Yaƙin Iran da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 10/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 10 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi, Usman Minjibir

  1. Jam'iyyun PRP da ADC sun gana da juna a

    ..

    Asalin hoton, PRP

    Bayanan hoto, Dr Hakeem Baba-Ahmed na jam'iyyar PRP tare da Sanata David Mark na ADC

    A daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin dangane da inda jam'iyyar adawa ta ADC za ta karkata hankalinta, jiga-jigan jam'iyyar ƙarƙashin shugabanta da INEC ta ce ba shi ne shugabna ba, Sanata David Mark sun gana da shugabannin jam'iyyar PRP a Abuja.

    A wata sanarwa, jam'iyyar PRP ta ce ta yi ganawar ne da jam'iyyar ADC domin nuna goyon baya da ƙarfafa mata gwiwa dangane da halin da take ciki tun bayan da hukumar zaɓen Najeriya ta ce ta cire sunan Sanata David Mark daga na'urarta.

    Su ma jiga-jigan jam'iyyar ta ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark da Malam Bolaji Abdullahi, sun bayyana jam'iyyar ta PRP da abokiyar aiki wadda ta kasance jam'iyya daya tilo da ta fito ta nuna damuwa kan halin da ADC ta tsinci kanta a ciki.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa jam'iyyar PRP na zawarcin ƴan jam'iyyar ta ADC.

  2. Akwai yiwuwar sufurin jirgin sama ya samu tsaiko a duniya

    Ƙungiyar da ke wakiltar filayen jiragen sama 600 a Turai ta ce ana fuskantar ƙarancin man jirgin sama wanda zai iya shafar tafiye-tafiye a lokutan bazara a bana, mutuƙar ba a sake buɗe mashigar ruwan Hormuz ba cikin makonni uku masu zuwa.

    Tuni dai wasu kamfanonin jiragen sama suka fara ƙara kuɗin tikiti saboda tsadar mai.

    Shugaban ɗaya daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama masu rahusa a Turai, Michael O’Lary na kamfanin Ryan-air, ya yi gargaɗin cewa za a iya samun ƙarancin man na kashi 50 cikin ɗari.

    Ƙungiyar ta Airports Council International ta yi kira ga Hukumar Tarayyar Turai da ta ƙara yawan samar da man jiragen sama domin rage matsalar.

  3. Ba za mu tattauna da Amurka ba sai Isra'ila ta dakatar da hare-hare a Lebanon

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Ba-gher Gha-li-baf, ya ce ba za a yi wata tattaunawa da Amurka ba har sai an tsagaita wuta a Lebanon.

    Ya kuma bukaci a saki kadarorin Iran da aka riƙe. Kalaman nasa na zuwa ne jim kaɗan bayan mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya nufi Pakistan, inda ake sa ran za a fara tattaunawa a ranar Asabar.

    Kafin tafiyarsa, ya ce kofar Amurka a buɗe take domin sasanci, matuƙar Tehran ba ta yi ƙoƙarin yaudararta ba.

  4. Babbar jam'iyyar adawar Venezuela ta nemi a yi zaɓen maye gurbin Maduro

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar Jam’iyyar adawa a Venezuela ta buƙaci a gudanar da sabon zaɓe, bayan cikar wa’adin kwanaki casa’in na doka da aka tanada, domin shirya zaɓen maye gurbin hambararren shugaban ƙasar, Nicolas Maduro.

    A cikin wata sanarwa, shugabar ‘yan adawa kuma wadda ta lashe lambar yabo ta Nobel, Maria Corina Machado, ta bukaci a gudanar da zaɓen cikin wata guda.

    Ta ce hakan ya zama dole musamman la'akari da halin da ake ciki na rashin Nicolas Maduro, wanda aka kama a wani samame da sojojin Amurka suka kai a watan Janairu.

    Ana kyautata zaton cewa ita ce ta lashe zaɓen da ya gabata, duk da cewa ba a taba bayyana sakamakon zaɓen ba.

  5. Yarima Harry na fuskantar shari'a kan ɓata suna

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Yariman Prince Harry, na Ingila na fuskantar shari'a kan zargin ɓata suna daga wata gidauniya da ya kafa tare da wasu.

