Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta bari matsalar tsaro ta durƙusar da ƙoƙarin da take yi na magance matsalar tsaro a sassan ƙasar daban-daban tare da tabbatar da inganta tsaro da walwalar ƴan ƙasar
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a lokacin da mataimakinsa da ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a gidansa da ke Legas.
Tinubu ya ce "tattaunawar da na yi a lokacin ziyarar aiki da na kai Birtaniya ta mayar da hankali ne kan tsaro da jin daɗin al’umma, tare da nemo hanyoyin samun kayan aiki da tallafi daga ƙasashen waje."
Tinubu ya ƙara da cewa ya tattauna da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron kan haɗin gwiwa wajen samar da kayan tsaro da tallafi.
Ya ce "gwamnati na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da sauran ƙasashe domin inganta tsaro, yana mai bayyana cewa rashin tsaro babbar barazana ce ga ci gaba da walwalar ƙasa.
Haka kuma shugaban ya yi gargaɗin tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya kan tattalin arziƙin ƙasa, musamman hauhawar farashin man fetur da rage ƙarfin saye.
Tinubu ya kuma buƙaci gwamnonin su ƙirƙiri matakan rage raɗaɗin wannan matsala ta hauhawar farashin man fetur ga al’umma, musamman a fannoni kamar makamashi da sufuri, tare da ƙara tallafawa marasa ƙarfi.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yaba da ƙoƙarin shugaban ƙasa, yana mai cewa gwamnonin za su ci gaba da aiki tare domin kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa kan batun ‘yan sandan jihohi, tare da shirin kai batun gaban majalisar dokoki domin samar da doka mai ɗorewa.