Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Muna godiya da bibiyarmu.

    Aisha Babangida ke cewa mu kwana Lafiya.

  2. Toshe jiragen ruwan Iran: Waɗanne tashoshi ne abun zai fi shafa?

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mintuna kaɗan bayan fara toshe zirga-zirgar jiragen ruwan Iran a hukumance, Donald Trump ya gargadi jiragen ruwan rundunar juyin juya halin Iran cewa za a lalata su idan suka kusanci yankin.

    Trump ya ce ɗaukar mataki a kansu zai kasance cikin gaggawa da tsauri kamar yadda ake yi wa jirage masu safarar miyagun abubuwa.

    Amurka ta bayyana cewa za ta hana duk wata hanya ta shiga ko fita daga gabar tekun Iran da tashoshin jiragen ruwanta.

    A martanin da ta mayar, Iran ta yi gargadin cewa idan aka taɓa tashoshin jiragenta, babu wani tashar jiragen ruwa a yankin da zai kasance cikin aminci.

    Manyan tashoshin kasuwancin Iran suna kudancin ƙasar ne inda ake da fiye da tashoshi 30, ƙanana da manya wanda wanna takunkumin zai iya shafa da suka hada da

    • Tashar Shahid Rajaee, shine mafi girma a fannin kasuwanci, wadda ke lodin kwantena kuma tana haɗi da layin dogo da hanyoyin mota na ƙasa.
    • Tashar Shahid Bahonar, duk da ƙanƙantarta, tana da muhimmanci wajen jigilar fasinjoji.
    • Tashar Imam Khomeini, wadda ake ɗauka a matsayin cibiyar shigo da muhimman kayayyaki zuwa Iran.
    • Tashar Bushehr, muhimmiyar tashar yankin.
    • Tashar Chabahar, wadda ita ce kaɗai tashar tekun waje a Iran.
    • Tashar Khorramshahr, ɗaya daga cikin tsofaffin tashoshi masu muhimmanci a yankin Arvandrud, mai amfani a kasuwanci da tsaro.
    • Tashar Abadan, ɗaya daga cikin tashoshin mai da kasuwanci.
    • Tashar Kharg, mafi muhimmanci wajen fitar da man fetur daga Iran.
    • Tashar Mahshahr, mai alaƙa da masana’antar sinadarai.
    • Tashar Assaluyeh, cibiyar makamashi da gas.
    • Tashar Lengeh, mai aiki a kasuwancin yankin.
    • Tashar Jask, wadda ke da tashar mai da ake shirin faɗaɗa ta.
  3. Wani abin fashewa ya sake kashe babban soja a Borno

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani babban jami’in soja ya rasa ransa bayan da wani bam da ake hadawa a gida ya fashe a yankin Monguno da ke Jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya.

    Sojojin Najeriya sun ce harin ya biyo bayan wani farmaki da aka kai kan daya daga cikin sansanoninsu a daren Lahadi a yankin da ke kan iyaka da ƙasar Chadi.

    A cewar rundunar, jami’in da ya jagoranci tawagar da ta je duba halin da ake ciki bayan harin ne ya mutu lokacin da motarsa ta taka abin fashewar. Wasu sojoji shida ma sun mutu a fashewar.

    Rundunar ta ƙara da cewa dakarunta sun fafata da maharan a wani musayar wuta, kuma sun ci gaba da mamaye yankin bayan harin.

    Ta ce an kashe wasu daga cikin maharan amma ba ta bayar da cikakken bayani kan adadin ba.

    A makon da ya gabata ne sojojin sun ce sun dakile wani harin ta’addanci da aka kai sansaninsu a Benisheikh, shi ma a Jihar Borno inda jami’ai suka tabbatar da mutuwar wasu sojoji, ciki har da wani Birgediya Janar, duk da cewa ba su bayyana adadi ba.

    Kungiyoyin ‘yan Boko Haram da ISWAP sun shafe sama da shekaru goma suna kai hare-hare kan sansanonin soji a arewa maso gabashin Najeriya, inda Jihar Borno ke zama cibiyar rikicin.

  4. Me ya sa gwamnan Kano ke jan ƙafa kan naɗin mataimakinsa?

    ,....

    Asalin hoton, Kano State Gov

    Duk da cewa batun sauya sheƙar wasu manyan ƴan siyasar Kano zuwa jam'iyyar ADC shi ne abin da ke tashe a yanzu, amma wani abu da ke ta yawo a zukatan al'ummar jihar shi ne batun mataimakin gwamna da babu shi.