    Takardun kotu sun nuna cewa a watan da ya gabata, gidauniyar Senta-ba-le, wadda ke tallafa wa matasa a yankin kudancin Afirka, ta shigar da ƙara a kansa, da kuma wasu tsoffin amintattu da suka bar aikin gidauniyar a bara bayan wani rikici.

    Ba ayi cikakken bayani kan abin da ƙarar ta ƙunsa ba.

    A bara, wani bincike da Hukumar Kula da Gidauniyoyi ta Birtaniya ta gudanar, ya gano cewa rikicin da ya ɓarke a bainar jama’a tsakanin amintattu da shugabar gidauniyar, Dokta Sophie Chan-duka, ya yi illa ga aikin gidauniyar.

    Har zuwa wannan lokaci, Prince Harry da kuma gidauniyar Senta-ba-le ba su mayar da martani ba.

  6. 'Hare-haren Isra'ila sun kashe jami'an tsaro 13 a Lebanon'

    Shugaban ƙasar Lebanon ya ce hare-haren Isra'ila sun kashe jami'an tsaron ƙasar 13 a birnin Nabatieh da ke kudancin ƙasar.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ofishin shugaban ƙasar ya ce shugaban ƙasar Joseph Auon ya yi alla wadai da hare-haren.

    Kawo yanzu rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba game da hare-haren.

  7. Martanin da Abba Kabir ya mayar wa Kwankwaso

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusf ya mayar da martani ga tsohon ubagidansa na siyasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tun bayan raba gari da mutanen guda biyu suka yi.

    A watan Janairun ne Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulki bayan ficewa daga jam'iyyar NNPP bisa dalilin rikicin da jam'iyyar take ciki.

    Watanni biyu kuma bayan nan sai shi ma sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC.

    Tun bayan raba garin ba a ji bakin Abba Kabir ba kan tsohon ubangidan nasa. Sai dai kuma a ranar Alhamis an jiyo gwamna Abba yana kakkausan martani ga maganganun da Kwankwaso ya yi kan fitarsa daga Kwankwasiyya.

    Yayin wata ziya da ƙungiyar mawaƙa da ake kira da mawallafan Abba Gida-Gida suka kai masa ranar Alhamis a gidan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausan martanin irin wanda ba a taɓa zata ba daga wurinsa kan Kwankwaso.

  8. Mabiya Yesu Almasihu ba za su jefa bama-bamai kan jama'a ba - Fafaroma Leo

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Leo XIV ya bayyana yadda yaƙi ya watsu a yankin Gabas ta Tsakiya da " rikicin rashin imani" inda ya ƙara da cewa an salwantar da rayuwar fararen hula masu yawa.

    "Babu wata riba da za ta kai darajar rayuwa ta marasa ƙarfi da yara da iyalai," kamar yadda ya fada a jerin wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na X da yammacin ranar Juma'a.

    Fafaroma Leo ya ce "babu wani mabiyin Yesu" da zai rinƙa jefa bama-bamai" kan jama'a.

    "Daukar matakan soji ba zai samar da ƴanci da zaman lafiya," in ji Leo XIV.

  9. Muna shirya makaman ƴaki ko da Iran za ta yi mana tutsu - Trump

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Amurka na ci gaba da zuba wa jiragen yaƙinta kayan yaƙi domin sake komawa fagen yaƙi da zarar tattaunawar da ake yi da Iran ta wargaje.

    Da yake magana a wata tattaunawa ta waya ga gidan jaridar New York Post a ranar Juma'a, Trump ya ce "za mu ga abin da zai faru a sa'o'i 24 masu zuwa".

    "Muna zuba wa jiragenmu na yaƙi makaman da ba taɓa ganin irinsu ba fiye da irin wadanda muke amfani da su wajen lalata abubuwa."

    "Idan ba a cimma komai ba to za mu yi amfani da su kuma za mu yi amfani da su da gaske."

    Trump ya sake bayyana Iraniyawa da mutanen da "ba su da tabbas kan faɗin gaskiya".

    Ana dab da fara tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da Iran ranar Asabar a Pakistan.

  10. Mun bar Iraniyawa a raye ne kawai domin mu tattauna - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce dalilin da kawai suka bar Iraniyawa da ransu shi ne domin a "tattauna" da su.

    A wani saƙonsa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce

    "Iraniyawa sun kasa fahimtar cewa ba su da sauran abin da ya rage musu illa tatsar duniya ta hanyar amfani da ruwan da duniya ke amfani da shi."

