Iran ta ce ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Isra'ila
Dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai sabbin hare-hare kan Isra'ila a yau.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ambato rundunar IRGC na cewa hare-haren kan Amurka da Isra'ila martani ne ga wasu ƴanjaridar Lebanon da aka kashe a hare-haren Isra'ila ta sama.
Sojojin Isra'ila sun ce na'urorin tsaron sararin samaniyarta sun shafe safiyar yau suna kakkaɓo makaman linzami da ake harbawa cikin ƙasar daga Iran.
An umarci mazauna yankunan da hare-haren ke nufa su ɗauki matakan kariya domin guje wa samun illa.
Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar NNPP
Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
Jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar bayan aƙalla shekara huɗu a cikin jam'iyyar.
Matakin na zuwa ne bayan da manyan jiga-jigan adawar Najeriya ke ƙoƙarin ƙulla wani ƙawancen siyasa domin ''kawar da jam'iyyar APC a 2027''.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga NNPP ne la'akari da halin da siyasar Najeriya ke ciki, wanda ke bukatar haɗin kai.
''Matakin ya zama tilas domin haɗa kai da wasu jam'iyyun don kawo wa ƙasarmu sauyi nagari'', kamar yadda Kwankwason ya bayyana.
Sanata Kwankwaso ya kuma gode wa magoya bayansa da jagororin jam'iyyar daga matakin mazaɓa zuwa ƙasa bisa damar da ya ce sun ba shi a tsawon zamansa na NNPP.
Kwankwaso - wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyyar NNPP an yi ta hasashen komawarsa APC a watannin baya.
A 2022 ne Kwankwaso ya koma jam'iyyar NNPP sannan tsaya takarar shugaban ƙasa, ya kuma yi nasarar kafa gwamnati a Kano, bayan da jam'iyyarsa ta ci zaɓen gwamna.
Kawo yanzu dai Kwankwaso bai bayyana jam'iyyar da zai shiga ba, amma alamu na nuna cewa ADC zai koma.
'Saudiyya ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa 10'
Ma'aikatar tsaron Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa 10 da suka shiga ƙasar da nufin kai hari.
Cikin wani saƙo da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ta ce ta kakkaɓo jiragen ne ƴan sa'ao'i da suka gabata.
Sauran ƙasashen yankin yankin Tekun Fasha - ciki har da UAE da Kuwait - sun bayar da rahoton hare-hare cikin daren da ya gabata.
Yankin Gulf ya yi fama da jerin hare-haren cikin wkana guda da ya gabata, ciki har da wana aka kai kan manyan wuraren more rayuwa, kamar yadda wakilinmu a Dubai ya ruwaito.
Ba mu fitar da kuɗin fom ɗin takara ba - APC
Asalin hoton, Nentawa/FB
Bayanan hoto, Shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Farfesa Nentawa
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta musanta wasu rahotonni da ke iƙirarin cewa ta fitar da kuɗin fom na tsayawa takarar kowace kujera ba gabanin zaɓen 2027.
Tun a ranar Juma'a ne ake ta yaɗa wata sanarwa, musamman a shafukan sada zumunta da cewa APC ta fitar da kuɗin fom ga masu sha'awar tsayawa takara a ƙarƙashin jam'iyyar.
Takardar ta nuna cewa kuɗin takarar kujerar shugaban ƙasa ta kai naira miliyan 200, yayin da masu sha'awar tsayawa takarar majalisar dokokin jihohi za su biya naira miliyan 20.
To sai dai cikin wata sanarwar da APC ta fitar ta ce waccar takarda da ake yaɗawa ba daga jam'iyyar ta fito ba.
Sanarwar - wadda sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Felix Morka, ya sanya wa hannu - ta ce takardar ba ta da tushe balle makama.
“APC na sanar da jama'a cewa wannan takarda ba gaskiya ba ce, kuma ba daga gare mu take ba,'' a cewar Morka.
Ya jaddada cewa APC ba ta tattauna ko amincewa da batun farashin fom ɗin takarar 2027 ba kawo yanzu.
A ranar Juma'a ne jam'iyyar ta gudanar da babban taronta na ƙasa, tare da zaɓar sabbin shugabannin da za su jagoranci jam'iyyar nan da shekara huɗu masu zuwa.
Dubban sojojin Amurka sun isa Gabas ta Tsakiya
Asalin hoton, Reuters
Kamar yadda muka bayar da labari a baya cewa ma'aikatar tsaron AMurka ta Pentagon na shirin tura dakarun Amurka zuwa cikin Iran ta ƙasa, kodayake ta ce babu tabbas ko Shugaba Trump zai amince da hakan.
Sai ga shi a ranar Asabar, rundunar sojin Amurka da te Gabas ta Tsakiya (US Central Command) na cewa jirgin yaƙin ruwan Amurka mai suna USS Tripoli ya isa yankin.
Cikin wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta ce jirgin na ɗauke da dakarun ƙundunbala da na ruwa kusan 3,500, haɗe da jiragen sama na yaƙi.
Isra'ila ta tabbatar da mutuwar sojanta ɗaya da raunata uku a Lebanon
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Isra'ila, (IDF) ta tabbatar da mutuwar sojan ƙasar ɗaya a kudancin Lebanon, inda Isra'ilar ta ƙaddamar da mamaya ta ƙasa tsawon mako biyu da suka gabata.
