Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 23/04/2026

Taƙaitattu

  • Sojojin Najeriya sun kashe gomman ƴan bindiga da lalata jiragen ruwansu a Tafkin Chadi
  • Trump ne zai yanke shawara kan lokacin da za a ƙare yaƙin Iran- White House
  • Wane ne Sarki Sulaimanu, Sarkin Kano na farko a tarihi?
  • 'Yawan kuɗin takardun neman takara na APC illa ne ga cigaban ƙasa'
  • PSG na son Fernandes, Barca na harin Silva da Neto
  • Iran na da tarin sindarin uranium - amma me ya sa ba za ta iya mallakar makamin nukiliya ba?

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar, Isiyaku Muhammad da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Ba zan yi amfani da makamin nukiliya a kan Iran ba - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Trump ya ce ba zai yi amfani da makamin nukiliya kan Iran ba yana mai cewa Amurka ta cimma manufofinta na soji ta hanyoyin da suka dace.

    Trump ya ce: "Me yasa zan buƙaci hakan?" a lokacin da wani ɗan jarida ya tambaye shi ko zai yi amfani da makamin nukiliya a Iran, inda ya ce tambayar ta "rashin hankali" ce.

    Ya ƙara da cewa: "me ya sa zan yi amfani da makamin nukiliyan bayan duk mun lalata inda ya kamata ba tare da makamin ba?"

    "Bai kamata a bari a yi amfani da makamin nukiliya a kan kowa ba," in ji Trump

  2. Trump ya ce yana son ƙulla yarjejeniya mai kyau da Iran

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba ya fuskantar wata matsin lamba domin ya dakatar da yaƙi da Iran.

    A yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, ya ce yana fatan cimma yarjejeniya mai kyau da Iran.

    Trump ya bugi ƙirjin cewa Amurka ce ke da iko da mashigar Hormuz a yanzu, kuma har sai an cimma yarjejeniya da Iran, za a buɗe.

    Ya ƙara da cewa ba ya son Iran ta samu miliyoyin daloli daga man da ta ke sayarwa a lokacin tsagaita wuta.

  3. An kashe masu neman itacen girki a Borno

    Zulum

    Asalin hoton, Zulum's Twitter

    Aƙalla fararen hula 17 ne mayaƙa suka kashe a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Wani mazauni yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an kai musu harin ne a lokacin da suke tattara itace a garin Gwoza da ke jihar Borno.

    Harin na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta sanar da samun galaba kan masu kai hare-hare a ƴan kwanakin nan.

    Zuwa yanzu babu wani ƙarin bayani daga hukumomin Najeriya kan harin.

  4. Trump ya ce lokaci na ƙure wa Iran

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Trump ya wallafa wani sabon saƙo a shafinsa na Truth Social, inda ya ƙalubalanci rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke wallafawa cewa ya matsu a kawo ƙarshen yaƙin.

    Trump ya ce yana da isasshen lokaci a yaƙin da ake yi.

    "Ina da isasshen lokaci, amma Iran ba ta da wannan lokacin - Lokaci yana ƙure mata," in ji Trump.

    Ya ƙara da cewa: "Za a cimma yarjejeniya ne kawai idan sun yi daidai da abin da Amurka ta ke so, da sauran ƙawayenta a duniya."

  5. An ji ƙarar harbe-harbe ta sama a birnin Tehran

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar Iran sun ba da rahoton jin ƙarar harbe-harbe a Tehran babban birnin ƙasar.

    Kamfanin dillancin labaran IRNA na ƙasar Iran ya bayyana cewa, an yi ta samun rahotannin harbe-harbe na sararin samaniya da jiragen sama a yammacin birnin Tehran.

    Su ma Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr mai alaƙa da Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya bayar da rahoton cewa: "An ji ƙarar jiragen sama a wasu sassan Tehran da suke daƙile hare-haren ta sama."

    BBC ta kuma yi magana da wasu mutane a Tehran waɗanda suka ce sun ji ƙarar harbi daga na'urorin tsaron sararin samaniya.

    Ba a dai bayyana halin da ake ciki ba tukuna, amma za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu.