    Dalilin kawai da ya sa suke a raye shi ne zama a teburin tattaunawa."

  11. JD Vance na hanyar zuwa Pakistan domin tattaunawa da Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin Shugaban ƙasar Amurka, JD Vance, na kan hanyarsa ta zuwa Pakistan, inda ake sa ran zai fara tattaunawa da Iran a gobe Asabar.

    Ya ce yana fatan ganin an gudanar da tattaunawar cikin nasara a Islamabad, kuma ƙofar Amurka a buɗe take ga ƙulla sulhu, matuƙar Tehran ba ta yi ƙoƙarin yaudara ko saɓa yarjejeniya ba.

    Wakiliyar BBC ta ce Islamabad na dakon bayanai da kuma isowar manyan bakin da zasu halarci zaman tattaunawar.

    A baya dai Pakistan ta yi gargaɗi cewa akwai tazara mai faɗin sosai tsakanin matsayar ƙasashen biyu.

    Kowace ƙasa dai na zargin ɗaya da karya sharuddan yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi da aka cimma a wannan makon.

    Iran ta dage cewa dole ne yarjejeniyar tsagaita wutar ta haɗa da Lebanon, yayin da Amurka ke cewa Iran ta gaza sake buɗe mashigar Hormuz gaba ɗaya.

  12. Najeriya ƙasa ce mai aminci - Gwamnati

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu

    Asalin hoton, X/BOLA TINUBU

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu

    Ministan sadarwa na Najeriya Mohammed Idrsi ya bayyana cewa ƙasar na cike da aminci, ƴan kwanaki bayan Amurka ta umarci ma'aikatan diflomasiyyarta da ayyukansu ba su zama wajibi ba su bar babban birnin ƙasar, Abuja.

    Amurka ta ce ta ɗauki matakin ne sanadiyyar "taɓarɓarewar harkar tsaro a ƙasar".

    Haka na Amurkar ta buƙaci ƴan Amurka da ke son zuwa Najeriya su sauya tunani sanadiyyar laifuka na "ta'addanci da manyan laifuka da kuma garkuwa da mutane".

    Ministan na Najeriya ya bayyana kalaman na Amurka a matsayin shawarwari kawai, ba wai halin da ƙasar ke ciki ba.

    "Mun yarda cewa akwai matsalar tsaro kaɗan, nan da can, amma babu taɓarɓarewar doka da oda, kuma mafi yawan fadin ƙasar na cikin aminci".

    Ya bayyana cewa matakan da ake ɗauka a fadin ƙasar na rage matsalolin tsaro a ƙasar.

  13. Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a cikin Lebanon

    Wani gini da harin Isra'ila ya lalata ranar Alhamis a birnin Beirut

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani gini da harin Isra'ila ya lalata ranar Alhamis a birnin Beirut

    Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan ƙungiyar Hezbollah a Lebanon duk da kiraye-kirayen ƙasashen duniya na a dakata.

    Isra'ila ta umarci al'ummar kudancin Lebanon da su gaggauta ficewa domin kauce wa hare-haren da take shirin kaiwa.

    Hezbollah ita ma ta ce ta harba rokoki zuwa cikin Isra’ila a daren jiya da kuma yau Juma’a.

    Sai dai ana ƙoƙarin ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin Isra’ila da gwamnatin Lebanon, duk da cewa Beirut ta sake tabbatar wa BBC cewa masu shiga tsakani daga Lebanon ba za su halarci tattaunawa kai tsaye da Isra’ila ba sai an tsagaita wuta.

    Shugaban Hezbollah, Na'im Qassem, ya buƙaci gwamnatin Lebanon da ta daina yin abin da ya kira ɗaga kafa ga Isra’ila.

  14. Ƙofar Amurka a buɗe take idan Iran ta zo tattaunawa da kyakkyawar manufa - Vance

    Mataimakin shugaban Amurka JD Vance wanda yanzu haka ke kan hanyarsa ta zuwa Pakistan domin tattaunawar sasanci da Iran ya ce "ƙofar Amurka a buɗe take" idan har Iran ta je da "kyakkyawar manufa".

    Amma ya ƙara da cewa idan "suka yi yunƙurin yaudarar mu" ba za mu ɗaga musu ƙafa ba.

