Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne zai maye gurbin mataimakin gwamman Kano?
Tun bayan da mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam ya sanar da ajiye aiki, yanzu kallo ya koma kan wanda zai maye gurbinsa.
A ranar Juma'a ne Aminu Abdussalam ya sanar da ajiye aikin nasa cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce mataimakin gwamnan ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da guje wa haifar da tsaiko a harkokin mulkin jihar.
Ajiye aikin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar ta fara yunƙurin tsige shi saboda wasu zarge-zarge da ta ce suna da alaƙa da almundahanar kuɗaɗe, zargin da mataimakin gwamnan ya sha musantawa.
An fara samun tsamin dangantaka tsakanin ɓangaren gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da mataimakin nasa ne tun bayan da gwamnan ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC tare da wasu kwamishinoninsa.
Shi dai mataimakin nasa bai bi shi zuwa APC ba, yayin da ya ci gaba da zama a NNPP, wani abu da masana siyasa ke ganin da kamar wuya tafiyar ta ɗore.
Tuni masu bibiyar harkokin siyasar jihar suka fara tsokaci kan mutanen da za su iya gaje kujerar mataimakin gwamnan.
Kawo yanzu dai an fara ambata sunaye wasu mutane da ake hasashen za su iya zama mataimakin gwamnan jihar, musamman saboda irin muhimmancinsu a tsarin siyasar jihar.
Manyan sunayen da aka fi jin amonsu a daidai wannan lokaci sun haɗa da:
Jibril Ismail Falgore
Hon. Hibril Ismail Falgore shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Kano a yanzu.
Mutum ne da ake yi wa kallon mai biyayya ga gwamna jihar tun bayan zamansa kakakin majalisar dokokin jihar a 2023.
Ya taka muhimmiyar rawa musamman wajen sauya dokokin da suka shafi masarautar Kano a watan Mayun 2024.
A ranar da Abba Kabir ya sanar da sauka shekarsa zuwa APC, Hon Falgore ya jagoranci wasu ƴanmajalisar dokokin jihar fiye da 20 domin bin gwamnan zuwa APC.
Hakan ne ya sa ake ganinsa a matsayin mutumin da Abba Kabir zai zaɓa a matsayin mataimakinsa.
Murtala Sule Garo
Hon. Murtala Sule Garo shi ne tsohon ɗan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.
Ya kasance jigo a jam'iyyar APC ta jihar Kano, kuma ɗaya daga cikin manyan yaran Abdullahi Umar Ganduje a siyasa.
Ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan ƙananan hukumomi zamanin mulkin Ganduje, kafin nan ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Kabo, kuma shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi reshen jihar Kano.
Ana ganin idan Abba ya zaɓe shi a matsayin mataimakinsa hakan zai nuna cewa babu wani bambanci a APCn Kano tsakanin sabbin zuwa da kuma tsoffi.
Hajiya Sa'adatu Yusha'u
Hajiya Sa'adatu Yusha'u ita ce shugabar ƙaramar hukumar Tudun Wada, kuma shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi reshen jihar Kano.
Ana yi mata kallon kallabi tsakanin rawuna, cikin ƴansiyasar Kano, da kuma kusancinta da gwamnan.
Hajiya Sa'adu ta koma APC ne tare da gwamna Abba Kabir Yusuf, kuma ana ganin ɗaukarta a matsayin mataimakiyar gwamna zai ƙara wa mata wakilci a cikin gwamnati.
Mata sun jima suna ƙorafe-ƙorafen rashin cikakken wakilci a cikin gamnati musamman a jihohin arewacin Najeriya.
Kabiru Al'assan Rurum
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kanon na daga cikin mutanen da ake ambaton sunayensu don maye gurbin Aminu Abdussalam.
Kabiru Al'assan Rurum - wanda a yanzu ke wakiltar ƙananan hukumomin Bunkure da Kibiya da kuma Rano a majalisar wakilan ƙasar - ya koma APC ne gabanin komawar Abba Kabir.
Rurum na da ƙwarewa a harkokin siyasa la'akari da muƙaman da ya riƙe, ciki har da mai tsawatarwa na marasa rinjaye a majalisar wakilai.
Baya ga waɗannan akwai kuma wasu mutum biyu da ake ambato da suka haɗa da Salihu Sagir Takai da kuma Yunusu Adamu Dangwani, ko da ya ke amon nasu bai yi ƙarfi sosai ba.
Me ya kamata gwamna ya yi?
Dr Kabiru Sufi, malami a Kwaleji Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa ya ce waɗannan ƴan siyasa da ake hasashe, matsayinsu da cancanta ko ƙwarewa ta kai su riƙe wannan gurbi.
Masanin siyasar ya ce akwai abubuwan da ake ganin za su yi wa gwamna jagora wajen zaɓar mataimakin nasa
''Na farko la'akari da inda gwamnan ya fito watau Kano ta tsakiya, dole a ɗauka daga Kano ta Kudu ko Kano ta Arewa''.
Akwai kuma gida-gida na siyasa da ake da su a Kano, kamar na ƴan jam'iyyar NNPP da aka dawo da su da kuma ɓangaren Ganduje da Sanata Barau, waɗanda aka samu.
''Kowanne akwai ƙarin da ake ganin zai zo da shi yayin da ake ganin ɗaukar wasu za ta iya kawo nakasu a danganta da wanda aka ɗauka daga cikinsu'', in ji masanin siyasar.
Dr Sufi ya ƙara da cewa abin dubawa shi ne, akwai dalilai na siyasa da na ƙara ƙima da daraja da kuma kwanciyar hankali za su iya taka rawa a ɗaukar mataimakin gwamnan.
''A wani lokacin irin waɗannan dalilai sukan ɗara batun cancanta ko kusanci da ƙwarewa''
Ya ce yawanci akan duba masalahar mulki da ci gaba da kwanciyar hankali da daidaito ga ɓangarori da dama.
'Ƙalubalen rashin ɗauka daga tsohuwar APC'
Wani abu da ke ɗaukar hankalin masu nazarin siyasar shi ne ɓangaren da gwamnan zai ɗauka tsakanin ƴan tsohuwar APC da kuma ƴan komen.
Dr Kabiru Sufi ya ce idan ana so a tafi da ƴan jam'iyyar APC da aka tarar zai yi kyau a ba su dama kamar yadda ya kamata, kuma wannan ne zai ba su damar bayar da haɗin kai cikakke a tafiyar.
''Idan kuma bai ɗauka daga cikin waɗanda ya taho da su daga jam'iyyar NNPP ba, babu shakka su ma za su ce an ajiye su, to amma za su fi sauƙin yin haƙuri saɓanin ƴan APC da aka tarar'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Abin jira a gani dai yanzu shi ne mutumin da gwamnan zai sanar nan gaba, bayan kammala babban taron APC da ya halarta a Abuja.