    Yanzu an kwashe kusan mako uku tun bayan da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam ya sauka daga muƙaminsa bayan rikicin siyasa da ya turnuƙe sanadiyyar sauya sheƙar gwamnan jihar zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

    Tun bayan saukar tasa ne ake ci gaba da hasashen wanda zai maye gurbinsa.

    Aminu Abdussalam ya sauka daga muƙaminsa ne lokacin da gwamnan ke halartar babban taron jam'iyyar APC na ƙasa da aka gudanara a Abuja a ƙarshen watan da ya gabata.

    Sai dai siyasar jihar ta ƙara ɗaukar zafi ne tun bayan komawar Gwamna Abba, inda ake sa ran zai sanar da magajin nasa, amma har yanzu shiru

  5. Shugaban Hezbollah ya ƙi amincewa da tattaunawa tsakanin Lebanon da Isra’ila

    ....

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Shugaban Hezbollah, Naim Qassem, ya yi watsi da shirin tattaunawa tsakanin gwamnatin Lebanon da Isra’ila, yana mai cewa tattaunawar “ba za ta haifar da komai ba.”

    Hakan na zuwa ne gabanin tafiyar jami’an Lebanon zuwa Washington domin ganawa da jami’an Isra’ila da na Amurka a ranar Talata.

    Gwamnatin Lebanon ta haramta ayyukan sojin Hezbollah mai samun goyon bayan Iran a farkon watan Maris, kwanaki kaɗan bayan fara yaƙi da Isra’ila, inda Shugaban ƙasar Lebanon, Joseph Aoun, ya soki ƙungiyar bisa jefa ƙasar cikin rikicin yankin.

    A cikin kalamansa da kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaƙa da Iran ya ruwaito, Qassem ya ce Isra’ila na harin dukkan ƙasar Lebanon, yana mai cewa alhakin gwamnati ne ta tashi tsaye ta shirya rundunar soji.

    Ya ƙara da cewa: “Matsayinmu a matsayin ‘yan gwagwarmaya shi ne ba za mu ja da baya ba, kuma ba za mu miƙa wuya ba.”

  6. Trump ya mayar da martani kan hoton da ya nuna shi kamar Yesu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da martani kan wani hoto da ya wallafa a shafin sada zumunta kafin daga baya aka, wanda ya nuna shi tamkar Yesu.

    Trump ya ce hoton ba ya nufin a nuna shi a matsayin Yesu, illa kawai yana wakiltar shi ne a matsayin “likita da ke warkar da mutane kuma ya sa su ji daɗi.”

    Ya kuma zargi kafafen yaɗa labarai da “ƙirƙirar labari” kan batun, yana mai cewa sun fassara abin da ba haka yake ba.

  7. Jirgin ruwa ya ratsa ta mashigar Hormuz duk da barazanar Trump, Thomas Spencer - Sashen tantancewa ta BBC

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jirgin ruwa ya ratsa ta mashigar Hormuz duk da takunkumin da Amurka ta kakaba kan jiragen da ke da alaƙa da Iran da kuma tashoshin jiragen ruwan ƙasar.

    Rahoton sashen tantancewa ta BBC, ya tabbatar da cewa wannan shi ne jirgi na farko da ya bi ta mashigar tun bayan fara shirin toshe mashigar..

    Bayanan wani shafi da ke bibiyar jiragen ruwa na MarineTraffic sun nuna cewa wani jirgin ɗaukar kaya da ya tashi daga Indiya yana ci gaba da tafiyarsa zuwa Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa.

    Haka kuma, bayanan sun nuna cewa wani jirgi mai suna Reach Starry ya sauya hanya yayin da yake kusantar mashigar Hormuz.

    Har yanzu ba a tabbatar da ko wannan jirgi, wanda ke ƙarƙashin takunkumin Amurka, yana da niyyar wucewa ta mashigar ba.

  8. Ba zan nemi afuwar Fafaroma Leo ba - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai nemi afuwa daga Fafaroma Leo ba.

    Ya bayyana cewa “babu wani dalili na neman afuwarsa,” yana mai ƙara da cewa Fafaroman “ya yi kuskure.”

    A jiya ne Trump ya zargi shugaban mabiya darikar Katolika na duniya da kasancewa “mai rauni a gaban laifi” da kuma “matsala ga manufofin ƙasashen waje,” a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social. Daga bisani ya shaida wa ‘yan jarida cewa “ba ya goyon bayansa.”