    Ya bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump ya ba shi sharuɗɗan da za a yi amfani da su wajen tattaunawar.

    Za a fara tattaunawar ne a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan a ranar Asabar, kamar yadda mai magana da fadar shugaban Amurka, Karoline Leavitt ta sanar tun farko.

    Tawagar Amurka a wurin tattaunawar za ta haɗa da jakadan shugaba Trump na musamman Steve Witkoff da kuma Jared Kushner, to amma har yanzu ana jiran isar tawagar Iran a birnin Islamabad.

  15. Mataimakin shugaban Amurka ya kama hanyar zuwa tattaunawar sasanci

    Mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mataimakin shugaban ƙasar Amurka J.D. Vance

    Mataimakin shugaban ƙasar Amurka J.D Vance yana kan hanyar zuwa Pakistan a shirye-shiryen tattaunawar sasanci da za a fara tsakanin ƙasarsa da Iran a gobe Asabar.

    Ya ce ya ƙagu a fara tattaunawar ta birnin Islamabad sannan yana fatan a samu fahimtar juna.

    Tun farko, Pakistan ta yi gargaɗin cewa buƙatun ƙasashen biyu game da yarjejeniyar sun yi hannun riga sosai.

    Dukkanin ɓangarorin biyu na zargin juna da karya sharuɗɗan tsagaita wuta da aka cimma a farkon wannan mako.

    Iran ta dage kai da fata cewa wajibi ne tsagaita wutar da aka cimma ta haɗa har da Lebanon, ita kuma Amurka ta zargi Iran da ƙin buɗe mashigar Hormuz ga jiragen dakon man fetur na duniya.

  16. Majalisar dokokin Iran na son a haramta wa jiragen Isra'ila bi ta Hormuz har abada

    Majlisar dokokin Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Majlisar dokokin Iran

    Majalisar dokokin Iran ta samar da wani daftarin dokoki kan yadda ƙasar za ta riƙa iko da mashigar Hormuz, kuma ana sa ran kaɗa ƙuri'a kan daftarin a cikin mako mai zuwa.

    Shugaban hukumar kula da ayyuka na majalisar, Mohammed Reza Rezaei Kochi ya ce daftarin ya ƙunshi sauye-sauye kan yadda jiragen ruwa ke ratsawa ta mashigar Hormuz sannan kuma akwai tsarin karɓar kuɗaɗe daga jiragen.

    Mista Kochi ya bayyana wa kafar dillancin labarai ta Fars cewa "ɗaukacin ƴan majalisar za su amince da daftarin sannan daga baya a sanar da fara amfani da shi".

    Bayanai sun nuna cewa daftarin ya ƙunshi wasu matakai guda biyar:

    - Haramcin ratsawar jiragen abokan gaba: Za a haramta wa duk wani jirgin dakon man fetur mai alaƙa da Amurka da Isra'ila ratsawa ta mashigar Hormuz har abada.

    -Karɓar haraji: Za a karɓi kuɗi a matsayin jangali kan aikin yin jagora da tabbatar cewa jiragen ruwa sun ratsa ta wannan mashiga cikin aminci.

    -Tallafa wa takardar kuɗin Iran: A ƙoƙarin bunƙasa darajar takardar kuɗi ta riyal, duk wani jirgi mai ratsawa zai biya jangali ne ta amfani da takardar kuɗin Iran ta Riyal.

    -Amfani da sunan Mashigar Gulf: Za a buƙaci duk wani jirgin da zai ratsa ya yi amfani da asalin sunan da aka san mashigar da shi, wato mashigar Persia a duk takardun da za a cike da kuma bayanan da suke bayarwa na tafiya.

    -Yadda za a kasafta kuɗi: Za a kasafta kuɗaɗen jangali da aka samu kamar haka: Za a kashe kashi 30% wajen ƙarfafa soji da tabbatar da tsaron yanki, sai kuma kashi 70% don inganta rayuwar al'umma.

  17. Tinubu ya jajanta kan kisan sojoji a Borno

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu

    Asalin hoton, X/Bola Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa al'ummar ƙasar kisan da aka yi wa sojoji a wani hari da mayaƙa suka kai kan wani sansanin soji a jihar Borno, arewa maso gabashin ƙasar.

