Ku San Malamanku tare da Sayyada Ummuhani Ibrahim Nyass
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
'Yar Shehi Ibrahim Nyass, Sayyada Ummuhani ta ce tana jin takaicin yadda wasu ke wuce gona da iri a da'awar soyayyar mahaifinta, wanda jigo ne a darikar Tijjaniya a duniya.
A cikin shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa, Sayyada Ummuhani ta ce hakan wasu lokutan har kuka yake saka ta, ta kuma kasa barci, musamman idan ta ji wasu na kwatanta mahaifin nata da matsayin Ubangiji mai girma.
Ta ce kwata-kwata wannan ba ya cikin koyarwar mahifinta, kamar yadda ya saba da tsarin Musulunci.
"Sheikh Ibrahim Nyass masoyin Annnbi SAW, kuma ya koya wa mutane bin sunna da kiyaye dokokin Allah.
"Shehu Ibrahim Nyass bai taba cewa shi Allah ne ba, shi ya bi sunnar Ma'aiki ne, saboda haka idan ana fadar irin wannan yakan sa ni kuka har ya hana ni barci," a cewarta.
Sayyada Ummuhani haifaffiyar birnin Landan ce a Birtaniya, ta koma kasar Senegal tana 'yar shekara shida, bayan rasuwar mahaifinta a shekarar 1975 sai ta koma birnin Okene na jihar Kogin Najeriya.
A yanzu kuma mazauniyar birnin Kano ce sakamakon aure da ya kai ta can tun shekarar 1980.
Tuni mijinta ya rasu ya bar ta da 'ya'ya tara da duk suke Kanon.
Sayyada Ummuhani mai shekara 58, tana karantar da Al-Kur'ani tun bayan da ta yi aure har zuwa yanzu.