KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Talata 7/4/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 7 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Abdullahi Bello

  1. 'Mun kai wa kamfanin sarrafa sinadaran man fetur na Amurka a Saudiyya hari'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun juyin juya hali Iran sun ce sun kai hari kan manyan kamfanonin sarrafa sinadaran man fetur mallakin Amurka da ke Saudiyya, ciki har da cibiyoyi a yankin Jubail da Al-Juaimah, a matsayin martani ga harin da aka kai kan masana’antar Asaluyeh.

    Sanarwar ta ce a jerin hare-haren Iran karo na 99”, an kai hare-hare da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan sansanonin Amurka da kadarorinta a yankin Tekun Farisa da mashigar Hormuz, da kuma cibiyoyin tsara kai hare-hare a Isra’ila.

    Dakarun sun bayyana cewa harin na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya kan abin da suka kira hari kan “ kamfanin sarrafa sinadaran man fetur da ke Asaluyeh”.

    Sun ƙara da cewa a matakin farko na harin, sun nufi manyan cibiyoyin sarrafa sinadaran man fetur da suka hada da na kamfanonin Amurka irin su ExxonMobil da Dow Chemical Company da kuma Chevron Phillips Chemical, inda aka ce an kai musu hari da makamai masu linzami.

    Har ila yau, dakarun sun yi gargaɗin cewa idan sojojin Amurka suka tsallake iyakar da suka gindaya, martanin da za su mayar zai wuce yankin Gabas ta Tsakiya.

    Sanarwar ta ce za su yi aiki kan lalata cibiyoyin samar da mai da iskar gas na Amurka da kawayenta domin hana su anfani da albarkatun yankin na tsawon shekaru.

    Sun kuma gargadi kawayen Amurka a yankin da cewa a baya sun nuna hakuri saboda kyakkyawar makwabtaka, amma yanzu sun cire duk wani sharadi wajen zabar wuraren da za su kai hari.

    Dakarun sun ƙara da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai hare-hare har ma da wuraren fararen hula idan rikicin ya ƙara ƙamari.

  2. Idan Amurka ta wuce gona da iri, martaninmu zai wuce yankin Gabas ta Tsakiya - Iran

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Rundunar juyin juya halin Iran ta yi gargaɗin cewa idan Amurka ta wuce gona da iri da hare-haren da take kai wa, martanin da za ta mayar zai wuce iya kan yankin Gabas ta Tsakiya kawai.

    A cikin wata sanarwa da aka wallafa ta kafafen yaɗa labaran gwamnati, rundunar ta ce duk da rikicin da ake ciki, ta nuna juriya sosai tare da yin taka-tsantsan wajen zaɓen wuraren da take kai hare-haren ramuwar gayya kan Amurka da ƙawayenta a yankin.

    Sai dai ta ƙara da cewa daga wannan lokaci, za ta ajiye irin waɗannan la’akari, tana mai gargadin cewa idan sojojin Amurka suka wuce gona da iri, martanin Iran zai haɗa da kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa na Amurka da ƙawayenta, tare da kawo cikas ga samar da mai da iskar gas a yankin na tsawon shekaru.

  3. Isra'ila ta yi barazana wa sufurin jiragen ƙasa na Iran

    Sojojin Isra’ila sun yi barazana wa sufurin jiragen ƙasa a Iran, inda suka gargaɗi ‘yan Iran da su guji amfani da jiragen ƙasa ko yin tafiya a fadin ƙasar saboda hatsarin rayuwa.

    Wannan gajeriyar sanarwa, wadda sojojin Isra’ila suka wallafa a harshen Farsi a X, ta ce: “Kasancewarku a kan jiragen ƙasa ko kusa da layukan jiragen ƙasa na sanya rayukanku cikin haɗari.”

    A wasu sassan Iran, ciki har da Tehran ta Kudu, layukan jiragen ƙasa suna kusa da yankunan da ake zama.

    Ranar ƙarshe da Donald Trump ya sanya wa Iran don bude mashigar Hormuz za ta cika cikin ƙasa da awanni 24, kuma ya ce zai kai hari kan kayan more rayuwa, ciki har da gadaje.

  4. Kakakin majalisar dokokin Jihar Kebbi ya rasu

    Hon. Ankwai

    Asalin hoton, Audi Photography

    Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Right Hon. Muhammad Usman Ankwai.

    Ɗan majalisar mai wakiltar yankin Zuru ya rasu ne a ƙasar Masar bayan fama da jinya, kamar yadda akawun majalisar Suleiman Shamaki ya tabbatar.