    Fafaroman ya kasance mai sukar yaƙin Iran, inda ya bayyana barazanar Trump na “shafe Iran” a matsayin abin da “ba za a amince da shi ba,” tare da kira gare shi da ya nemi hanyar fita daga rikicin da kuma kawo ƙarshen tashin hankali.

  9. Trump ya ce jadawalin tunkarar rikici da Iran bai sauya ba

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa jadawalin da ya tsara na tunkarar rikici da Iran bai sauya ba.

    Da yake magana da ‘yan jarida a Fadar White House, Trump ya ce a halin yanzu babu yaki kai tsaye da ke gudana, sai dai “toshe zirga-zirga,r jiragen ruwan a mashigar Hormuz” yana mai cewa Iran ba ta yin wata harkar kasuwanci a wannan lokaci.

    Trump ya ce a halin yanzu Iran ba ta da harkokin kasuwanci a mashigar kuma “za mu iya ci gaba da riƙe wannan yanayin cikin sauƙi.

  10. Wike ya musanta zargin hana jam'iyyar ADC amfani da dandalin Eagle Square

    ....

    Asalin hoton, Nyesom Wike/X

    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta zargin da jam’iyyar hadaka ta ADC ta yi cewa an hana ta amfani da dandalin Eagle Square.

    Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin rangadin duba ayyukan gine-gine.

    Ya ce zargin cewa an hana wasu jam’iyyu amfani da dandalin Eagle Square ba shi da tushe, yana mai kiran hakan “ƙoƙarin neman tausayawar jama’a ne kawai.”

    A cewarsa, babu wata buƙata a hukumance da jam'iyyar ADC ta gabatar da sunan tana son ta yi amafi da dandalin.

    Ya jaddada cewa Eagle Square a buɗe yake ga dukkan jam'iyya da kungiyoyi matuƙar sun bi ka’ida kuma sun biya kudin da aka ƙayyade.

    Sai dai jam’iyyar ADC ta dage cewa ta bi dukkan matakan da doka ta tanada, inda ta ce ta riga ta mika takardar buƙata domin neman amfani da dandalin. Jam’iyyar ta bayyana cewa zargin cewa ba a karɓi wata takarda daga gare ta ba ba gaskiya ba ne.

    Hakazalika, akwai wata takardar bukatar neman amfani da wurin da ake dangantawa da jam’iyyar da ke yawo a shafukan sada zumunta, abin da ya ƙara janyo muhawara a tsakanin jama’a kan sahihancin batun da kuma ko an bi ƙa’ida yadda ya kamata.

  11. Firaministar Italiya ta soki kalaman Trump kan Fafaroma Leo

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministar Italiya, Giorgia Meloni, ta bayyana kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump kan Fafaroma Leo XIV a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba.

    Meloni ta ce a cikin wata sanarwa cewa kalaman Trump game da Fafaroma ba su dace ba,” tana mai jaddada cewa Fafaroma shi ne shugaban Cocin Katolika, kuma yana da cikakken ‘yanci da kuma nauyin yin kira ga zaman lafiya da yin allawadai da duk wani nau’in yaƙi.

    Wannan martani ya biyo bayan da Trump ya zargi Fafaroma da kasancewa “mai rauni a fuskantar laifi” da kuma cewa “yana zama matsala ga manufofin ketare” a shafinsa na Truth Social, sannan daga baya ya shaida wa ‘yan jarida cewa ba ya goyon bayansa.

    Fafaroman ya kasance mai sukar yakin Iran, inda ya bayyana barazanar Trump na “shafe Iran gaba ɗaya” a matsayin abin da ba a yarda da shi ba.

  12. Gwamnatin Yobe ta yi ƙarin haske kan harin jirgin sojoji

    ...

    Asalin hoton, Yobe State Government

    Gwamnatin Jihar Yobe ta yi ƙarin haske kan harin jirgin sojojin Najeriya da aka kai a yankin da ke kan iyaka da Jihar Borno, tana mai cewa wurin da aka kai harin “ba mallakar kowa ba ne kuma an kai harin ne kan sansanin ‘yan Boko Haram, ba kan fararen hula ba.

    Rahotanni sun ce an kashe daruruwan mutane a ranar Asabar a lokacin harin kan abin da aka bayyana a matsayin babban sansanin ƙungiyar ISWAP a arewa maso gabas.

