An ga baƙin hayaƙi na tashi a saman wasu kamfanonin Isra'ila
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce an ga baƙin hayaƙi na tashi a sama wasu kamfanonin Isra'ila da ke yankin Negev a Kudancin ƙasar.
Kafar yaɗa labaran Isra'ila, Channel 12 da jaridar Times ta ƙasar duka sun yaɗa hotunan baƙin hayaƙin da ke tashi daga yankin da suka ce rukunin masana'atun Ne'ot Hovav ne da ke birnin Beersheba a kudancin ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran sun ce ba a samu labarin jikkata ba.
Sojojin Isra'ila sun ce gobarar ka iya tashi sanadiyyar ɓaraguzan makamai masu linzami da suka kakkaɓo, kamar yadda kamfanin dilancin labarai na AFP ya ambato su.
Lamarin na zuwa ne bayan da rundunar sojin Isra'ila ta ce tana aiki domin kakkaɓo makamai masu linzami da aka harba cikin ƙasar daga Iran.