    Cikin saƙon ta'aziyyae da gwamnan jihar ya fitar, ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar mutumin da ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan gwamnatin jihar.

    ''Ya kasance jagora mai ƙoƙari, ɗan kishin ƙasa na gaskiya da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimta wa al'umma, haƙiƙa ba za mu manta da ƙwarewarsa ba wajen ciyar da jiharmu gaba'', in ji shi gwamnan.

    Hon Ankwai ya rasu ya bar matarsa ɗaya da ƴaƴa biyar.

  5. Amurka ta yi asarar aƙalla jiragen yaƙi tara a yaƙin Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Amurka ta yi asarar aƙalla jiragen yaƙi tara a yaƙin da take yi da Iran zuwa yanzu, bisa binciken hotuna da sanarwar hukumomi, da bayanai daga kafofin watsa labaran Amurka.

    CBS News ta ruwaito a ranar 5 ga Afrilu cewa Iran ta lalata jirage guda biyu ƙirar F-15E da aka tura don taimakawa aikin ceto. Hotuna da aka tabbatar sun nuna ɓirɓishin jiragen na hayaƙi a tsakiyar Iran.

    A ranar 3 ga Afrilu, Iran ta kakkaɓo tare da harbe jirgin yaƙin Amruka ƙirar F-15E Strike Eagle a saman tsakiyar ƙasar. A wannan rana, New York Times ta ruwaito cewa wani jirgi ƙirar A-10 Warthog ya faɗi a tekun Gulf, matukin sa ya tsere, sannan daga baya aka ceto shi.

    Hotuna da aka tabbatar a ranar 29 ga Maris sun nuna jirgin E-3 Sentry ya lalace a sansanin jirgin saman Prince Sultan a Saudiyya, bayan rahotannin harin Iran.

    A ranar 12 ga Maris, mutane shida da ke jirgin yaƙin Amurka ƙirar KC-135 sun mutu a yammacin Iraq bayan ya faɗi, in ji babbar cibiyar ayyukan sojin Amurka (Centcom). Ana binciken dalilin faduwar, amma Centcom ta ce ba harin abokan gaba ba ne.

    A ranar 2 ga Maris, jiragen Amurka ƙirar F-15E guda uku sun rikito a sararin samaniyar ƙasar Kuwait a abin da Centcom ta bayyana a matsayin “abin da ake zargin kuskure ne daga dakarun ƙawance.” Duk ma’aikatan jiragen guda shida sun kuɓuta lafiya, sashen tantance labarai na BBC Verify ya tabbatar da gaskiyar bidiyon da ke nuna jirgi guda ɗaya na F-15 yana jujjuyawa a lokacin da yake fadi ƙasa a yammacin babban birnin Kuwait.

  6. Isra'ila ta ce Iran ta kai mata hari da makamai masu linzami

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra’ila sun ce Iran ta kai hari da makamai masu linzami a kan Isra’ila.

    Sanarwar da rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta fitar ta ce dakorunta na ƙoƙorin kakkaɓo makaman da Iran ɗin ta harba.

    A wani sabon bayani, rundunar ta ce jama’a za su iya barin wuraren da suka fake domin kariya, bayan da ta yi gargadin cewa su tsaya a wuraren da suka dace idan an ba da sanarwar gargaɗi.

  7. An sake buɗe gadar da ke haɗa Saudiyya da Bahrain

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    An sake buɗe gadar da ita kaɗai ce ke haɗa Saudiyya da Bahrain bayan an rufe ta sakamakon hare-haren Iran.

    Hukumomi sun rufe gadar King Fahd Causeway “a matsayin matakin kariya” yayin da hare-haren da aka kai wuraren makamashi kusa da gadar ke ƙara tsananta.

    Sanarwar sake buɗe gadar ta zo bayan awa biyar, inda hukumomi suka bayyana a shafukan sada zumunta cewa zirga-zirgar motoci ta ci gaba.

    Gadar tana da tsawon milimita 15.5 kuma tana haɗa ƙasashen Gulf guda biyu ta hanyar jerin gadaje.

  8. Harin da aka kai wa Iran ya lalata wurin bautar Yahudawa

    ,....

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban birnin Iran, Tehran, na fuskantar sabbin hare-haren jirage marasa matuƙa inda harin ya lalata wurin bautar Yahudawa, yayin da ake jin ƙarar fashe-fashe daga sassa daban-daban na babban birnin.