    Wasu rahotanni daga mazauna yankin da hukumomin agaji sun ce adadin waɗanda suka mutu na iya kai wa kusan 200, yayin da wasu kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ce adadin ya bai kai ba wanda suka ce daga mutum 10 zuwa sama da 50 ne suka mutu, tare da wasu da suka jikkata da ake kula da su a asibiti.

    A cikin sanarwa da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya, ya fitar a ranar Litinin, ya ce harin ya faru ne a Jilli da ke Ƙaramar Hukumar Gubio a Jihar Borno, wadda ya bayyana a matsayin sansanin ‘yan tada ƙayar baya da ake amfani da shi wajen shirye-shiryen hare-hare.

    Ya ce wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Geidam a Jihar Yobe sun je kasuwar mako ta Jilli ne, inda harin ya rutsa da su.

    Ya kuma bayyana Jilli a matsayin “yanki da ba mallakar kowa ba ne,” yana mai cewa babu wata kafaffen mazauni na fararen hula a wurin. Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ayyukan soji domin rushe sansanonin ‘yan bindiga da dawo da tsaro a yankin.

    A halin yanzu, rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta fara bincike kan zargin asarar rayukan fararen hula da ke da alaƙa da farmakin.

  13. Firaministan Pakistan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin warware rikicin Amurka da Iran

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif, ya bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin warware rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.

    A cewar kamfanin dillancin labaran AFP, Sharif ya shaida wa majalisar ministocinsa cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Iran tana nan daram, kuma a halin yanzu ana yin dukkanin ƙoƙari domin magance sauran batutuwan da suka rage.

    Ya ce ana ci gaba da tattaunawa da matakan diflomasiyya domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da rage tashin hankali a yankin.

  14. 'Babu ƙasar da ke da ikon toshe zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz'

    Shugaban hukumar kula da harkokin teku ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce babu ƙasar da ke da ikon toshe zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz.

    Arsenio Dominguez, sakataren hukumar ta Ƙungiyar Kula da Jiragen Ruwa ta Duniya (IMO), ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, “Bisa dokar ƙasa da ƙasa, babu ƙasa da ke da ikon hana ‘yancin wucewa ko zirga-zirga cikin aminci ta mashigar Hormuz da ake amfani da ita wajen safarar man duniya.”

    Ya ƙara da cewa, “Dora haraji ko takunkumi a irin wannan mashigar ya saɓa wa dokokin teku na ƙasa da ƙasa da kuma dokokin da aka saba bi.”

    A halin da ake ciki, sanarwar sojojin Amurka ta ce an fara toshe tashoshin jiragen ruwan Iran da ke Tekun Oman da Tekun Fasha a hukumance ‘yan mintuna da suka wuce.

    An ce ana gudanar da wannan aiki ne bisa umarnin shugaban Amurka, Donald Trump, kuma manufarsa ita ce hana jiragen ruwa shiga ko fita daga tashoshin jiragen ruwan Iran a yankin.

  15. Trump ya yi 'kuskure' kan barazanar shafe Iran - Starmer

    Firaiministan Birtaniya Keir Starmer

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firaiministan Birtaniya Keir Starmer

    Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ya ce barazanar da Donald Trump ya yi a makon da ya gabata ta ''shafe Iran'' idan ba ta amince ta buɗe mashigar Hormuz ba "kuskure" ne.

    Wannan kalamin na Starmer sun fi ƙarfi a kan waɗanda ya yi amfani da su makon da ya gabata, lokacin da ya ce ba ya da kalmomin da zai iya amfani da su wajen mayar da martani kan barazanar ta Trump.

    Lokacin da yake magana a majalisar wakilan Birtaniya, Keir Starmer ya ce fafaren hular Iran sun sha wahala sosai a hannun gwamnati tun cikin shekaru masu yawa da suka gabata.

  16. NATO ta ce ba za ta shiga shirin rufe mashigar Hormuz ba

    Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar tsaro ta NATO sun sanar cewa ba za su shiga shirin Donald Trump na rufe mashigar Hormuz ba. Maimakon haka, sun ce za su iya shiga tsakani ne kawai bayan rikicin ya ƙare.

    Wannan mataki na iya jawo rashin jin daɗin shugaba Amurka, Donald Trump.

    Faransa ta riga ta bayyana shirin kafa rundunar haɗin gwiwa mai “manufar zaman lafiya” tare da Birtaniya, domin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin ‘yanci a mashigin Hormuz.

