Yaƙin Iran – Ƙasashen da ke ƙirga riba da waɗanda ke tafka asara

    • Marubuci, Dharshini David
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Deputy economics editor
  • Lokacin karatu: Minti 5

Tun daga hauhawar farashin mai da gidaje a Yorkshire ya zuwa rufe makarantu saboda tsadar abin hawa a Pakistan, babu wanda b yai ji a jikinsa game da yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

A bayyane take cewa ramuwar gayya da Iran ta ƙaddamar, ya yi matuƙar tasiri wajen wargaza tsarin tattalin arziƙi da yin lahani, sai dai komai zai iya wucewa.

Amma tabbas ba abu ne da aka saba gani ba.

Sai dai duka wahalar da yaƙin ya jefa duniya a ciki, akwai waɗanda su kuma riba suke ƙirgawa sakamakon yaƙin.

Masu cin riba: Norway, Canada da Rasha

Duk da ƙoƙarin da duniya ke yi na mallakar makamashin da ba ya gurɓata muhalli, har yanzu duniya ta fi dogaro kan man fetur da iskar gas.

Don haka ga masu rumbunan waɗannan makamashi, tamkar ɗimbin dukiya ce gare su, musamman yadda ake kallon man fetur a matsayin ''baƙin zinare''.

A duk lokacin da farashinsa ya tashi, masu arzikinsa kan ci gajiyar hakan, yayin da masu saye ke ji a aljihunsu.

Yankin Gabas ta Tsakiya ya kasance matattarar da ke fitar da mai, musamman ta mashigar Hormuz.

To amma rufe mashigar - wanda ya dakatar da jigilar man - da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin mai a yankin ya shafi manyan ƙasashen da ke fitar da man matuƙa gaya, irin su Qatar da Saudiyya, yayin da Iran ke kai wa ƙawayen Amurkan a yankin hare-hare.

Yayin da masu saye ke neman man daga wasu yankuna, ƙasashen Norway da Canada su ne ke cin gajiyar hakan.

Bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a 2022, lokacin da ƙasashe da dama suka daina dogara da man Rasha, Norway ta samu damar ƙara yawan man da take haƙowa don cin gajiyar hakan.

Ana haka kuma sai ministan makamashin Kanada, Tim Hodgson ya yi gaggawar mayar da ƙasarsa ''cikakkiyar mai samar da makamashin da za a iya dogaro da ita'', to amma akwai ayar tambayar kan yadda za ta inganta haƙar man.

Amma abin mamaki, Rasha ce babbar wadda ke cin gajiyar yaƙin. Yayain da Amurka ta sassauta takunkuman da ta sanya wa man Rasha domin rage tsadar man a duniya, man da Rasha ta sayar wa Indiya ya ƙaru da kashi 50 cikin 100.

Wasu na ƙiyasin cewa Moscow ka iya samun ƙarin dala biliyan biyar zuwa ƙarshen watan Maris, kuma hakan zai sa ta samu sayar da mai mafi yawa a shekara da samun kuɗin mai masu yawa tun 2022.

Amurka ta yi kasadar bai wa Moscow dama fiye da ƙasashen yankin Gulf.

Baya ga Rasha da Norwa akwai kuma wasu masu cin gajiyar wannan yaƙi.

Yayin da wasu suka ƙara yawan amfani da makamashin coal, wannan wata babbar dama ce ga ƙasashen da ke samar da makamashin irin su Indonesia.

Masu tafka asara: Amurka, Birtaniya da Turai

Ya lamarin yake ga Amukan kanta? Shugaba Donald Trump ya ce idan farashin mai ya tashi, Amurka ''za ta samu kuae masu yawa''.

Kuma d alama kamfanonin mai na Amurka na kan hanyar samun ƙarin biliyoyin daloli na ribar man da suka sayar a wannan shekara, idan farashin mai ya ci gaba da tsayawa a matakin da yake a yanzu.

To amma hakan ba zai sa Amurka ta zama wadda ta fi cin ribar yaƙin ba.

Dalili na farko shi ne wasu kamfanonin sun samu tsaikon aiki a Gabas ta Tsakiya.

Alal misali kamfanin ExxonMobil da ke aiki a Qatar ya dakatar da aiki tun a farkon watan Maris, a yanzu kuma harin Iran ya faɗa masa, lamarin da ya haifar masa da ''mummunar ɓarna''.