  6. Majalisa ta buƙaci a dakatar da yaƙin neman zaɓe a jihohin arewa 8 saboda matsalar tsaro

    Seante

    Asalin hoton, @NGRSenate/X

    Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta duba yiwuwar dakatar da yaƙin neman zaɓen 2027 a wasu jihohin arewa guda takwas da ke fama da matsalar tsaro.

    Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi ne ya gabatar da ƙudurin a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda ya ce akwai buƙatar a duba yanayin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a ƙasar.

    Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ningi ya ce bai kamata ƴan majalisar su kauda kai daga matsalar tsaron da ke damun wasu sassan ƙasar saboda su suna zaune a Abuja.

    "Mataki ne da ya zama wajibi mu ɗauka. Ko dai a dakatar da duk wasu tarukan siyasa a faɗin ƙasar ko kuma a dakatar a jihohin da ke da matsala," in ji Sanata Ningi.

    Sanatan ya lissafo johohin Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi da wasu sassan Kano.

    "Ya kamata mu dakatar da duk wasu abubuwan siyasa a waɗannan jihohin har sai lamuran tsaro sun daidaita," in ji shi.

    Gargaɗin na Sanata Ningi na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, ciki har da hare-hare kan sansanonin soji a ƙasar da kuma garkuwa da mutane.

  7. Isra'ila ta ce amincewar Amurka kawai take jira domin ganin bayan Iran baki ɗaya

    Israel Katz

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce ƙasarsa a shirye take ta ci gaba da yaƙin da take yi da Iran tare da mayar da ita baya da lalata duk wani ci gaban da ta samu.

    Israel Katz ya ce sojojin Isra'ila suna jiran amincewar Amurka ne kawai domin ganin bayan tsatson Khamenei baki ɗaya bayan kisan Ayatollah Ali Khamenei, a harin da Amurka da Isra'ila suka kai a ranar farko ta fara yaƙin.

    Ya kuma yi barazanar "ɗaiɗaita Iran da maida ta baya" ta hanyar kai hari cibiyoyin makamashinta da wuraren tattalin arziki.

    "Hare-haren da za mu kai a wannan karon za su zama munana da rashin tausayi a wurare masu muhimmanci, wanda zai durƙusar da ci gaban ta," in ji Katz.

  8. Komai na tafiya yadda na tsara a yaƙin Iran - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce da alamu komai na tafiya yadda ya tsara a yaƙin Iran.

    Yayin da ya ke amsa tambaya daga BBC kan matakan da ya ɗauka kan Iran da barazanar shafe ƙasar da ya yi, Trump ya ce "Duk matakan da na ɗauka, da alama suna aiki sosai."

    Wakilin BBC ya zanta da Trump ta waya inda ya tambaye shi kan kalamansa na shafe Iran ko barazana ce da ya yi ko niyyar amfani da makamin nukiliya.

    Sai dai Donald Trump ya ce: "Ɗaya ɓangaren ba su da haƙurin cimma yarjejeniya. Ko ma mene ne na yi, da alama ya yi aiki."

    Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa a yanzu "Amurka ba ɓukatar NATO da ƙawayenta ko kaɗan" a yaƙin da take yi da Iran amma "ya kamata a ce sun sa hannu a yaƙin"

  9. An tabbatar da naɗin Dr Muttaqha Darma a matsayin sabon ministan gidaje

    Muttaqha Rabe Darma

    Asalin hoton, .

    Majalisar Dattijan Najeriya ta tabbatar da naɗin Dakta Muttaqha Rabe Darma a matsayin ministan gidaje.

    Hakan ya biyo wasiƙar da shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar a Jiya, yana buƙatar ta amince da naɗin.

    A yayin zaman majalisar, wadda Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya jagoranta, ƴan majalisar sun yi wa Dr Darma tambayoyi da dama kan dabarun da zai yi amfani da su wajen magance matsalar ƙarancin gidaje da ƙasar ke fama da ita.

    Bayan gamsuwa da amsoshin sa, Majalisar ta amince da naɗa shi.

    A ranar 21 ga watan Afrilun 2026 ne Shugaba Tinubu ya yi wasu sauye-sauye a majalisar ministocin ƙasar, inda ya cire tsohon ministan gidaje, Ahmed Musa Dangiwa da na kuɗi, Wale Edun.

