Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 24 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran a yau.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

  2. 'Bahrain ta fuskanci mafi munin hare-hare a yau', Frank Gardner, wakilin sashen tsaro na BBC

    Bahrain

    Asalin hoton, AFP via Getty

    Ƙasar Bahrain ta fuskanci mafi munin hare-haren Iran a yau Talata.

    Rahotonnin farko sun nuna cewa makami mai linzamin Iran ya faɗa kan wani sansanin soji a yammacin ƙasar.

    Bahrain ta ce harin da aka kai sansanin soji na Hamala ya kashe wani mai kwantiragin soji ɗan asalin Moroko, tare da raunata gomman mutane, ciki har da huɗu da ke cikin mawuyacin hali.

    Bayanai sun ce duka waɗanda suka jikkata ƴan ƙasar ne ciki har da sojoji.

    A ƙasar Bahrain ne Amurka ke da sansanonin sojin ruwa na Fifth Fleet, kodayake an janye duka dakarun ƴan kwanaki kafin fara yaƙin, jiragen ruwansu suka bar wurin.

    Bahrain - wadda a wasu lokuta Iran ke kallon ta a matsayin wani yanki nata da ta rasa - ta kasance mafi munin alaƙa da Iran daga cikin ƙasashen yankin Gulf shida.

    Sauran hare-haren sun faɗa kan tankunan mai da filin jirgin sama da gidaje.

    Mafi yawan al'ummar Bahrain ƴan shi'a ne kuma wasu daga cikinsu na goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

    Kuma ƙasar ta hana ƴan jaridar waje shiga cikinta domin bayar da rahotonnin abubuwan da ke faruwa.

  3. 'An kashe mutum 1,072 a Lebanon tun fara hare-haren Isra'ila kan Hezbollah'

    Ma'aikatar lafiyar Lebanon ta ce adadin mutanen da suka mutu a ƙasar tun bayan fara hare-haren Isra'ila kan Hezbollah ya kai 1,072.

    Wannan ya haɗa da mutum 33 da suka mutu a cikin sa'a 24 da suka gabata.

    Lebanon ta ce adadin wadanda suka jikkata ya kai 2,966.

  4. Kotun ƙolin Brazil ta mayar da ɗaurin Bolsonaro na talala

    Wani alƙali a Koton Ƙolin Brazil ya amince da mayar da ɗaurin da ake yi wa tsohon shugaban ƙasar, jair Bolsonaro na talala saboda dalilai na rashin lafiya.

    Bolsonaro na zaman ɗaurin shekara 27 a gidan yari sakamkon samunsa da laifin kitsa juyin mulki bayan faɗuwa zaɓen 2022.

    Tsohon shugaban na fama da matsanancin ciwon sanya na nemoniya, inda a baya-bayan nan aka sallame shi daga sashen kula da masu buƙatar gaggawa na asibiti.

  5. Gwamnatin Sokoto ta gargaɗi mata kan amfani da gas wajen girki

    Gobara

    Asalin hoton, Sokoto State Gov

    Gwamnatin jihar Sokoto, ta yi kira ga matan jihar su zama masu kula da mai da hankali yayin girki da tukwanen gas.

    Gwamnan jihar Ahmad Aliyu ne ya bayyana haka lokacin zuyarar jaje bayan wata gobara ta tashi a yankin Igwai har ta yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin hadimansa.

    Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne sanadin girki da gas, lamarin da ya kai ga rasa ran da kuma asarar dukiya.

    gobara

    Asalin hoton, Sokoto State Gov

    Ahmad Aliyu ya ce yana da kyau mata su ƙara kula sosai a lokacin da suke amfani da gas domin girki a cikin gidajensu.

    A lokuta da dama dai gas ɗin girki kan haddasa gobara a wasu sassan Najeriya, lamarin da a wasu lokutan kan zo da asarar rayuka.

  6. A shirye muke mu karɓi baƙuncin tattaunawa - Pakistan

    ..

    Asalin hoton, ....

    Firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ya yi tayin karɓar baƙuncin tattauanwar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka.

    Cikin wani sako da ya wallafa shafinsa na sada zumunta Mista Sharif ya ce idan Amurka da Iran sun amince Pakistan za ta karɓi baƙuncin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.

    Haka shi ma takwaransa na Indiya Narendra Modi ya ce ''ya yi tattaunawa mai armashi da Shugaba Trump na Amurka game da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

    ''Na yi waya da shugaban Amurka, kuma mun yi tattaunawa mai armashi kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya. Indiya na goyon bayan kawo ƙarshen yaƙin domin samun zaman lafiya'', kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

  7. Ba za mu shiga tsakani a yaƙin Amurka da Iran ba - Qatar

    Sarkin Qatar

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar harkokin wajen Qatar, ta ce ƙasar ba za ta shiga aikin sasanta tsakanin Amurka da Iran ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran ba.