    Wasu rahotanni sun nuna fashewa a Parchin da wasu unguwanni a yamma da kudu na Tehran.

    Hakanan an samu rahotanni na fashe-fashe a Qom, yayin da gwamnan Lorestan ya sanar da harin da aka kai Filin Jirgin Sama na Khorramabad.

    A cewar Kamfanin Watsa Labarai na Iran, wurare da aka kai wa hari a Tehran sun haɗa da Tehranpars da Saadataba da filin Jirgin Sama na Mehrabad, da Babban titin Haki da shagunan kasuwanci na Rumi. make the first paragraph tally with the headline Harin da aka kai Iran ya lalata wurin bautar Yahudawa

  9. Yadda hayaƙi da wuta ke tashi a filin jirgin saman Tehran

    Sashen tantance gaskiyar labarai na BBC na nazarin hotuna da bidiyo da suka bayyana bayan hare-haren da aka kai na a filin jirgin Tehran.

    Hotunan da aka tabbatar sun nuna aƙalla gobara huɗu da hayaki mai yawa na tashi daga ɓangaren filayen saukar jiragen Mehrabad.

    BBC Verify ta tabbatar da wurin da aka ɗauki hotunan ta hanyar gano masallaci da babban gini kusa da wurin.

    Bayyanar waɗannan bidiyon ya biyo bayan bidiyo da aka tabbatar na sakamakon hare-haren da suka faru a filin jirgin a ranar Lahadi, wanda sojojin Isra’ila suka ce a ranar Litinin sun kai.

    Bayanan bidiyo, Lasta hoton domin kallon bidiyon
  10. Iran ta yi kakkausar suka ga Saudiyya da UAE kan 'bai wa Amurka damar' kai mata hari

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta yi kakkausar suka ga Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana zargin ƙasashen biyu da bai wa Amurka damar amfani da yankunansu wajen kai mata hare-hare, inda ta bayyana hakan a matsayin babban take haƙƙinta da barazana ga tsaron ƙasarta.

    A cikin wasiƙu guda biyu da ta aika zuwa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Iran ta buƙaci waɗannan ƙasashe su mutunta ka’idojin makwabtaka mai kyau tare da dakatar da amfani da yankunansu wajen kai hare-hare kan ƙasar.

    Jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya bayyana a cikin wasiƙun cewa ƙasashen biyu sun saba doka ta hanyar bai wa wasu ƙasashe damar kai hare-hare a Iran.

    Iran ta kuma yi gargaɗi cewa duk da tana girmama Saudiyya da UAE, tana da haƙƙin ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare kanta.

    Tun bayan fara rikicin da ke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, ƙasashe da dama a yankin, ciki har da Saudiyya da UAE, sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuki daga Iran.

    Iran ta bayyana cewa hare-haren nata a kan sansoninin Amurka ne da wuraren da ke da alaƙa da Amurka da Isra’ila a yankin.

  11. Ƴan sama-jannatin da suka je duniyar wata sun kamo hanyar saukowa ƙasa

    Ƴan sama-jannati huɗu da suka je zagaye a duniyar wata

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ƴan sama-jannati huɗu da suka je zagaye a duniyar wata

    Ƴan sama-jannati huɗu da suka yi balaguron da aka yi wa laƙabi da 'Artemis II' zuwa duniyar wata sun kamo hanyar dawowa gida bayan kammala shawagi a sararin samaniyar wata, ciki har da ɓangaren da ɗan'adam bai taɓa gani ba.

    Wannan ne karon farko da bil'adama ya taɓa ganin ɗayan ɓangaren na duniyar wata a tarihi.

    Sadarwa ta tsinke tsawon minti 40 tsakanin ƴan sama-jannatin huɗu da masu magana da su a nan kan doron duniya.

    Hakan ya faru ne sanadiyyar yadda wata ya shiga tsakanin kumbon ƴan sama-jannatin da duniyar bil'adama.

    A lokacin da sadarwa ta dawo, ɗaya daga cikin ƴan sama-jannatin mai suna Christina Koch ta ce "mun yi murna da sake jin muryarku daga duniya".

    A yanzu kumbon da suke ciki mai suna 'Orion' zai ɗauki kimanin kwana huɗu kafin isowa doron duniyarmu.

