Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Muna godiya da bibiyarmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 22/03/2026
Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Muna godiya da bibiyarmu.

Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
Manyan jiga-jigan hamayyar siyasar Najeriya na wata ziyara a gidan jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Cikin waɗanda ke ziyarar har da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar LP, Peter Obi da gwamnan Oyo Seyi Makinde da Sanata Seriake Dickson da sauransu

Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya ce ƴan siyasar sun kai masa ziyarar gaisuwar sallah ne.
Kwankwaso - wanda ke jam'iyyar NNPP mai hamayya - ana tunanin zai sauya sheƙa zuwa wata jam'iyyar, bayan da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP zuwa APC mai mulki.

Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
A cikin watannan ne dai Peter Obi ya sanar da komawarsa ADC a hukumace, yayin da gwamnan Oyo Makinde ya kasance gwamna na biyu bayan na Bauchi da suka rage a jam'iyyar PDP.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Isra'la ta ce sabbin hare-haren Iran sun nufi cikin Isra'ila.
Cikin wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na Telegram, ta ce tana ƙoƙarin kakkaɓo hare-haren yayin da aka aike da saƙon gargaɗi ta waya ga mazauna yankunan da hare-haren suka dosa.
Kafar yaɗa labaran IRIB, mallakin gwamnatin Iran ta ce an fara ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami na Iran.
A wani labarin na daban ma'aikatar tsaron UAE ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami huɗu da jirage marasa matuƙa 25 da Iran ta harba ƙasar a ranar Lahadi.
Cikin wani saƙo da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce tun bayan fara yaƙin Iran ta kakkaɓo makaman linzami fiye da 350 da jirage masara matuƙa fiye da 1,750 da Iran ta harba mata
Kamfanin Dillancin Labaran Lebanon ya ambato ma'aikatar lafiyar ƙasar na cewa an kashe mutum huɗu tare da jikkata wasu bakwai a wasu samame da sojojin Isra'la suka kai wasu yankunan ƙasar biyu.
An kashe mutum uku a garin Sultaniyeh sannan aka kashe guda a garin Marjeyoun da ke makabtaka, dukkansu a kudancin ƙasar.
Dakarun juyin juya halin Iran, IRGC sun ce za su datse gaba É—ayan mashigar Hormuz idan har aka kai hari kan tasoshin samar da lantar na IRan.
Cikin wata sanarwa da kafofin yaÉ—a labaran Iran suka yaÉ—a, rundunar IGRC ta ce babu abin da zai hana ta É—aukar wannan mataki idan har aka hari cibiyoyin makamashinta.
Tun da farko Shugaba Trump ne ya yi barazanar ''lalata'' tasoshin lantarkin Iran idan ba ta buÉ—e mashigar Hormuz ba nan da kwana biyu.

Asalin hoton, AP
Firaministan Isra'ila Benjami Netanyahu ya buƙaci Isra'ilawa su riƙa ɓuya idan sun ji ƙarar sautin ankararwa.
Netanyahu ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci garin Arad da ke kudancin ƙasar, inda wani harin makami mai linzami na Iran ya faɗa a kansa.
Fiye da mutum 80 ne suka jikkata a lokacin harin kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar ta bayyana.
Netanyahu ya ce abin "mu'ujiza" babu wanda ya mutu a harin, inda ya yi kira ga Isra'ilawa kada su ''daddara'', su riƙa neman wurin ɓuya da zarar sun ji sautin ankararwa.
"Sauti ya riƙa kaɗawa har na tsawon minti 10 sannan makamin ya sauka,'' in ji shi.
“Sannan makamain ya faɗa a nan tsakanin gine-gine. Da a ce kowa ya gudu ya ɓoye a cikin waɗannan mintuna a wuraren ɓuya da ke ƙasan kowane gini, da babu wanda zai jikkata,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Iran Massoud Pezeshkian ya naɗa sabon shugaban riƙo na hukumar tattara bayanan sirri na ƙasar bayan kisan shugaban hukumar Ismail Khatib.
Mataimakin shugaban ƙasar na musamman kan fanonin sadarwa, mehdi Tabatabaei ne ya bayyana haka a shafinsa na X, inda ya ce naɗin ya fara aiki ne nan take.
An kashe Ismail Khatib ne ranar 16 ga watan Maris a harin da Isra'ila ta kai birnin Tehran.
Isra'ila ta ce ta kashe mayaƙan ƙungiyar Hezbolla tara a kudancin Lebanon.
A cewar rundunar sojin Isra'ilar, dakarunta na sama da ƙasa ne suka ƙaddamar harin da ya kai ga kisan mambobin ƙungiyar.
Sojojin na Isra'ila sun ce ƴanƙungiyar ta Hezbolla ne suka ''nufo'' inda sojojin Isra'ila da ke gudanar da aiki a kudancin Lebanon suke cikin daren da ya gabata.
A cewar sojojin na Isra'ila, babu É—aya daga cikin dakarunsu da ya jikkata a lokacin harin.