    "Ina miƙa saƙon ta'aziyyata ga iyalan jajirtattun sojojinmu ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare ƙasarmu a jihar Borno," kamar yadda shugaban ya bayyana a wani bayani da ya fitar a jiya Alhamis.

    A ɗaya ɓangare, cikin wata sanarwa, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile harin da aka kai kan sansanin soji a garin Benisheik ranar Alhamis, sai dai rundunar ba ta tabbatar ko ƙaryata kashe sojoji ba.

    Wasu mazauna yankin da abin ya faru sun shaida wa BBC cewa babban sojan da ya jagoranci yunƙurin dakile harin Birgediya Janar Oseni Braimah na cikin waɗanda aka kashe.

    Kafar yaɗa labarai ta AFP ta bayar da rahoton kashe babban sojan, inda ta kafa hujja da bayanai daga majiyoyin tattara bayanan sirri, duk da cewa sojojin Najeriya ba su tabbatar da hakan ba.

    Harin na cikin hare-hare na baya-bayan nan da masu iƙirarin jihadi ke kaiwa kan sansanonin soji a arewa maso gabashin Najeriya, inda mayaƙa suka kwashe sama da shekara 10 suna kai hare-hare.

  18. Ko tattaunawar Iran da Amurka a Pakistan za ta yiwu?

    Shugaban Amurka Donald Trump da jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, Multiple

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump da jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei

    Ana shirye-shiryen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a Pakistan, wadda za ta gudana a cikin ƙarshen mako.

    Sai dai ya zuwa yanzu babu sanarwa a hukumance da ke nuna cewa tawagogin ɓangarorin biyu sun isa Islamabad, birnin da za a yi ganawar.

    Pakistan na ci gaba da kyautata fatan yiwuwar tattaunawar, da kuma fatan cewa za a samu fahimtar juna.

    To amma a halin yanzu kowa jininsa a ƙumba: A wani saƙon da aka wallafa a shafin sada zumunta, kafin daga baya aka goge, ministan tsaron Pakistan ya bayyana Isra'ila a matsayin "tsinuwa ga bil'adama".

    Isra'ila ta ce ba za a amince da irin haka ba daga ƙasar da ta ce za ta yi aikin sasanci.

  19. Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka na rawa

    Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Iran na fuskantar barazana, kwana ɗaya gabanin ganawar ƙeƙe-da-ƙeƙe da ake sa ran ɓangarorin biyu za su yi a Pakistan.

    Shugaba Trump na Amurka ya zargi Iran da karya sharuɗɗan yarjejeniyar ta hanyar ƙin buɗe mashigar Hormuz ga jiragen ruwan dakon man fetur.

    Hukumar kula da sufurin ruwa ta duniya ta ce jiragen ruwa ƙalilan ne suka samu damar ratsawa ta mashigar tun bayan cimma yarjejeniyar.

    A ɓangare ɗaya kuma Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a ƙasar Lebanon - abin da Iran ta ce ya saɓa da sharuɗɗan yarjejeniyar.

  20. 'Ba haka muka yi da Iran ba': Trump kan mashigar Hormuz

    Shugaban Amurka Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi Iran da kin barin jiragen dakon mai su wuce ta mashigin Hormuz, yayin da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ke tanga-tangal, kafin hawa teburin sulhu a karshen makon nan a birnin Islamabad na Pakistan.

    A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Mista Trump ya ce hakan ya saɓa wa yarjejeniyar da aka cimma, sannan ya gargaɗi Tehran da kada ta ƙaƙaba kuɗin wucewa ga jiragen ruwan.

    Buɗe mashigar Hormuz na daga cikin wani ɓangare na yarjejeniyar, to sai dai jirage tsiraru ne suka samu wucewa tun bayan fara aiki da yarjejeniyar.

    Tun da farko yayin wani jawabi da ya gabatar, jagoran addinin Iran din Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya ce a yanzu mashigin na Hormuz ya shiga wani sabon mataki.

    A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin din kasar, Mojtaba Khamenei ya ce Iran na da yancin daukar fansa kan hare-haren Amurka da Isra’ila, kana za ta kare kawayenta, watau Hezbollah da sauran kungiyoyin yan turjiya a gabas ta tsakya.

    Ƙasar Pakistan ta ce tana da yaƙinin cewa tattaunawar zaman lafiyar da za a yi a Islamabad a karshen wannan mako za ta gudana kamar yadda aka tsara.

Trending Now