    Artemis II commander Reid Wiseman looks out the window of the Orion spacecraft at the Moon

    Asalin hoton, NASA

    Bayanan hoto, Kwamandan tafiyar Artemis II Reid Wiseman a bakin tagar kumbon Orion lokacin da suka tunkari duniyar wata
    Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon lokacin da ƴan sama-jannatin Artemis II suka tashi daga duniyar bila'adama zuwa duniyar wata
  12. Ina mamakin yadda muke jefa wa ƴan Iran bam suke cewa mu ƙaro - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana mamakinsa kan yadda ‘yan Iran ke mayar da martani ga harin da aka kai kan muhimman wurarensu, inda ya ce: “‘Yan Iran da muka gani suna cewa, ku ci gaba da jefa mana bam. Duk da cewa bamai-bamam na fadawa kusa da gidajensu, suna ci gaba da cewa mu ƙaro.”

    A cikin wani jawabi, Trump ya ce ya bai wa rundunar sojin Amurka umarni su yi duk abin da ya dace wajen ceto matukin jirgin saman Amurka, wanda tuni Trump in ya sanar cewa sun ceto shi.

    Trump ya ce aikin da ya haɗa da jirage 155, ciki har da masu jefa bam guda huɗu, jiragen yaki 64, jiragen ceto 13 da sauran jirage da dama.

    Trump, yana maimaita barazanar sa kan kai hari a muhimman wuraren Iran inda ya ce: “Za a iya lalata duk Iran gaba ɗaya cikin dare guda, kuma watakila ma a daren gobe.”

  13. Za a iya lalata Iran cikin dare ɗaya - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada barazanar cewa zai iya lalata Iran cikin dare ɗaya, yana mai cewa hakan na iya faruwa a daren ranar Talata, yayin da wa’adin da ya bai wa Tehran ke ƙarewa.

    A lokaci guda, Firaministan Qatar ya yi wata tattaunawa ta waya da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, inda ya yi Allah-wadai da kai hare-hare kan muhimman kayayyakin more rayuwa daga kowanne ɓangare na rikicin.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a Iran, ciki har da filayen jiragen sama da masana’antun man fetur, tun kafin wa’adin da Trump ya sanya ya cika.

    A wani bangare kuma, wani kwamandan rundunar juyin juya halin Iran, Majid Mousavi, ya ce Iran ta fara wasu jerin hare-hare waɗanda babu wanda zai iya dakatar da su sai Iran kaɗai.

  14. Yau ne wa'adin da Trump ya bai wa Iran ke ƙarewa

    Shugaban Amurka Donald Trump da Jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, Getty Images/Tasnim

    A yau ne wa'adin da shugaban Amurka, Donald Trump ya bai wa Iran kan buɗe mashigar Hormuz ke ƙarewa.

    A jiya Litinin ne dai Trump ya yi barazanar cewa za a lalata tashoshin wutar lantarki da gadoji a Iran idan har ƙasar ta ki buɗe mashigar Hormuz.

    Tun farko, Iran ta ƙi amincewa da tsagaita wuta na wucin gadi, tana mai cewa za ta amince ne kawai da kawo ƙarshen yaƙin na dindindin.

    Sai dai jakadan Iran a Pakistan, wanda ke shiga tsakanin Amurka da Iran, ya yaba wa Islamabad, yana mai cewa ƙoƙarinsa na dakatar da rikicin na kai wa wani muhimmin mataki.

  15. Iran ta kai ƙara Majalisar Ɗinkin Duniya kan kalaman Trump

    Iran ta aika wasiƙa zuwa ga Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan batun aika makamai ga masu adawa da Jamhuriyar Musulunci.

    Jakadan Iran na dindindin a Majalisar, Amir Saeed Iravani, ya bayyana a cikin wasiƙar da ya aika wa Antonio Guterres cewa kalaman Trump hujja ce da ke nuna cewa Amurka na da hannu a rikice-rikicen da suka faru a Iran a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a watan Janairu.

    A cewar wasiƙar, Iran ta zargi Amurka da ƙoƙarin mayar da zanga-zangar lumana zuwa tashin hankali, tayar da ƙayar baya na rikice-rikicen cikin gida da kuma zubar da jini.

    Haka kuma, gwamnatin Iran ta ɗora wa Amurka alhakin dukkan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a lokacin rikice-rikicen watan Disamban 2025 da Janairun 2026.

    A lokacin waɗannan zanga-zanga, dubban mutane sun mutu. Duk da cewa gwamnati ta Iran ta ce kusan mutum 3,000 ne suka rasu, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun ce sun gano kusan mutum 7,000 da suka mutu, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu da dama.

  16. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata ga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.

Trending Now