Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 21/03/2026
Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Rundunar dakarun juyin juya halin Iran, IGRC ta yi iƙirarin ''kai hari'' sansanonin sojin sama a Kuwait da UAE waɗanda ta ce Amurka da Isra'ila na amfani da su.
Kwamandan rundunar sojin ruwa na IRGC, Alireza Tangsiri ya bayyana a shafinsa na X cewa sun '' yi amfani da makamai masu linzami da jiragen ƙunar baƙin wake marasa matuƙa wajen kai hari sansanonin biyu, Al-Minhad da Ali Al-Salem da wurin ajiye jiragen sama da kuma rumbunan ajiye man fetur na Amurka da Isra'ila''.
Ya yi iƙirarin cewa waɗannan sansanoni su ne ''tushen hare-haren da ake kai wa Iran''.

Asalin hoton, A A Sule
Gwamnan jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, Abdullahi Sule ya ce zai tsaya takarar sanatan Nasarawa ta Arewa a zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito gwamnan na bayyana haka lokacin ziyarar barka da sallah da majalisar zartaswar jihar ta kai masa a gidansa da ke unguwar Gudi da ke ƙaramar hukumar Akwanga.
Gwamna Sule ya ce sarakunan gargajiya da manyan ƴansiyasar Nasarawa ta Arewa ne suka matsa masa da kiraye-kirayen
“La'akari da matsin na nake samu daga jagororinmu, kuma ba na son su ga kamar na ƙi yi musu abin da suke so, na yi alƙawarin tsayawa takarar idan lokacin ya zo'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa a baya ya fara shirin goya wa wani ɗantakarar baya, amma ya sauya tunaninsa bayan da shi mutumin ya shiga cikin jerin masu kiraye-kirayen.
A shekarar 2027 ne Gwamna Sule zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu a matsayin gwamna jihar Nasarawa da aka fara zaɓensa a 2019.
A Najeriya dai galibi bayan gwamnoni sun wa'adin mulki a jihohnsu, sukan nemi kujeran sanata domin shiga majalisar dattawan ƙasar.

Asalin hoton, Reuters
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ruwaito cewa wani makami mai linzami mai ƴaƴa ya lalata wata makarantar renon yara a Rishon Lezion da ke tsakiyar Isra'ila.
Wani tarkacen makamin ya yi mummunan lalata ginin da ke cikin makarantar renon yaran, amma shafe ta kai tsaye ba.
Wasu gungun alburusai sun tarwatse cikin iska bayan an harba su, inda suka watsa ƙananan bama-bamai a kan wani yanki mai faɗi.
Rundunar tsaron cikin gida ta Isra'ila tana gudanar da ayyukan ceto da bincike a wurare da dama da suka shafi yankin da ke tsakiyar Isra'ila.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano wasu makamai masu linzami da suka nufi ƙasar bayan harba su daga Iran.
"Na'urorin tsaronmu na kan aiki domin kakkaɓo barazanar," kamar yadda rundunar sojin Isra'ilar ta wallafa a shafinta na Telegram.
An aike wa ''mutane saƙon gargaɗi'' a yankunan da makaman suka nufa, kamar yadda ta bayyana ba tare da bayyana sunayen wuraren ba.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar juyin-juya halin Iran ta ce ta harbi wani jirgin yaƙin Isra'ila mai suna F-16 a sararin samaniyarta.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, IRNA ya ambato wata sanarwa daga rundunar da ke cewa ta harbo jirgin ne da asubahin yau a tsakiyar ƙasar.
Rundunar ta ce wannan ne jirgin Isra'ila na uku da ta harba tun bayan fara wannan yaƙi, to amma ba ta bayar da bayanai kan sauran biyun ba.
Haka kuma rundunar ba ta bayyana faɗuwar jirgin bayan harbi shin ba.
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta ya fuskanci harin makami mai linzami da aka harba daga ƙasa.
Cikin wata sanarwa da sojojin Isra'ilan suka fitar sun ce ''a lokacin ayyukan rundunar sojin saman Isra'ila, wani makami mai linzami da ka harba daga ƙasa ya yi yunƙurin harbo ɗaya daga jirgin jiragen yaƙinta. To amma harin bai samu nasara ba, kuma babu lahanin da aka yi wa jirgin, sannan aikinmu bai samu tangarɗa ba''.