    Kakakin ma'aikatar Majid Ansari ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar a Doha, babban buirnin ƙasar.

    Mista Ansari ya ce a yanzu abin da ke gaban Qatar shi ne kawo ƙarshen hare-haren da ake kai mata na kare kai.

    A shekarun da suka gabata, musamman kafin yaƙin kwana 12, Qatar ta kasance ɗaya daga cikin masu shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran.

    da aka tambaye shi Qatar za ta ci gaba da hukɗa da Jamhuriyar Musulunci bayan hare-hare kan ƙasashen Larabawa da ke yankin Tekun Gulf, sai Ansari ya ce ''E za mu ci gaba ai ba za mu iya raba kanmu da juna ba''.

    Ya kuma ce Qatar na tattaunawa daa Amurka don lalubo hanyoyin diplomasiyya.

    ''Gwamnatin Amurka ta yanke shawara fara wannan yaƙi ne saboda fargabar da take da shi kan tsaron yankin Gabas ta Tsakiya'', in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa Qatar na aiki da Amurka don yayyafa wa yaƙin ruwa da dakatar da hare-hare ''kan ƙasashenmu''.

    Ya zuwa yanzu ƙasashen Masar da Pakistan da Turkiyya na ƙoƙarin shiga tsakani don kawo ƙarshen yaƙin.

  8. Iran ta ce ta kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi a Tehran

    Jirgi

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin-juya halin Iran ta ce ta kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi samfurin Hermes a sararin samaniyar Tehran.

    A cewar kamfanin dillancin labaran Mizan, rundunar ta yi amfani da sabon na'urar tsaron samaniyarta wajen harbo jirgin maras matuƙi, wanda ke ɗauke da makamai.

    Akwai samfurin ijrage marasa matuƙa na Hermes da dama masu al'amura daban-daban, kuma galibi an tsara su ne domin tattara bayanan sirri.

    Sabon samfurin jiragen irin wannan mai suna Hemes 900 - mai tsayin mita takwas - zai iya tafiyar aƙalla 36.

    Iran ta ce tun bayan fara yaƙin ta lalata jirage marasa matuƙa 132.

  9. Sojojin Sudan sun yi ƙazamin faɗa da RSF a kan iyakar Habasha

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni na bayyana cewa ana can ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin sojojin Sudan da ƴantawayen RSF a jihar Blue Nile da ke kusa da kan iyakar Habasha.

    Rahotanni sun bayyana cewa RSF da wasu ƙungiyoyin mayaka da ke goyon bayanta na ci gaba da kutsawa, kuma tun ranar Lahadi suka fara kai hare-hare da dama a kusa da garin Kurmuk.

    Wani jami'in gwamnatin Sudan da ba a bayyana sunan sa ba ya zargi Habasha da taimakawa ƙungiyar RSF a yankin.

    Addis Ababa ta buƙaci 'yan ƙasarta da ke wannan yanki na kan iyaka da su fice.

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin ta'azzarar rikicin na jefa rayukan fararen hula cikin hadari, inda aka kashe sama da mutane dari biyar a cikin watanni uku na farkon wannan shekara.

  10. Kotu ta ɗage sauraron buƙatar bada belin El-Rufai

    ..

    Asalin hoton, Channels/Grab

    Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga Maris, 2026.

    An ɗauki wannan matakin ne bayan zaman kotun na ranar Talata, inda ɓangaren masu ƙara da masu kare kai suka gabatar da hujjoji.

    A zaman kotun, lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci kotun da ta ba da belin tsohon gwamnan, yana mai cewa hakan na cikin haƙƙinsa a kundin tsarin mulki, tare da buƙatar samun isasshen lokaci domin shirya kare shi a kotu.

    Sai dai ɓangaren masu ƙara sun yi adawa da buƙatar, suna mai cewa tuhume-tuhumen da ake yi wa El-Rufai masu nauyi ne, kuma bayar da beli na iya kawo cikas ga binciken da ake ci gaba da yi.

    Alƙalin kotun ya ɗage sauraron buƙatar neman beli zuwa ranar 31 ga watan Maris, bayan da mai gabatar da ƙara na ICPC ya ce idan aka bayar da belin tsohon gwamnan to zai iya lalata shari'ar.

    Hukumar ICPC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu bisa zargin cin hanci da kuma amfani da mukami ba daidai ba.

  11. Isra’ila za ta karɓe iko da Kudancin Lebanon

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Isra'ila, Isreal Katz ya ce sojojin ƙasar za su karɓe ikon kudancin Lebanon har zuwa kogin Litani, har sai an kawar da barazanar Hezbollah.

