Yaƙin Iran da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 09/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf

  1. Benjamin Netanyahu ya umarci ministocinsa da su fara tattaunawa da Lebanon

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ya umurci majalisar ministocinsa da su fara tattaunawar kai tsaye da gwamnatin Lebanon cikin gaggawa.

    Sanarwar ta zo ne jim kaɗan bayan da sojojin Isra'ila suka fitar da wani sabon gargaɗi na ficewa ga mazauna yankunan kudancin babban birnin ƙasar Lebanon.

    Dakarun sojin Isra’ilar dai sun ce sun kai hari wuraren da kungiyar Hezbollah ke amfani da shi wajen kai hare-hare a Lebanon.

    Wannan na zuwa ne ba da jimawa ba, bayan Benjamin Netanyahu ya ce ya umarci majalisar ministocinsa da su fara tattaunawa kai tsaye da gwamnatin Lebanon cikin gaggawa.

    Wakilin BBC ya ce Mista Netanyahu ya ce tattaunawar za ta mayar da hankali kan kwance damarar Hezbollah da kuma kafa dangantaka ta zaman lafiya.

    Sai dai Isra’ila ta fuskanci suka sosai saboda hare-haren da ta kai a jiya Laraba, inda ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce mutane fiye da ɗari uku ne suka rasa rayukansu.

    Wani jami’in Lebanon ya ce gwamnatinsu na son a cimma tsagaita wuta kafin fara kowace irin tattaunawa da Isra’ila.

  2. Amurka ta dakatar da bayar da bizarta a Abuja

    Tinubu and Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya sanar da soke duk wasu buƙatun neman biza da aka shigar.

    Ta buƙaci masu neman shiga ƙasarta su duba saƙonninsu na imel don samun cikakkun bayanai kan mataki na gaba.

    A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ofishin Jakadancin Amurkar ya ce za a ci gaba da gudanar da tantance neman bizar a ofishin jakadancinta da ke Legas.

    Sanarwar ta ce jami'anta za su ci gaba da duba bayanan ƴan Amurka ne kawai a yanzu musamman ga masu buƙatar gaggawa.

    Wannan matakin na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta buƙaci jami'anta da ke aiki a Najeriya su yi gaggawar barin ƙasar, saboda dalilai na tsaro.

    Amurkar ta ce duk waɗanda ayyukansu ba su zama wajibi ba, da ke a ofishin jakadancinta a birnin tarayya Abuja, su tattara kayansu da iyalai domin barin ƙasar.

    A wani saƙo da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Amurkar ta kuma lissafa wasu jihohin Najeriyar 23 daga kudu da arewacin ƙasar, inda ta ce suna da haɗari, kuma ta gargaɗi ƴan ƙasarta su guji tafiya zuwa waɗannan jihohin da ta ɗora su a mataki na huɗu na gargaɗi.

  3. Hare-haren Isra'ila kan Lebanon ba daidai ba ne - Starmer

    Kier

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Lebanon "ba daidai ba ne" kuma "ya kamata ta dakata".

    A wata hira da tashar talabijin ta ITV, ya ce duk da haka "da wuya a ce" sun karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta na wucin gadi da aka kulla tsakanin Amurka da Iran a wannan makon.

    "Ba mu samu damar ganin dukkan bayanan tsagaita wutar ba," in ji shi, amma ya kara da cewa "bai kamata a ci gaba da kai hare-haren ba".

    Ya ce hujjarsa ita ce "ya kamata a sanya Lebanon cikin tsagaita buɗe wutar kuma wannan ya kamata ya zama wani muhimmin bangare".

  4. Pakistan ta tabbatar mana cewa muna cikin yarjejeniyar tsagaita wuta - Lebanon

    Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya nemi takwaransa na Pakistan da ya tabbatar masa cewa Lebanon na cikin yarjejeniyar tsagaita wuta, kwana guda bayan hare-haren Isra’ila da suka kashe sama da mutane 200 a ƙasar.

    Ofishin Mista Salam ya bayyana cewa ya kira Shahbaz Sharif domin nuna godiya ga ƙoƙarin Islamabad wajen samar da tsagaita wuta, sannan ya roƙe shi da ya “tabbatar da cewa yarjejeniyar ta haɗa da Lebanon domin hana sake aukuwar irin hare-haren da suka faru jiya.”

    Sai dai Isra’ila da Amurka sun bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wutar ba ta shafi Lebanon ba, kuma Isra’ila ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan ƙungiyar Hezbollah.