Asalin hoton, Kano State Gov
Wasu ƴanbindiga sun kai hari gidan sakataren ƙaramar hukumar Kibiya da ke jihar Kano tare da sace shi.
Shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Hon. Sabo Yusuf Usman ya shaida wa BBC cewa lamari ya faru ne ranar Juma'a da daddare a gidan sakataren da ke garin Dinya.
''Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da sakataren ke barci a gidansa'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa lokacin da maharan suka je gidan sun tashi ɗan gidan sakataren da ke kwana a zauren waje, inda suka tilasta masa ƙwanƙwasa kofar gidan, sannan ya faɗa wa mahaifinsa cewa cikinsa na ciwo.
''Hakan kuwa aka yi, bayan ya ƙwanƙwasa mahaifin nasa ya ce wane ne? Sai ya ce shi ne (ɗansa), ya ce me ya faru? Sai ya ce cikinsa ne ke ciwo, nan take mahaifin ya buɗe ƙofa, daga nan maharan suka kama shi tare da ɗan nasa'', a cewar Hon Sabo.
Ya ƙara da cewa tuni dai jamai'an tsaro suka kai taimakon gaggawa, amma kafin zuwansu maharan sun tafi da sakataren bayan sun sako ɗan nasa.
A baya dai ba a san ƙaramar hukumar Kibiya da matsalar tsaro ba, amma an sha samun matsalolin hare-haren ƴanbindiga a ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono da suka yi iyaka da jihar Katsina.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce yana maraba da ''duk wani yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin ƙasar gaba ɗaya''.
Cikin wata hira da kafar yaɗalabana Japan da Kyodo, Mista Araqchi ya ce a ''shirye yake ya saurari'' shawarar da za ta kawo ƙarshen yaƙin
Sai dai ya ce duk da yunƙurin da wasu ƙasashen duniya suka yi na kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya, ''Amurka ba ta nuna alamun dakatar da faɗan ba''.
Mista Araghchi ya bayyana wannan yaƙin a matsayin wanda aka ''ƙaƙaba'', sannan ya ce ba tsagaita wuta Iran ke nema ba, a a tana neman kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya ne''.
BBC ta fahimci cewa Iran ba ta ƙaddamar da harin makamai masu linzami kan sansanin sojin haɗin gwiwar Amurka da Birtaniya na Diego Garcia ba.
An fahimcii cewa harin bai yi nasara ba, kuma ya faru ne kafin Birtaniya ta ayyana faɗaɗa amfani da sansanonin sojin Birtani da Amurka ke yi cikin daren da ya gabata.

Asalin hoton, Sokoto State Gov
Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa na aiki hannu da hannu da ta tarayya domin kawo ƙarshen matsalar tsaron jihar.
Yayin wata ziyarar gaisuwar salla da ya kai wa Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III a fadarsa da ke birnin Sokoto, Ahmad Aliyu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa jami'an tsaro duk taimakon da suka buƙata.
''Gwamnatinmu za ta ci gaba da tallafa wa jami'an tsaron gwamnatin tarayya da ƴan sa kai na jiharmu, kayan aiki da duk abin da suke buƙata domin inganta tsaro a jiharmu'', in ji shi.

Asalin hoton, Sokoto State Gov
Jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar tsaro, inda ƴanbindiga ke kai hare-hare da sace mutane a wasu yankunan jihar.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al'ummar jihar su ci gaba da bai wa gwamnati da jami'an tsaro haɗin kai domin magance matsalar ƴanbindiga da jihar ke fama da su.
“Haka kuma muna buƙatar yi wa jami'an tsaronmu, musamman waɗanda aka tura yankunan da ke fama da matsalar tsaro, addu'ar neman kariya,” in ji shi.
A nasa ɓagare Mai Alfarama Sarkin Musulmin ƙasar ya yaba wa jami'an tsaron da ke aiki a jihar na kare rayuka da dukiyoyin al'umma, inda ya buƙaci su ci gaba da ƙoƙarin da suke yi.