  10. An yi kutse a kundin bayanan lafiyar Birtaniya

    Gwamnatin Birtaniya ta tabbattar da cewa an samu kutse a kundin bayanan lafiya, inda ake ƙoƙarin sayar da bayanan lafiyar mutum aƙalla dubu ɗari biyar a China ta intanet.

    Ministan Fasaha Ian Murray ya ce dukkanin mutanen da suka bayar da bayanan su ga UK Biobank - wata gidauniyar da ke tattara bayanan lafiya domin taimakawa wajen ganowa da managance ciwuka masu tsanani kamar cutar mantuwa da cancer, an gano bayanan su a shafin Alibaba.

    Mista Murray ya ce an sanya bayanan sau uku, amma ba a samun wanda ya taya ba, sai dai kuma babu sunaye da wasu bayanan su baya ga na lafiya.

    Sai dai tuni aka sauke bayanan, kuma gidauniyar na bincike kan lamarin.

  11. Sojojin Amurka sun kama wani jirgin ruwan dakon mai da suka ce na ɗauke da man Iran

    jirgin ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce dakarun Amurka sun kama wani jirgin ruwan dakon mai a tekun Indian Ocean, da suka yi iƙirarin yana ɗauke da man Iran.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna sojojin suna dira kan jirgin daga cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu.

    Rundunar sojin Amurka ta ce ba a san jirgin ko ta wace ƙasa bace, amma wani shafin intanet da ke bibiyar jirage, ya nuna jirgin da tutar Guyana, kuma yana kan hanyar zuwa China.

    Wannan ne karo na biyu da Amurka ke ƙwace jirgin ruwa a wannan makon.

    Sojojin ruwan Amurkar sun kai hari kan wani jirgin Iran a ranar Lahadi, inda suka zarge shi da ƙoƙarin tsallake shingen da ta sanya.

  12. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƴan bindiga da dama a jihar Yobe

    SOJOJI

    Asalin hoton, NDHQ

    Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta sun kashe wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai 24 a wani gumurzu da sukai da su a arewa maso gabashin ƙasar.

    Wani jami’i ya ce sojoji 2 sun jikkata, bayan da akai musu kwanton ɓauna da safiyar yau Alhamis a jihar Yobe.

    Ba a bayyana ƙungiyar da ke da alhakin kai harin ba.

    Sai dai Ƙungiyar Boko Haram ta ƙara kaimi wajen kai hare-hare a watannin baya-bayan nan, inda take kai hare-hare kan sansanonin soji da ƙauyuka a jihohin Borno da kuma Yobe.

    Jerin hare-haren da ƙungiyar ta kai na tsawon kusan shekaru 20 ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba sama da mutum miliyan 2 da muhallansu.

  13. Tinubu na neman sahalewar Majalisa domin karɓo bashin $500m daga Jamus

    TINUBU

    Asalin hoton, BAYO/X

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawan ƙasar ta amince da ciyo bashin fiye da dala miliyan 516 daga babban bankin Jamus (Deutsche bank) , domin aikin wani ɓangare na babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.

    A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Godswil Akpabio, Shugaban ƙasar ya ce an tsara aikin gina kilomita 100 na titin ne domin ya haɗa Arewa maso yammacin ƙasar da kudu maso yammaci, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

    A cewar sa, babbar hanyar za ta taso ne daga Illela a jihar Sokoto, ta bi ta jihohin Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun, ta kare a Badagry da ke Jihar Legas.

    A cewar wasiƙar, za a yi amfani da bashin wajen gina sashe na 1, rukuni na 1 da na biyu, mai nisan kilomita 120, cikin bakidaya kilomita 1,000.

    Za a biya bashin ne cikin shekaru 9, amma za a iya ƙara lamunin aƙalla shekaru uku.

    Shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni Majalisar ministocinsa ta amince da tsarin karɓo bashin, inda ya buƙaci majalisar Dattawan ta sanya bashin cikin tsarin karbo bashi na ƙasar.

    Wasiƙar shugaban ƙasar ta bayyana cewa babbar hanyar za ta taimaka wajen bunƙasa kasuwanci, da samar da isashen abinci, da haɗin kan ƙasa.

    Sanata Akpabio ya miƙa buƙatar ga kwamitin kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, kuma ana sa ran zai bayar da rahoto nan da mako guda.