    A cewar sanarwar sojojin Amurka, an fara toshe zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran a hukumance ‘yan mintuna da suka wuce.

    An ce wannan aiki yana gudana ne bisa umarnin Donald Trump, kuma manufarsa ita ce hana jiragen ruwa shiga ko fita daga tashoshin jiragen Iran a yankin Tekun Fasha da Tekun Oman.

  17. An fara toshe tashoshin jiragen ruwa na kudancin Iran a hukumance

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Bisa sanarwar sojojin Amurka, an fara toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran da ke Tekun Oman da Tekun Fasha.

    Hedikwatar rundunar Amurka ta CENTCOM ta ce ana gudanar da aikin ne bisa umarnin Donald Trump, kuma manufarsa ita ce hana jiragen ruwa shiga ko fita daga tashoshin jiragen ruwan Iran a yankin Tekun Fasha da Tekun Oman.

    Iran dai ta gargadi cewa babu wani tashar jiragen ruwa a yankin da zai kasance cikin aminci idan aka taɓa tsaron tashoshin ta.

    Haka kuma Iran ta ce tana ɗaukar duk wani jirgin ruwan yaƙi da ya kusanci mashigar Hormuz a matsayin take yarjejeniyar tsagaita wuta,.

  18. Ana ci gaba da nemo hanyoyin warware rikicin Gabas ta Tsakiya - Shehbaz Sharif

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya ce yunƙurin warware rikicin Amurka da Iran na ci gaba.

    Wannan na zuwa ne bayan tattaunawa tsakanin ƙasashen guda biyu da aka gudanar a babban birnin Pakistan, Islamad a ƙarshen mako, ba ta cimma komai ba.

    "Tsagaita wutar na ci gaba a daida lokacin da nake maganar nan, ana kuma yunƙurin samar da mafiya dangane da sauran batutuwan da ake taƙaddama a kansu, kamar yadda Sheriff ya shaida wa majalisarsa.

  19. An ƙone gawar mawaƙiyar India, Asha Bhos-le

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Asha Bhos-le ta yi waƙoƙi fiye da 12,000 a rayuwarta.

    Fitattun mutane daga masana’antar shirya fina-finai da kiɗe-kiɗe da wasanni na ƙasar India sun hallara a birnin Mumbai domin yi wa fitacciyar mawaƙiya Asha Bhos-le bankwana, wadda ta rasu tana da shekaru 92.

    Taurari da suka haɗa da tsohon kyaftin ɗin wasan kwallon cricket, Sa-chin Ten-dul-kar sun taru a gidanta kafin a kai ga Kone gawarta, cikin wani salo na girmamawa a filin wasa na Shivaji Park inda za'a yi mata jana'izar ban girma.

    Dubban mutane ne suka fito kan tituna yayin da ake wucewa da gawar. Asha Bhos-le ta shafe shekaru tana jan zaren ta wajen rera waƙoƙin da ‘yan Bollywood ke amfani da su.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Dandazon masu alhini yayin da suke sanya gawar mamaciyar a mota domin kai ta wurin da aka ƙonata.
  20. Rundunar sojin Amurka ta ce nan ba da jimawa ba za ta rufe Hormuz

    Rundunar sojin Amurka ta aika da sanarwa ga masu harkokin jiragen ruwa, inda ta ce za ta fara ƙaddamar da takunkumi kan hana jiragen da ke ta'ammali da Iran a ruwa a tekun Oman da na gabashin yankin Larabawa a mashigar Hormuz.

    Rundunar ta ce hare-haren zai shafi dukkanin jiragen ruwa ba tare da la’akari da tutar ƙasar da suke ɗauke da ita ba.

    Rundunar sojin ta Amurka ta ce duk wani jirgin ruwa da ya shiga ko ya fita daga yankin da aka ƙaƙaba wa takunkumi ba tare da izini ba, zai fuskanci tarewa ko karkatarwa ko kuma a kama shi.

    Sanarwar ta kuma ce takunkumin zai shafi dukkan gaɓar tekun Iran, ciki har da tashoshin jiragen ruwa da wuraren fitar da mai, ba tare da iyakancewa ga wasu wurare kaɗai ba.

    Iran ta yi barazanar ɗaukar matakin ramuwar gayya kan shirin takunkumin, wanda ake sa ran zai fara aiki nan ba da jimawa ba.

Trending Now