    A gefe guda, kakakin majalisar dokokin Iran ya gargadi cewa Tehran na kallon Lebanon a matsayin “ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta,” tare da yin barazanar mayar da martani mai ƙarfi.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kiran ƙasashen duniya su tabbatar an haɗa Lebanon cikin yarjejeniyar tsagaita wutar.

  5. Qatar da UAE sun ce su na ci gaba da kakkaɓo makamai masu linzami

    Dakarun ƙasar Qatar sun ce sun daƙile harin makami mai linzami da aka kai musu kan iyakokinsu.

    Ma'aikatar tsaron kasar ta rubuta a shafukan sada zumunta cewa ta kawar da barazanar "da yardar Allah.

    Ita ma Ma'aikatar tsaron Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce na'urorin tsaron saman kasar suna "ci gaba" da kakkaɓo hare-haren da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.

    Ma'aikatar a wani sakon da ta wallafa a dandalin sada zumunta na X ta ce: "Ana buƙatar jama'a da su kwantar da hankulansu tare da bin ka'idojin tsaro da hukumomin suka bayar."

  6. Mutanen da suka mutu a harin Isra'ila kan Lebanon sun haura 300

    A

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon a ranar Laraba ya ƙaru zuwa fiye da mutane 300, a cewar ma'aikatar lafiya ta kasar.

    Ta ce harin ya jikkata mutum sama da 1,150.

    A baya dai an bayyana cewa an kashe mutane 203 tare da jikkata sama da 1,000 a hare-haren.

    Yanzu haka dai ƙasar Labanon na zaman makoki bayan hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai kan ƙungiyar Hezbollah.

  7. Baƙin haure huɗu sun mutu a yunkurin ƙetarewa daga Faransa zuwa Ingila

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla baƙin haure 4 ne suka mutu yayin da suke yunkurin ketarewa daga Faransa zuwa Ingila ta wani ƙaramin kwale-kwale.

    Hukumomin Faransa sun ce maza 2 da mata 2 ne suka nutse sakamakon kaɗawar Igiyar ruwa.

    Ba a san ƙasashen da waɗanda suka mutu suka fito ba, amma a ci gaba da kula da sauran baƙin haure kusan 40 a wajen da lamarin ya faru.

    Sai dai kwale-kwalen ya ci gaba da tafiyarsa dauke da kusan mutane talatin a cikinsa.

    Kawo yanzu a wannan shekara, mutane dubu biyar sun samu nasarar ƙetarawa Ingila ta wannan hanya mai hadari.

  8. Koriya ta Kudu za tura jakada na musamman zuwa Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministocin harkokin wajen Tehran da Seoul, ƙasar za ta aika da jakada na musamman zuwa Iran domin tattauna halin da ake ciki a yankin.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Koriya ta Kudu, Yonhap, ya ruwaito cewa ministan harkokin wajen ƙasar, Cho Hyun ya yi magana ta waya a yau da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, inda Seoul ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka.

    Haka kuma, Koriya ta Kudu ta jaddada muhimmancin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin ‘yanci ta mashigar Hormuz.

  9. Burin maƙiya na taƙaita arziƙin ƙasarmu mu ba zai tabbata ba - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliyar Iran, Mohammad Eslami, ya jaddada cewa ƙasar ba za ta amince a takaita shirinta na sarrafa uranium ba.

    Eslami ya bayyana hakan ne a gangamin cika shekaru 40 da kisan tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci, Ali Khamenei.

    Shugaban ya ce Tehran ba za ta amince da kakaba mata takunkumi kan shirinta na tace sinadarin uranium ba, wani muhimmin sharadi da Amurka da Isra’ila ke nema a yakin da suke yi.

    Ya ce irin waɗannan sharudda burika ne kawai da za su tafi a banza.

    Dangane da wata bukata ta Amurka kan buɗe mashigar Hormuz gaba daya, Tarayyar Turai ta ce bai kamata a bari Iran ta rika karbar haraji daga jiragen ruwa masu amfani da hanyar ba.

    Tun da farko, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Kha-tib-zadeh, ya ce hare-haren Isra’ila kan Hezbollah a Lebanon sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta, yana mai cewa dole ne Amurka ta yanke shawarar ko tana son zaman lafiya ko yaki.

  10. Lebanon ta ce mutum 203 sun mutu a hare‑haren Isra’ila jiya

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikata lafiyar ƙasar Lebanon ta ce mutum 203 ne suka mutu a hare‑haren da Isra’ila ta kai jiya yayin da Iran ta ce wannan babbar keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ne.

    Ma’aikatar ta kuma ce fiye da mutum 1,000 ne suka jikkata a hari na ranar.