  14. Tarayyar Turai za ta samar da tallafin fiye da Euro miliyan 200 ga Yammaci da tsakiyar Afirka

    Hukumar Tarayyar Turai ta sanar da bayar da tallafin jinƙai na Euro miliyan ɗari biyu da talatin da biyar domin tallafawa marasa ƙarfi a Yammaci da tsakiyar Afirka.

    Tallafin zai je ne ga mutanen da rikice rikicen da ake samu a yanzu suka shafa, da matsalar ƙarancin abinci, da waɗanda suka rasa muhallansa, da alummomin da ake rikici cikinsu, da waɗanda tallafi ke wuyar isa garesu.

    Najeriya za ta samu Euro miliyan 33,(fiye da Naira biliyan 52) domin taimakawa a fannin kiwon lafiya, da samar da abinci mai gina jiki a Arewa maso gabashi da Arewa maso Yammacin ƙasar.

    Za kuma a ware Euro miliyan 75 ga tsakiyar Sahel, da Euro miliyan 16 zuwa Kamaru, sai Euro miliyan 22 zuwa Jamhuriyar tsakiyar Afirka, Chadi kuma za ta samu Euro miliyan 72, Mauritania kuwa za ta samun tallafin kusan Euro miliyan 5.

    A cikin wata sanarwa da kwamishiniyar samar da daidaito ta hukumar Hadja Lahbib ta fitar, ta ce Yammaci da tsakiyar Afirka na fama da matsalolin jin ƙai waɗanda suka samo asali daga rikice rikicen da ake samu, da talauci, da yunwa, da rashin dai daito, da kuma matsalolin sauyin yanayi.

    A cewar sanarwar, Yammaci da tsakiyar Afirkan na fama da waɗannan ɗimbin matsalolin da ke buƙatar tallafin jinƙai.

  15. DSS ta gurfanar da El Rufai kan zargin tatsar bayanai daga wayar Nuhu Ribadu

    ElRufai

    Asalin hoton, KDGOV

    Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya (DSS) ta gurfanar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai, a gaban mai shari'a Joyce Abdulmalik a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

    DSS ta gurfanar da shi ne saboda zargin sa da hannu a tatsar bayanai daga wayar mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

    Hukumar ta DSS tana zargin El Rufain da yin kutse da gangan, wanda kuma ya saɓa wa doka kan wayar Ribadun, wanda ya saɓa wa sashe na 7 (b) da (c) na kundin kare bayanan ƙasa masu muhimmanci na 2024, wanda sashe 5(1) na dokar hana aikata laifuka ta intanet na 2024 da aka yi wa gyaran fuska ya tanaji hukunci kansa.

    Wanda ake zargin ya musanta laifukan da ake zargin sa da su, wanda ya sa lauyan masu shigar da ƙara, Oluwole Aladedoye (SAN) ya buƙaci kwanaki uku domin sauraron shari'ar.

    Bayan lauyoyin ɓangarorin biyun sun gabatar da jawabai, mai shari'a Joyce Abdulmalik ta dage sauraron shari'ar zuwa ranakun 18 da 19 da 20 na watan Mayu.

  16. An kashe mutum fiye da 500 a Tanzania bayan zaɓen shugaban ƙasa a bara - Bincike

    jami'an tsaro a gaban hoton Samia Suluhu Hassan

    Asalin hoton, Reuters

    Wani kwamitin bincike da gwamnati ta kafa ya gano cewa an kashe fiye da mutum ɗari biyar a lokacin wata mummunar zanga zanga da ta biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na Tanzania a watan Oktoban bara.

    Sai dai tawagar masu binciken ta ce ba a iya tabbatar da rahotannin da aka yi ta yaɗawa cewa an binne gomman ƴan adawa a wasu manyan ƙaburbura ba.

    Ƴan jamiyyar adawa, waɗanda suka kauracewa zaɓen, sun ce an kashe dubban mutane a yayin da jam'ian tsaro ke ƙoƙarin shawo kan tashin hankalin.

    Majalisar ɗinkin duniya ta yi kiran a gudanar da cikkaken bincike, mai zaman kansa kan abin da ta kira tsantsar take haƙƙin biladama.

    Kwamitin binciken na gabatar da rahotonsa a Dar-es-Salaam.