    Wannan dai shi ne karon farko da Isra'ila ke amincewa kai tsaye cewa tana shirin mamaye kusan kashi goma na yankin Lebanon.

    Katz ya ce 'yan ƙasar Lebanon da aka tilastawa barin gidajensu ba za su iya komawa ba har sai mutanen arewacin Isra'ila sun samu kwanciyar hankali.

    Katz ya ce dukkan gadoji biyar na kan kogin Litani da Hezbollah ke amfani da zu wajen safarar makamai da mayaƙa an ruguza su.

    Isra'ila ta buƙaci gwamnatin Lebanon da ta magance barazanar da kungiyar Hizbullah ke yi da kuma kwance damarar kungiyar da ke samun goyon bayan Iran.

    Yanzu haka dai Beirut ta umarci jakadan Iran da ya bar kasar, nan da zuwa ranar Lahadi.

  12. Iran ta naɗa Mohammad Bagher Zolqadr a matsayin wanda zai gaji Larijani

    ...

    Asalin hoton, Etemad

    Fadar shugaban kasar Iran ta nada wanda zai gaji Ali Larijani da aka kashe, a matsayin sakataren hukumar tsaron kasar.

    An naɗa Mohammad Bagher Zolqadr, wani jami'in dakarun juyin juya halin Iran.

    Da alama naɗin nasa zai ƙara ƙarfafa ayyukan dakarun IRGC wajen kare ƙasar, biyo bayan kashe shugabannin Iran da Isra'ila da Amurka suka yi ta yi cikin makonni hudu da suka gabata.

    Zolqadr ya yi aiki a matsayin kwamandan soji a cikin rundunar, kuma yayi aiki a matsayin shugaban sashen ilimi na dakarun.

    Hakazalika ya riƙe muƙamin tsohon mataimakin ministan tsaro.

  13. Kotu a Kano ta sauke shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso

    Wata babbar kotu a jihar Kano ta soke nasarar Abdullahi Ghali Shitu a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, tare da umartar a bi hukuncinta na baya da ya ayyana Ali Musa Dan Maliki a matsayin halastaccen wanda ya lashe takarar.

    Kotun ta jaddada cewa hukuncin da ta yanke tun ranar 25 ga watan Oktoban 2024 yana nan daram, inda ta ce Ali Musa Dan Maliki shi ne ya cancanci riƙe mukamin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso bisa tanadin doka.

    Bangaren Ali Musa Dan Maliki ne suka garzaya kotu bayan da gwamnan jihar, Abba kabir Yusuf ya rantsar da Abdullahi Ghali Shitu ranar 14 ga watan Nuwambar 2024 a matsayin shugaban karamar hukumar.

    Da wannan hukuncin, kotun ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da hukuncin ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da bin doka da oda a harkokin mulki a matakin ƙaramar hukuma.

  14. Rikicin Gabas ta Tsakiya ka iya tilasta yin aiki daga gida - Dangote

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Attajirin nan na Afirka, Aliko Dangote, ya gana da shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ziyarar da ya kai masa a Legas a jiya Litinin, inda ya bayyana damuwarsa kan hauhawar farashin man fetur a ƙasar da rashin tabbas a kasuwanni duniya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Attajirin ya ce rikicin yankin ka iya tilasta wa ma’aikata yin aiki daga gida kamar lokacin annobar Covid-19, saboda karancin man fetur da rikicin ke haifarwa.

    Dangote ya yi gargaɗin cewa rikicin yankin na iya ƙara tsananta wahalhalu a nahiyar Afirka idan ba a magance shi cikin gaggawa ba.

    Haka kuma, ya ce rikici mai tsawo zai shafi ƙananan kamfanoni da masana’antu da ke dogaro da wutar lantarki da janareta mai amfani da mai, wanda hakan zai ƙara wahalar tattalin arzikin nahiyar.

    Dangote ya ƙara da cewa duk da cewa Najeriya ba ta cikin rikicin kai tsaye, illa daga hauhawar farashin man fetur a duniya tabbas zai shafi ƙasar.

    “Duk da cewa Najeriya ba ta da hannu kai tsaye a yaƙin Iran da Amurka da Isra’ila, rikicin zai shafe mu, amma muna addu’a a warware wannan matsalar,” in ji Dangote.

  15. Lebanon ta kori jakadan Iran daga ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Iranian Ministry of Foreign Affairs

    Gwamnatin Lebanon ta soke takardun jakadan Iran, Mohammad Reza Rauf Sheibani, tare da umartar shi da ya bar ƙasar kafin ranar Lahadi mai zuwa.

