KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 21/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC

    ..

    Asalin hoton, BBC Hausa Collage

    Magoya bayan tsoffin ƴan takarar shugaban ƙasa a Najeriya Peter Obi, da kuma Rabiu Musa Kwankwaso sun kafa wata ƙungiya mai suna Obi–Kwankwaso (OK Movement) da ta soma tattaunawa domin ganin jam'iyyar ADC ta tsayar da su takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027 da ke tafe.

    Ƙungiyar, wadda aka kafa a Abuja a ranar Litinin, ta ce tuni ta soma samar da rassanta a jihohi 36 na ƙasar da Abuja, tare da naɗa shugabanninta na jihohi da yankuna domin jagorantar yaɗa ayyukanta.

    Sakataren watsa labaran ƙungiyar na ƙasa, Justin Ijeh, ya bayyana ta a matsayin gamin gambiza, don haɗa karfi da karfe tsakanin ƙungiyar magoya bayan Peter Obi ta Obidient Movement, da kuma ta magoya bayan Kwankwaso, wato Kwankwasiyya.

    Wannan dai na nuna wani irin sabon salo na sake ɗaure ɗamara yayin da ake ta ƙulla mu'amalar siyasa, sakamakon rashin tabbacin wanda zai lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na ADC kafin babban zaɓen 2027.

    Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin kungiyar ya bayyana cewa sabuwar kungiyar ta kunshi mambobi daga Kwankwasiyya, da Obidients, da jam'iyyar NNPP, da Labour da kuma wasu daga ADC.

  2. Dalilai huɗu da suka sa tattaunawar Iran da Amurka ke cikin ƙila-wa-ƙala

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Makomar tattaunawar Iran da Amurka ta shiga cikin rashin tabbas yayin da lokacin da aka kebe na tsagaita wuta ke daf daƙkarewa. Abin da ya sa ake gani a yanzu ba wai rashin cimma matsayar diflomasiyya ba ce kaɗai, har ma da kalamai masu zafi da tsauri tsakanin ɓangarori, barazana da kuma bayanai masu cin karo da juna daga dukkan ɓangarori.

    A cewar rahotanni da dama, babu tabbas cewa Iran za ta shiga tattaunawar da aka tsara za a yi wanda Pakistan ke shiga tsakani. Yayin da wasu majiyoyi ke bayyana cewa Iran na duba yiwuwar shiga tattaunawa, wasu kuwa sun ce ƙasar za ta iya janye wa watakila saboda yanayin da ake ciki.

    A ɗaya gefe, lamarin yana ci gaba da zama mai tsarkakiya bayan da rahotanni suka ce mataimakin shugaban Amurka wanda ke jagorantar tawagar tattaunawar, JD Vance, bai ma je Pakistan ba watakila saboda rashin tabbas da ake da shi kan tattaunawar.

    A nan, tattaunawar za ta iya kawo fatan cimma matsayar diflomasiyya ko kuma barazanar komawa fagen daga.

  3. Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami'an tsaro uziri

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A jamhuriyar Nijar hukumomin tsaron ƙasar na kira ga al'ummar yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da su yi uzuri ga dakarun ƙasar dangane da jinkirin zuwan jami’an tsaro idan aka kai hari, kamar yadda al’ummar ƙasar suka gani.

    Minista tsaron ƙasar ne Janar Salifou Mody ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da kafar Television ta RTN, inda ya ƙara da kira ga yan Nijar da su fahimci cewa jami’an tsaro ba za su iya kasancewa a kowane ƙauye ba, duba da cewa Nijar na da kusan ƙauyuka 32,000.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan ta'adda musamman a kan sojojin ƙsar.

  4. Rundunar IRGC ta bayyana Donald Trump a matsayin "maƙaryaci kuma mayaudari"

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labarai na Fars da ke da alaƙa da dakarun juyin-juya hali na Iran ya wallafa maganar wani babban sojan ƙasar a shafinsa na Telegram.

    Manjo Janar Abdullahi wanda ya rubuta saƙon da Farsi ya ce rundunar IRGC ta wahalar da Amurka da Isra'ila inda ta tilasta musu neman tsagaita wuta ido biyu.

    Ya ƙara da cewa rundunar ba za ta bar "maƙaryaci kuma mayaudarin shugaban Amurka ya rinƙa ƙirƙirar labaran ƙarya dangane da haƙiƙanin abin da ke faruwa ba," musamman a kan batun mashigar Hormuz.

  5. Har yanzu tawagar Iran ba ta je Pakistan ba

    Gidan talbijin na ƙsar Iran ya wallafa wani saƙo a shafin Telegram cewa kawo yanzu babu wata tawagar ƙasar da ta tafi zuwa Islamabad domin tattaunawa da Amurka.

    Saƙon ya yi watsi da abin da ya kira jita-jita dangane da tashin tawagar zuwa Islamabad ko kuma saukarta da kafafen watsa labaran ƙasashen duniya keta yaɗawa.

    Saƙon ya kuma nanata matsayar jami'an Iran da suka hada da kakakin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf wanda a baya ya ce Iran ba za ta amince da duk wata yarjejeniya ba a ƙarƙashin matsin lamba.

  6. China ta yaba wa Pakistan a ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka

    ..

    Asalin hoton, Pakistan Ministry of Foreign Affairs via X

    Jakadan China a Pakistan ya bayyana cikakken goyon bayan ƙsarsa ga ƙoƙarin shiga tsakanin da ƙasar Pakistan ke yi domin sasanta Amurka da Iran.

    Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce mataimakin firaiminista Ishaq Dar wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen Pakistan ya gana da Jiang Zaidong domin tattauna halin da ake ciki.

    A lokacin ganawar tasu, mista Zaidong ya bayyana farin cikinsa ga yadda Pakistan take ci gaba da ƙoƙarin samar da tattaunawa tsakanin Iran ɗin da Amurka.

  7. Har yanzu Iran ba ta yanke ko za ta je Pakistan tattaunawa da Amurka ba

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwana guda ya rage yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta kare, yayin da har yanzu babu tabbacin ko Iran din za ta halarci tattaunawar tsagaita wuta a Pakistan.

    Tehran ba ta tabbatar ko za ta tura tawaga ba, yayin da mataimakin shugaban Amurka JD Vance wanda zai jagoranci tawagar Amurka, har yanzu bai tashi daga Washington ba.

    Shugaba Donald Trump ya ce ba zai ɗage takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa a tashoshin Iran ba har sai an cimma yarjejeni

    Wakilin BBC ya ce mista Trump na son a sake bude mashigin Hormuz, kana Iran ta mika wa Amurka sinadarin Uranium din ta da ta sarrafa, abun da Iran din ta bayyana a matsayin wasan yara.

    Jagoran masu tattaunawar zaman lafiyar na bangaren Iran Mohammad Bagher Qalibaf, ya bayyana cewa ba za za su amince da tattaunawa ƙarƙashin matsin lamba ba

  8. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da warhaka da fatan an yi wayi garin ranar Talata lafiya. Yau ma kamar kullum mun dawo muku da shafin namu na kai tsaye inda muke kawo muku muhimman labarai dangane da al'amuran yau da kullum.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa.

Trending Now