Cikin wani saƙon da rundunar IDF ta wallafa a shafinta na X ta ce an kuma raunata wasu dakarunta uku.
IDF ta ce sojan da aka kashe mai suna Sajan Moshe Yitzchak HaKohen Katz ɗan asalin New Haven ne aga jihar Connecticut ta Amurka.
Fararen hula fiye da 1,100, ciki har da ƙanana yara 120 da ma'aikatan lafiya 42 aka kashe a Lebanon sakamkon rikicin na baya-bayan nan, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Lebanon ta bayyana.
Muna jiran sojojin Amurka su shigo ƙasarmu ta ƙasa - Iran
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf
Kafofin yaɗa labaran Iran ciki har da kamfanin dillancin labarai na IRNA sun ruwaito kakakin majalisar dokokin ƙasar, Mohammad Bagher Ghalibaf na jawabi gamne da cikar yaƙin ƙasar da AMurka kwana 30.
Cikin jawabin nasa, Mista Ghalibaf ya ce ''cikin ƙudurori 15 na kawo ƙarshen yaƙin da Amurka ta gabatar, ta zuba zallar muradunta ne da ta kasa cimmawa a lokacin yaƙin''.
Ya ce ''maƙiya na nuna alamun sulhu bainar jama'a, yayin da suke shirin hari ta ƙarƙashin ƙasa''.
Don haka ne Mista Ghalibaf ya ce dakarun Iran na ''dakon sojojin Amurka su shiga ƙasar ta ƙasa, daga nan ne za su gane shayi ruwa ne''.
Dangane da batun cewa Iran ta miƙa wuya, kakakin majalisar dokokin ƙasar ya ce saƙon Iran a bayyane yake cewa ba za ta amince da duk wani ''tozarci'' ba.
'Sojojin Amurka na shirin shiga Iran ta ƙasa'
Asalin hoton, EPA
Jaridar Washington Post ta bayar da rahoton cewa ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon na shirin tura sojojin ƙasar domin shiga Iran ta ƙasa don yin yaƙi na makonni.
Sai dai jaridar ta ambato wasu jami'ai na cewa babu tabbaci ko Shugaba Trump zai sahale wa buƙatar tura sojojin ta ƙasa.
Rahoton ya ce shirin ya nuna shigar sojojin ta ƙasa ba zai zama cikakkiyar mamaya ba, sai dai yawaita samame haɗe da yaƙi ta ƙasa.
Amurkawa sun yi imanin cewa sojojin ƙundunbalan ƙasar fiye da 4,000 ne suka nufi yankin Gulf, yayin da ake tattauna batun ƙari.
BBC ta tuntuɓi Fadar White House da ma'aikatar Pentagon game da labarin.
Mayaƙan Houthi sun yi barazanar gurgunta sufurin jiragen ruwa a Tekun Maliya
Asalin hoton, Getty Images
Ƙawayen Iran a Yemen - mayaƙan Houthi sun yi barazanar gurgunta harkokin sufurin jiragen ruwa a mashigar Bahar Maliya ta kudu.
Rahotonni na cewa damuwar Isra'ila a kan shiga rikicin, Isra'ilar ka iya rufe muhimmiyar hanyar ruwa ta harkokin kasuwanci - mashigar Bab-Armanda da ke Bahar Maliya, abin da zai ƙara matsalar tattalin arziki ta duniya.
A ranar Asabar ƴan Houthin suka ƙaddamar da harinsu na farko na makamai masu linzami, tun bayan da aka fara yaƙin Gabas ta Tsakiya wata ɗaya da ya wuce, kodayake Isra'ila ta ce ta kakkaɓo makaman.
A lokacin irin wannan barazana da ƴan Houthin suka yi a kan jiragen ruwa shekara biyu da suka wuce, yawancin jiragen ruwa da ke zuwa Turai da Amurka sun sauya hanya, ala tilas inda suke bi ta Afirka.
Iran ta ci gaba da luguden hare-hare kan ƙasashen yankin Gulf
Asalin hoton, Getty Images
Iran ta ci gaba da kai hare-hare da makamai masu linzami da jirage marassa matuƙa a kan ƙasashen yankin tekun Fasha.
An bayar da rahotannin irin waɗannan hare-hare da ta kai cikin dare a Qatar da Kuwait da Hadaddiyar Dalar Larabawa.
A Bahrain, ɗaya daga cikin kamfanonin da suka fi samar da goran ruwa ko sanholo a duniya - Alba, ya ce yana duba irin ɓarnar da irin harin ya yi wa wasu daga cikin masana'antunsa.
Tun da farko Iran ta ce ta kai hari kan masana'antun samar da goran-ruwan a Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ta ce wuraren suna da alaƙa da sojin Amurka.
Haka kuma Iran ɗin ta yi barazanar kai hari kan jami'o'in da ke da alaƙa da Isra'ila da kuma Amurka a Gabas ta Tsakiya, domin abin da ta kira ramuwar-gayya ga harin da take zargi an kai wa jami'arta a Tehran.
Dakarun juyin-juya-halin ƙasar sun gargaɗi dalibai da malamai da kuma mazauna kusa da jami'o'in, su ƙaurace wa harabar duk wata jami'a ta Amurka da ke yankin, da tazarar kilomita ɗaya, idan suna son kansu da arziki.
Ta ce za ta kai harin har sai Amurka ta soki harin bama-baman da aka kai wa jami'o'in Iran.
Sallama
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.