Ana zaman ɗarɗar a birnin Jos na jihar Filato bayan wasu rahotanni da ke cewa an samu hargitis bayan sassauta dokar hana zirga-zirga ta kwana biyu da aka ƙaƙaba sanadiyyar wani mummunan hari da wasu ƴan bindiga suka kai.
A ranar Lahadi ne wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari a Unguwar Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, inda hukumomi suka ce hakan ya yi sanadiyyar rayukan aƙalla mutum 20.
Wasu faya-fayen bidiyo da aka riƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda tururuwar mutane ke guje-guje, inda wasu suka bayyana hakan a matsayin wani sabon tashin hankali a safiyar yau Laraba.
Sai dai a tattaunawarta da BBC, kwamishinar yaɗa labaran jihar Filato, Joyce Ramnap ta ce an shawo kan ƴar hatsaniyar da ta so ta tashi a safiyar ta Laraba bayan ɗage dokar hana zirga-zirga.
Ta ce: "Abin da ya faru shi ne wasu ɓata-gari ne da suka ga an ɗage doka suka so su shiga kasuwa su yi fashi, to masu shaguna a kasuwar sai suka fara gudu domin tsare dukiyarsu a cikin kasuwa, to amma da aka ga suna ta gudu sai aka fara yaɗa jita-jita, hakan ne ya kawo wani ɗan tashin hankali da safiyar yau".
Sai dai ta ce jami'an tsaro sun hanzarta wajen daƙile duk wani abu da zai iya haifar da ƙazancewar lamarin.
Ta ƙara da cewa a yanzu hankula sun kwanta a garin na Jos, babban birnin jihar Filato.
Amma kwamishinar ta bayyana cewa jami'an tsaro na nazari, domin ganin ko akwai buƙatar a sake mayar da dokar hana zirga-zirga domin daƙile duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali.
Filato na cikin jihohin arewa ta tsakiyar Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro mai nasaba da addini da ƙabilanci a tsawon shekaru da dama.