Asalin hoton, Reuters
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) ta ce an sake kai hari kan cibiyar nukiliyarta ta Natanz da ke tsakiyar ƙasar da safiyar yau.
Cikin wata sanarwa da kafofin yaɗa labaran Iran suka wallafa, hukumar ta ce an gudanar da binciken gwajin ƙwararru game da ko gurɓataccen tiririn makamashin ya bazu, to sai dai binciken ya gano cewa hakan bai faru ba.
“Ba a samu bazuwar gurɓataccen makamashin ba daga cibiyar, don haka babu wani hatsari ga mazauna kusa da wurin''.
Hukumar ta kuma yi Allah wadai da harin, tana mai cewa ya ''saɓa wa yarjejeniyar hana bazuwar makaman nukiliya da duniya da sauran dokokin da suka shafi kariya da tsaron nukiliya.''
A baya ma AEOI ta ce an kai hari kan cibiyar da ke Natanz, sannan a ranar 3 ga watan Maris ta ce ba a zamu bazuwar gurɓataccen makamashin ba.
A watan Yunin bara ne Amurka ta jefa bama-bamai kan cibiyoyin nukiliyar Iran uku, da suka haɗa da Natanz da Fordo da kuma Isfahan, inda daga baya Shugaba Trump ya ce hare-haren sun ''wargaza'' shirin nukiliyar Iran.

Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce Iran ta harba makamai biyu masu linzami da ke cin matsakaicin zango kan sansanonin soji na haɗin gwiwar Amurka da Birtaniya a Diego Garcia.
Mujallar Wll Street Journal ta ambato wasu majiyoyi masu yawa na cewa babu ɗaya daga cikin makaman da ya faɗa kan sansanin, da ke tekun Indiya.
Kafar yaɗa labaran CNN ta ambato wani jami'i a Amurka na cewa an harba makaman ne ranar Juma'a da safe a gogon ƙasar.
Nisan tazarar da ke tsaknain Iran zuwa Diego Garcia ya kai kusan kilmita 3,800.
A baya dai tsohon jagoran addinin Iran ya bayar da umarnin cewa kada nisan tazarar da makamai masu linzami ƙasar ya zarta kilomita 2,000.
BBC ta tuntuɓi ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon da ma'aikatar tsaron Birtanita game da harin. Amma Pentagon ta ce babu ''bayanan da za ta iya bayarwa a yanzu''.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayar da rahoton fashewa ta harin bama-bamai a cikin dare, a ciki, da kusa da babban birnin kasar, Tehran, da kuma birnin Isfahan.
Can kuma a Isra'ila, tarkacen wani makami mai linzami sun faɗa tsohon birnin Kudus, dan taƙi kaɗan daga, wasu daga cikin wuraren ibadar addini da suka fi muhimmanci a duniya.
Sai dai Isra'ila ta ce tarkacen wani ɓangare ne na makamai masu linzami da garkuwarta ta tare.
Ba a bayar da rahoton rasuwa ko jikkatar wani ba a sanadiyyar harin.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ɗage takunkumin da ta sanya wa man Iran - wanda tuni yake cikin jiragen ruwa a teku - na wucin-gadi.
Ta yi hakan ne domin rage illar da yaƙin ke haifar wa a kasuwar makamashi.
Matakin na tsawon kwana 30 ya shafi man da aka riga aka loda ne a jiragen ruwa, kafin, ranar Juma'a 20 ga watan Maris din nan.
Sakataren Baitul- Malin Amurka, Scott Bessent, ya ce hakan zai sa a samu gangar mai miliyan 140 a kasuwar duniya.
A ba ya ma Amurkar, ta dage takunkumin da ta sanya a kan man Rasha wanda tuni yake teku.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Donal Trump ya ce Amurka na tunanin kammala yaƙin da take yi a Iran.
Cikin wata da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce Amurka na dab da cimma manufarta ta yaƙin.
Bayanai na nuna cewa wannan saƙo ya ci karo da rahotannin kafofin yaɗa labaran Amurka.
Kafin wannan saƙon nasa, Trump faɗa wa manema labarai cewa, ba ya son dakatar da buɗe wuta.
Waɗannan sakonni masu karo da juna, sun zo ne, yayin da kafar yada labarai, ta CBS, ta bayar da rahoton cewa, jami'an sojin Amurka na nazarin shirin tura dakarun kasa cikin Iran.
Kafar ta tattauna da majiyoyi da dama inda ta ce shirin ya haɗa da yadda Amurka za ta yi kan batun tsare sojojin Iran, idan suka shiga hannu.
A sakonsa na baya-bayan a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce, dole ne sai dai wasu ƙasashe da suke amfani da mashigar Hormuz su tsare ta, amma Amurka ba ta cikinsu.