    Sakataren Janar na ma’aikatar, Abdel Sattar Issa, ya kira Tawfiq Samadi Khoshkho, jakadan wucin gadi na Iran a Beirut, don sanar da shi wannan mataki.

    Haka kuma, Lebanon ta dawo da jakadanta, Ahmed Suwaidan, daga Tehran don tattaunawa.

    Hakan na nuna cewa dangantakar Lebanon da Iran na ƙara taɓarɓarewa.

    Hezbollah, wanda ke da alaka sosai da Iran, na fuskantar matsin lamba daga Amurka da Isra’ila kan batun ƙungiyar ta ajiye makamai.

    Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Youssef Raji, ya bayyana a bara cewa bai yarda da gayyatar tafiya Tehran ba, ya fi son a gudanar da tattaunawar a wata kasa mai zaman kanta idan duka ɓangarorin suka amince.

  16. Ba mu shiga tsakanin yaƙin Amurka da Iran ba - Qatar

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Dr. Majid Al-Ansari, ya bayyana cewa Qatar ba ta shiga kowanne yunƙurin sulhu tsakanin Amurka da Iran don kawo ƙarshen yaƙin.

    Ya ce, “Mu mun fi mayar da hankalinmu kan kawo ƙarshen hare-haren da ake kai mana da kare iyakokin ƙasar mu.”

    Da BBC ta tambaye shi ko Qatar za iya sake samun kyakkyawar dangantaka da Iran bayan waɗannan hare-haren da aka kai ƙasashen Gulf, sai ya ce: “Eh, ba za mu iya canza yanayin ƙasa ba.”

  17. Rundunar IRGC ta Iran ta yi barazanar kai wa dakarun Isra'ila hari a zirin Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran ta bayyana cewa Isra’ila ta wuce gona da iri wajen kisan kiyashin da take wa Falasdinawa inda ta ce ba za a ci gaba da jurewa wannan halin ba.

    A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, IRGC ta yi gargaɗi ga rundunar sojin Isra’ila cewa "idan har laifukan da take aikatawa kan fararen hula a Lebanon da Falasdinu suka ci gaba, to rundunar za ta kai wa wuraren da sojojin Isra’ila ke taruwa a arewacin Falasɗinu da zirin Gaza manyan hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki ba tare da wani la’akari ba.."

  18. Bahrain ta ce ta daƙile gobarar da harin Iran ta haddasa

    ....

    Asalin hoton, Bahrain MOI/X

    Ma’aikatar cikin gida ta Bahrain ta bayyana cewa an dakile gobara da ta tashi sakamakon wani hari da Iran ta kai a wani kamfani.

    Ma'aikatar bata bayyana sunan kamfanin ba.

    Wannan na zuwa ne kimanin sa’o’i shida bayan da ma’aikatar ta yi gargadi a shafin sada zumuntarta na X, inda ta ce ana jin karar siren kuma ta yi kira ga ‘yan ƙasa su nemi wuraren tsaro su ɓoye..

  19. Da waɗanne laifuka ICPC ke tuhumar Nasir El-Rufai?

    ...

    Asalin hoton, KDSG

    A ranar Talatar nan ne hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta sanar da shirinta na gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotuna guda biyu duk a Kaduna.

    Hukumar ta ce za ta gurfanar da shi tare da wani Joel Adoga a Babbar Kotun Tarayya da kuma wani Amadu Sule a wata babbar kotun ta daban duka a

    Tun dai ranar 19 ga watan Fabrairu ne tsohon gwamnan jihar ta Kaduna ke riƙe a hannun hukumar ICPC bayan da ta kama shi jim kaɗan bayan sakin sa da hukumar EFCC ta saske shi.

    A ranar 5 ga watan Maris ne wata kotun majistire ta bai wa ICPC damar tsawaita tsare El Rufai da mako biyu.

  20. Isra’ila ta tabbatar da mummunar ɓarna bayan hare-haren Iran a ƙasar

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra’ila sun tabbatar da cewa harin makamai masu linzami daga Iran ya janyo mummunar ɓarna a yankunan tsakiyar ƙasar, inda aka tura jami’an ceto da agaji zuwa wuraren da abin ya shafa.

    Hotunan da aka wallafa a shafin Telegram na hukumomin agajin gaggawa na Isra’ila sun nuna hayaƙi na tashi daga gine-gine tare da tarkace da suka bazu a wuraren.

    A baya an ruwaito cewa, bayan gargadin da sojojin Isra’ila suka bayar game da harba makamai masu linzami daga rundunar juyin juya halin Iran IRGC, an tura jami’an agaji zuwa kudancin ƙasar inda aka samu ɓarna bayan harin ya afku.

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

Trending Now