Asalin hoton, Reuters
Babban kwamandan shlkwatar rundunar sojin Iran da ake yi wa laƙabi da Khatam al-Anbiya ya ce 'salon' yaƙin ƙasar ya sauya daga kare kai zuwa ƙaddamar da hare-hare.
''Don haka mun sauya salon yaƙin dakarunmu da ke filin daga'', in ji shi.
Kafofin yaɗa labaran Iran, sun ce Manjo Janar Abdollahi ya ce tuni ƙasar ta ''ƙera sabbin makamai na zamani'', waɗanda da su ya ce za su wargaza shirin waɗanda ya kira ''maƙiya''.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce wani hari da aka kai kan wani asibiti a jihar East Dafur ta Sudan ya hallaka aƙalla mutum 64 da suka haɗa da yara, da jikkata wasu kusan 90.
Da yake bayani daga irin kalaman da ma'aikatan asibitin da marassa lafiya suka yi masa, shugaban hukumar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce harin da aka kai ranar Juma'a a kan asibitin koyarwa na Al Daein, ya sa an daina aiki a asibitin.
Ƙungiyar RSF ta zargi rundunar sojin Sudan da amfani da jirgin sama maras matuƙi kirar Turkiyya wajen kai harin.
Sai dai a wata sanarwa ita ma rundunar sojin ta Sudan ta yi watsi da zargin , inda ta ce RSF É—in ce ta kai harin.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar tsaron Qatar ta ce mutum shida sun mutu bayan wani jirgi mai saukar ungulu na ƙasar ya faɗo.
Qatar ta ce jirgin ya rikito ne a lokacin da yake gudanar da atisayen da ya ''saba yi'' bayan ya gamu da matsalar na'ura.
"Bayan ƙoƙarin nema, an samu nasarar gano gawarwakin mutum shida cikin bakwai da ke cikin jirgin,'' kamar yadda ma'aikatar tsaron ƙasar ta bayyana a shafinta na X.
Ma'aikatar ta ce cikin waÉ—anda suka mutu har da Æ´an Turkiyya biyu fararen hula da sojan Turkiyyar É—aya.
Game da wannan: A cikin makonnin baya-bayan nan Qatar na fuskantar hare-haren Iran. Kuma a wannan mako Iran ta kai hari kan babbar cibiyar adana gas ɗin Qatar. To amma ba a sani ba ko haɗarin wannan jirgi na da alƙa da yaƙin Iran ko a'a.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Sabbin hotuna sun fara fitowa na ɓarnar da hare-haren Iran suka yi a biranen Dimona da Arad da ke kudancin Isra'ila da muka bayar da rahotonsu a baya.
Harin Arad ya lalata gine-gine masu yawa, tare da haifar da ƙaton rami mai matuƙar zurfi a garin.