  17. 'Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasɗinawa uku'

    Gaza

    Asalin hoton, Khames Alrefi/Anadolu via Getty Images

    Hukumomin lafiya a Gaza da hukumar tsaron farin kaya a zirin sun ce Falasɗinawa biyar, ciki har da yara uku sun mutu sakamakon hare-haren Isra'ila ta sama.

    Hukumomin Falasɗinu sun ce an kashe mutum biyar ɗin ne a kusa da masallaci a Beit Lahiya da ke arewacin Gaza a ranar Laraba.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari ne kan abin da ta ƙira ’ɗan ta'adda’ da ke kusanto sojojin ta, kuma ya kasance barazana gare su.

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce fiye da Falasɗinawa ɗari bakwai aka kashe, yayin da aka jikkata fiye da dubu biyu a hare haren Isra'ila tun bayan tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila a watan Oktoba.

  18. An mayar da gawar tsohon shugaban Zambia Edgar Lungu ƙasarsa

    Edgar Lungu

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Zambia ta ce an dawo mata da gawar tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu, bayan watanni goma ana taƙaddama kan dawo da gawar daga Afirka ta Kudu.

    Gwamnatin Zambia na so a gudanar da janaizar girmamawa ga Mista Lungu a babban birnin ƙasar Lusaka, wani abu da iyalan sa suka nuna ƙin amincewa.

    Rahotanni sun bayyana cewa an ɗauki gawarsa ne daga wani wurin ajiyar gawa a daren Laraba ba tare da sanin iyalansa ba.

    Babban lauyan gwamnati na Zambia ya ce babbar Kotun Pretoria ce ta miƙa gawar mista Lungu ga gwamnati, bayan da iyalan sa suka yi watsi da batun ɗaukaka ƙarar da suka shigar na buƙatar a soke hukuncin cewa a binne tsohon shugaban ƙasar a Lusaka.

  19. Harin Isra'ila "da gan gan" a kudancin Lebanon ya hallaka wata ƴar jaridar ƙasar

    yar jarida a Lebanon a bakin aiki

    Asalin hoton, AP

    Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaƙi bayan an sake kashe wata 'yar jarida 'yar Lebanon a kudancin kasar.

    Wani harin Isra'ila ta sama ne ya samu Amal Khalil a lokacin da ake cewa tana kokarin tsira a wani gida.

    Jami'an Lebanon sun ce, da niyya Isra'ila ta kai harin kan 'yar jaridar.

    Firaministan ya ce sojin Isra'ila sun hana ma'aikatan agaji kaiwa ga wajen da suka kai harin.

    Ya ce kasarsa za ta kai batun gaban taruka na duniya.

    Sojin Isra'ila sun musunta kai hari kan 'yan jarida ko hana ma'aikatan agaji kai dauki wajen, kuma sun ce suna gudanar da bincike.

  20. Sojojin Najeriya sun kashe gomman ƴan bindiga da lalata jiragen ruwansu a Tafkin Chadi

    sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabashin Najeriya, Operation haɗin kai, ta yi nasarar hallaka aƙalla ƴan bindiga talatin, tare da lalata jiragen ruwansu da dama, a yayin wani aiki da suka yi a kan Tafkin Chadi, kusa da yankin tsibirin Kaniram a jihar Borno.

    A cikin sanarwar da kakakin Operation Hadin Kai, Lt. Col Sani Uba ya fitar, sojojin sun kai harin ne cikin daren Talata zuwa safiyar Laraba.

    A cewar sa, ''Jiragen saman sojin rundunar sunyi sintiri tare da tabbatar da kasancewar jiragen ruwan ƴan ta'adda fiye da talatin da suke amfani da su wajen safarar kayayyaki a yankin.''

    Ya kuma ce bayan tabbatar da sun tantance su wane ne, kuma bisa dokokin aikin soji, jami'an rundunar sun kai hare hare ta sama wanda ya lalata jiragen, ya kuma kawo cikas ga ƙoƙarin sufurin kayayyaki.

    Uba ya kuma ce hare haren da suka biyo baya, sun kai su ne kan yan bindigar da ke ƙoƙarin tserewa, wanda ya kai ga kashe kusan mayaƙa 30.

Trending Now