    Iran ta bayyana cewa ci gaba da hare‑haren Isra’ila a Labanon wani “babbar keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ne tana mai cewa yarjejeniyar ta ƙunshi daina gaba ɗaya duk wani abu na tashin hankali.

    Iran ta yi Allah wadai da ayyukan sojojin Isra’ila a matsayin karya wannan yarjejeniya kuma ta yi barazanar iya janye wa daga yarjejeniyar idan har irin waɗannan hare‑haren suka ci gaba.

  11. Ya kamata Amurka ta ja kunnan Isra'ila kan hari a Lebanon, Paul Adams - Wakilin diflomasiyya na BBC

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu sharhi na ganin cewa ya kamata Amurka ta ja kunnen Isra’ila kan hare-haren da take kai wa a Lebanon, duk da cewa harin da ya faru a jiya bai zo da mamaki ba.

    Duk da cewa jami’an Amurka, tun daga shugaban ƙasar har zuwa sauran manyan jami’ai, sun nace cewa Lebanon ba ta cikin tsarin tsagaita wutar da aka cimma a yaƙin Iran, ra’ayoyin Iran da firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, sun sha bamban.

    Amma kowa ya san cewa ci gaba da fada a Lebanon na iya lalata tattaunawar sulhu da mayar da yankin cikin yaƙi.

    Don haka, sai dai idan Donald Trump na ganin wannan abu a matsayin abin so, amma lokaci zai zo da Amurka za ta ja kunnan Isra'ila kan harin da take kai wa a Lebanon a fili ko a ɓoye.

    Isra’ila ta gane cewa lokaci na iya ƙare mata kan yaƙin da take yi a Lebanon, don haka ta ƙara ƙaimi a hare-haren ta yayin da har yanzu tana da goyon bayan diflomasiyyar Amurka.

  12. Harin masu iƙirarin jihadi 'ya kashe wani babban jami’in soja' a jihar Borno

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami’i a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ce an kashe wani babban jami’in soja a wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai kan sansanin soji.

    Shugaban ƙaramar hukumar Kaga ya ce Birgediya Janar O. O. Braimah ya rasu ne bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari sansanin da ke Benisheikh cikin dare.

    Wannan ne karo na biyu da aka kashe janar ɗin Soji a arewacin Najeriya cikin ƴan watannin da suka gabata.

    Rahotanni sun ce wasu jami’an tsaro, da na rundunar tsaro JTF, da kuma wasu ‘yan tada kayar baya ma sun mutu a harin da aka kai a ranar Alhamis.

  13. Harin da Isra'ila ta kai wa Lebanon ya ƙeta yarjejeniyar tsagaita wuta - Shugaban Iran

    ...

    Asalin hoton, AA Video/Anadolu via Getty Images

    Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezzekian, ya bayyana hare-haren da Isra’ila ta kai a jiya da yau a Lebanon a matsayin “keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma”, yana mai cewa “Iran ba za ta taɓa barin ‘yan’uwa mata da maza na Lebanon su kaɗai ba.”

    Shugaban ya bayyana hakan ne a shafin sada zumuntarsa na X, inda ya kuma kira hare-haren na Isra’ila da cewa “alama ce mai haɗari ta yaudara da rashin bin yarjejeniyoyi.”

    Ya ƙara da cewa: “Ci gaba da waɗannan hare-hare zai sa tattaunawa ta zama marar amfani,” tare da yin barazanar cewa “Iran za ta fice daga yarjejeniyar idan har hare-haren suka ci gaba.”

  14. Firaministan Birtaniya ya isa UAE don tattaunawa kan yaƙin Iran

    ...

    Asalin hoton, PA

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya isa ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a ci gaba da ziyararsa da yake yi a Gabas ta Tsakiya domin tattaunawa kan rikicin Iran.

    Ziyarar ta zo ne a lokacin da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ke fuskantar ƙalubale, yayin da Iran ta bayyana cewa ci gaba da hare‑haren Isra’ila a Labanon wani “babban keta yarjejeniyar” ne.

    A baya, Starmer ya gana da Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya a birnin Jeddah, kuma ana sa ran zai gana da Shugaban UAE, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan don ci gaba da tattaunawa kan matsalolin tsaro da zaman lafiya a yankin. .

  15. Iran da Saudiyya sun tattauna a karon farko tun bayan fara yaƙi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin Wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Saud, ya tattaunawa ta waya da takwaransa na Iran, Abbas Araqchi, a karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙi da hare‑haren Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Wannan shi ne mataki na farko na hulɗa kai tsaye tsakanin ƙasashe biyu a cikin wannan rikici.

    Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana a shafin ta na X cewa ministocin biyu sun tattauna kan sabbin abubuwan da suka faru a yankin, tare da bincikar hanyoyin rage tashin hankali don dawo da tsaro da kwanciyar hankali a yankin

  16. An sake buɗe masallacin Al-Aqsa da saura wuraren bauta a Birnin Kudus

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    ‘Yan sandan Isra’ila sun sanar cewa za a sake buɗe wuraren ibada a Birnin Kudus ga masu ziyara da masu ibada bayan cimma tsagaita wuta na wucin gadi a rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Waɗannan wurare sun haɗa da Masallacin Al-Aqsa da Western Wall, da Cocin Holy Sepulchre a Tsohuwar Birni, wadanda suke daga cikin wuraren ibada mafi muhimmanci ga Musulmai da Yahudawa da Kiristoci.

    Sakamakon yaƙin da Iran ke yi da Amurka da Isra’ilan ne aka rufe wadannan wurare.

    Birnin Kudus ta kasance wurin da kullum cike take da mazauna, masu sayayya a kasuwa da masu yawon bude ido, da masu ibada.

    ‘Yan sanda sun ce za a buɗe wuraren ne a safiyar Alhamis, kuma za a tura ƙarin ‘yan tsaro da dama don tabbatar da tsaro.

  17. Farashin mai ya sake tashi saboda rashin tabbas a tsagaita wutar Amurka da Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin mai ya sake tashin gwauron zabo a kasuwannin Asiya da safiyar yau Alhamis saboda rashin tabbas a yarjejeniyar tsagaita Wutar Amurka da Iran, bayan ya faɗi saboda tsagaita wuta na makonni biyu.

    Farashin mai nau'in Brent ya tashi da kashi 2.2 cikin 100 zuwa dala $96.70 kan kowanne ganga, yayin da farashin ɗanyen man Amurka na West Texas ya tashi da kashi 2.8 cikin 100 zuwa dala $96.90.

    Bayan ci gaba da harin Isra’ila a Lebanon, an fara samun rashin tabbas a yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka.

    Farashin mai nau'in brent dai ya faɗi da kashi 15 cikin 100 zuwa ƙasa da dala $92 kan kowanne ganga a farkon ranar Laraba bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta, amma a ranar kuma ya sake tashi

    Farashin mai har yanzu ya fi na kafin barkewar yaki a ranar 28 ga Fabrairu tsada.

  18. Spain ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Spain, José Manuel Álvarez, ya sanar da cewa ƙasar za ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Tehran, wanda aka rufe a watan Maris saboda yaƙi, bayan cimma matsaya ta tsagaita wuta tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran.

    "Na umarci jakadanmu a Tehran da ya koma Iran," in ji ministan a lokacin da yake magana da ‘yan jarida a Madrid.

    Mista Álvarez ya ƙara da cewa da komawar ƙasar za ta ba da gudummawa ga ƙoƙarin zaman lafiya ta duk hanyoyin da suka dace

  19. Ana gangamin cika kwana 40 da kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Iraniyawa da dama suna gudanar da gangami a birane daban-daban na ƙasar don tunawa da cika kwana 40 da kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei kamar yadda gidan talabijin na gwamnatin ƙasar ya ruwaito.

    A cikin hotunan, za a ga ɗimbin magoya bayan gwamnati na nuna alhini a titunan biranen Hamedan da Yazd da Khorramabad da Shiraz da Yasuj da dai sauransu.

    An kashe Ali Khamenei ne a ranar farko ta yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran a ranar 29 ga Maris kuma har yanzu ba a yi jana'izarsa ba a hukumance.

  20. Amurka ta umarci jami'anta su fice daga Najeriya

    Shugaban Amurka Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta umarci jami'anta na diflomasiyya su fice daga Abuja, babban birnin Najeriya, yayin da tsaro ke ''ƙara taɓarɓarewa'' a ƙasar.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce ta umarci ma'aikatan gwamnatin Amurka a ofishin waɗanda aikinsu bai zama wajibi ba, da kuma iyalansu su bar ƙasar.

    Haka kuma gwamnatin Amurkar ta shawarci ƴan ƙasarta da ke so ko kuma suke shirin zuwa Najeriya da su sake shawara, saboda matsalar tsaro - wadda ta haɗa da satar mutane da ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindiga.

    A jiya Laraba ne hukumomin Najeriyar suka fara shari'ar sama da mutum 500 da ake zargin su da hannu a hare-haren ƴan bindiga, da suka yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a musamman a arewacin ƙasar.

Trending Now