalkwatar ta fitar ta ce hakan ci gaba ne a kan sanarwar da ta bayar a watan Janairun 2026 wadda ta yi bayani kan lamarin.
Sanarwar ta ce "wannan wani muhimmin mataki ne na tabbatar da ɗa'a da gaskiya da kuma mayar da hankali kan aiki a ƙoƙarin kare mutuncin ƙasa da kuma gwamnati.
"Za a yi shari'ar ne ta hanyar bin dukkanin ƙa'idojin da suka kamata, da nuna adalci ta yadda za a yi hukunci na gaskiya ba tare da tsoro ko kuma nuna bambanci ba," in ji sanarwar..
Ana gudanar da shari'ar ne a wani zauren shaƙatawar sojoji na barikin Guards Brigade da ke Asokoro a Abuja, babban birnin Niya.
An tsaurara tsaro a wurin da ake zaman sannan an hana ƴan jarida shiga zauren.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ce an kai sojojin da ake zargi wurin da ake zaman ne a cikin wata motar bas cikin tsattsauran tsaro da misalin ƙarfe 9 na safe.
Sannan an ga wasu lauyoyi sun isa wurin zaman gabanin isar sojojin, wadanda ake tunanin su ne za su kare waɗanda ake zargi.
A baya-bayan nan iyalan sojoji da sauran mutanen da aka kama sun ta hanƙoron ganin an yi adalci, bayan zargin da suka yi na cewa an hana su ganin iyalan nasu tun bayan kama su da aka yi bisa zargin yunƙurin kitsa juyin mulki.
Mece ce kotun soji, yaya take aiki a ƙarƙashin gwamnatin farar hula?
BBC ta tuntuɓi wani tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka mai ritaya, kuma ya bayyana mana yadda kotun soji ke aikinta karkashin mulkin farar hula.
"Kotun soji tana kama da babbar kotun jiha. Idan ba ka amince da hukuncin da aka yi ba, za ka iya ɗaukaka ƙara, duk da cewa sai majalisar sojoji sun tabbatar da hukuncin," in ji Kukasheka
Ya ƙara da cewa an yi kotun ne kaɗai don hukunta sojojin da suka yi laifi, amma wani lokaci suna gudanar da shari'ar fararen hula waɗanda suka kasance ƴan ƙasar.
"Kotun sojojin na cikin kundin tsarin mulki kuma tana da ikon gudanar da shari'o'i tare da yanke hukunci. Hukuncin ya haɗa da rage girman mukami da kora da zaman gidan yari, har ma da hukuncin kisa," in ji tsohon kakakin sojojin Najeriyar.
Ya ce duk mutumin da ake zargi, yana da damar ɗaukar lauya don kare shi a kotun na sojoji kuma ya danganci irin shari'ar da ake yi masa.
Kukasheka ya ce kotun sojojin ce kaɗai ke da ikon yi wa sojojin da ake zargi da yunkurin juyin mulki shari'a.
"Abin da ya rage kawai shi ne a tabbatar da hakan a kotu, wanda kuma masana shari'a ne ke da ikon yin haka. Kuma hujjojin da ke ƙasa ne za su tantance ko mutanen suna da laifi ko kuma saɓanin haka."
Wani masanin shari'a, Barrister Umar Bala, shi ma ya bayyana cewa babu wata kotu da ke da hurumin sauraron shari'ar sojojin da ake zargi, illa kotun soji.
"Kotun soji ce doka ta bai wa damar yin shari'a da ta danganci haka, kuma tana hukunta sojojin da suka ƙarya doka, aikata manyan laifuka, ko kuma saɓa wa dokokin soji," in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan kotu ta samu waɗanda aka kama da laifin yunkurin juyin mulki, to za ta yanke musu hukunci.
"Idan kotu ta samu waɗannan mutane da laifi, za ta iya yanke musu hukuncin kisa, saboda cin amanar ƙasa babban laifi ne," in ji Barrista Umar.
Su wane ne sojojin da ake tuhuma?
A watan Janairu ne rundunar sojin Najeriya ta ce ta kammala bincikenta kan jami'an soji 16 waɗanda aka kama a watan Oktoban, 2025 kan yunkurin kifar da gwamnati.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaru na rundunar sojin, Manjo-Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce sun kammala binciken su kuma sun miƙa rahotonsu zuwa ga "hukumomi na sama" domin ɗaukar mataki na gaba.
Duk da cewa bai bayyana sunayen sojojin da aka kama ba, amma ya ce sun gano waɗanda ke da hannu a yunƙurin kifar da gwamnati, kuma hakan ya saɓa wa tanade-tanade da ɗa'ar da ake son sojojin Najeriya su kasance a ciki.
"Binciken ya gano wasu sojoji da ake zargi da yunkurin juyin mulki, abu ne da ya saɓa ka'idar aikin soji," in ji sanarwar.