Asalin hoton, Reuters
Can ma a garin Dimona harin makami mai linzamin Iran ya kauce wa na'urar tsaron samaniyar Isra'ila.
Mutane da dama ne suka jikkata a harin na Dimona mai nisan kilomita 13 daga cibiyar binciken nukiliyar Iran.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Getty Images
Wani ɗan majalisar dokokin Iran mai suna, Alaeddin Boroujrrdi ya yi iƙirarin cewa ƙasar na karɓar dala miliyan biyu ga wasu jiragen ruwan da ke bi ta mashigar Hormuz.
Yayin wata hira da wani gidan talbijin na ƙasar a yau, Mista Boroujrrdi ya ce ''sabuwar gwamnatin'' ƙasar ce ta saka wannan doka a mashigar, ''kuma yaƙin ne ya janyo hakan''.
Ya ƙara da cewa hakan na nuna cewa ''hukukomin Iran na da dama da haƙƙin da Jamhuriyar Musuluncin ke da shi''.
BBC ba ta iya tabbatar da ingancin wannan iƙirarin ba.

Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta Isra'ila ta ce fiye da mutum 160 ne suka samu munanan raunuka a ƙasar bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai garuruwan Dimona da Arad da ke kudancin ƙasar.
Jami'an ma'aikatar sun ce mutum 84 ne suka jikkata a garin Arad yayin a Dimona suka kai 78 bayan da makamin Iran mai linzami ya faɗa kan garuruwan, waɗanda ke kusa da cibiyar nukiliyar ƙasar.
Hukumar kula da makamin nukiliya ta duniya, (IAEA) ta ce ba ta da labarin samun kowace irin ɓarna a cibiyar binciken nukiliyar da ke da tazarar kilomita 13 daga garin Dimona.
Tun da farko kafofin yaÉ—a labaran Iran sun ce harin martani ne kan harin ranar Asabar da Isra'ila ta kai wa cibiyar nukiliyar Iran ta Natanz.
Hukumar IAEA ta ce ''ba a samu rahoton tashin tiririn iska'' ba bayan harin na Natanz.

Asalin hoton, Reuters
Hukumomin Saudiyya sun umarci, babban jami'in soji na ofishin jakadancin Iran da wasu ma'aikatan ofishin huɗu da ke Saudiyyar su fice daga ƙasar cikin sa'a 24.
Matakin na zuwa ne bayan da Saudiyyar ta ayyana su a matsayin waÉ—anda ba ta maraba da su.
A wata sanarwa da ma'aiakatar harkokin wajen Saudiyyar ta fitar ta ce ci gaba da hare-haren da Iran ke kai wa ƙasar, na nuni da fadada yaƙin, kuma zai yi tasiri sosai a kan dangantakar Iran da makwabtanta.
Iran dai na kai hare-hare kan ƙasashe maƙwabtanta da ta zarga da bai wa sojojin Amurka sansani a cikinsu.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya yi barazanar tarwatsa duka tashoshin samar da lantarki na Iran, idan har gwamnatin ƙasar ba ta buɗe mashigar Hormuz ba, cikin sa'a 48.
Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin hanyoyin mafiya muhimmanci na jigilar mai, kuma duk wani mataki na rufe ta na haifar da illa sosai ga tattalin arziƙin duniya.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Trump ke barazanar kai hari kan tashoshin samar da makamashi na Iran ba.A ranar Alhamis ya ce Amurka za ta tarwatsa tashar samar da iskar gas ta South Pars.
Iran É—in ta mayar da martani da cewa muddin aka kai wa kayayyakinta na mai da makamashi hari to ba makawa za ta mayar da martani ta hanyar kai hari a kan dukkanin wasu kayayayyakin samar da makamashi na Amurka da ke yankin.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da ci gaba da shagulgulan sallah.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.
Ku ci gaba da bibiyarmu a wannan shafi da ma shafukanmu na sada zumunta domin bayyana mana ra'ayoyinku