Na biyu, bayan shafe shekaru ana rage yawan man da suke haƙowa saboda raguwar farashinsa, yawancin masu samar da man ba za su iya ƙara yawan man da suke haƙowa cikin sauri ba.

Kuma wani abu mafi muhimmanci shi ne Amurka ce ƙasar da ta fi kowa yawan amfani da mai da iskar gas a duniya.

Kama daga sanyayawa ɗaukuna a lokacin tsananin zafi da ɗumama su a lokacin matsanancin sanyi, zuwa saka mai lokacin tuƙi, suna samun ƙarancin farashin mai a cikin gida.

Masana tattalin arziƙia Jami'ar Oxford sun yi gargaɗin cewa idan farashin mai ya kai dala 140 - kuma ya tsaya a haka - tattalin arziƙin duniya na cikin barazanar durƙushewa

Tabbas ba Amurka ce kaɗai ba a wannan asara ba. Kwastomomin Truai da na Birtaniya da suka dogara da man da ake shigar da ke daga ƙetare, suma za su ɗanɗana kuɗarsu.

Hakan zai faru ne ta hanyar tashin farashin kayayyaki. Tuni aka samu tashin farashi a kasuwanni da kusan kashi 0.5, kuma idan hakan ya ci gaba, farashin kayayyaki zai ƙaru, wanda kuma zai shafi muhimman kayayyaki rin su takin zamani da kuɗin fito.

Amma labari mai daɗi shi ne, domin samun wadatuwar makamashi cikin shekarun da suka gabata, ƙasashen Yamma sun jima suna jure wa tsadar mai.

Amma, alal misali, mai da iskar gas ne fiye da rabin makamshin da ake amfani da shi a Birtaniya, kama daga direbobi, da na'urorin ɗumama da sanyaya gidaje da kuma manyan sassan tattalin arziƙi kamar masana'antu za su shiga matsala.

Wannan kuma shi ne abin da mafi ƙasashen Turai ke fuskanta.

Mafi yawan tasirin wannan kuwa ba ya dogara ba ne kawai a kan makomar farashin a nan gaba ba, amma martanin gwamnati, wanda shi ne batu mafi ɗaukar hankali a ƙasashen.

Ba abin mamaki ba ne cewa hukumomi da yawa na shakkar yin tunani game da babban mafita, saboda kuɗaɗen su ma na fuskantar matsalar karyewar daraja.

Matakan da kasuwannin lamuni za su ɗauka game da haɗarin hauhawar farashin kayayyaki na barazanar ƙarin kuɗin ruwa na biliyoyin kuɗi ga ƙasashen da ke fama da tarin basuka.

A zahiri, kodayake, babbar barazanar za ta fi shafar waɗanda ke sayen man fetur da iskar gas da ke bi ta mashigar Hormuz.

Yankin Asiya na samun kashi 59 cikin 100 na manta daga yankin Gabas ta Tsakiya, Koriya ta Kudu ce kan gaba, wadda ke sayan kashi 70 cikin 100.

yayin da hannayen jari suka faɗi sakamakon damuwar da ake da ita, ƴansiyasa na gargaɗi game da hatsarin rushewar kamfanonin ƙera na'urorin adana bayanai na laturoni.

Koriya ta Kudu ce ke ƙera kusan rabin na'urorin dana bayanai na duniya.

A wani wurin kuma, taƙaita sayar da man sannan an rufe makarantu na kusan mako huɗe a wasu ƙasashe irin su Sri Lanka da Bangladesh da Philippines.

Amma manyan masu fafutika a nahiyar sun fara wani shiri ta fuskar diflomasiyya.

China alal misali an bayar da rahoron cewa ta kwashe watanni tana ƙara yawan sayen mai daga Iran.

Haka ita ma Indiya, wadda ta ci gajiyar ɗage takunkuman da aka yi wa man Rasha.

Haƙiƙa abin da zai faru a nan gaba ko shakka babu, zai dogara ne akan abubuwan da za su faru a wannan rikici.

Amma ba zai yiwu ba, yayin da ta tsara dabarun fara kai hare-hare kan Iran, Amurka ta hango wasu daga cikin waɗannan illar tattalin arziki.

Kuma idan wannan yaƙi ya jima, mafi girman hadarin ba kawai illa ce ga ɗaiɗaikun ƙasashe ba, zai zama mummunan bala'i ga duniya.