BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Gwamnatin Kano ta gargaɗi masu shirin aibata Kwankwaso
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Alamu biyar da ke nuna cewa ɗan'adam na samun ci gaba a doron ƙasa
A cikin wannan muƙala, mun zaƙulo wasu abubuwa biyar, da ke tuna mana irin nasarorin da muka samu cikin gomman shekaru a fannoni daban-daban
Abin da APC ta ce kan matsayin Wike a jihar Rivers
Da alama jam'iyyar APC da gwamnatinta a Najeriya, sun fara juyawa ministan Abuja, babban birnin tarayyar kasar, Nyesom Wike, baya
Me ya sa ƙasashen Larabawa ke ɗari-ɗari kan yiwuwar rushewar gwamnatin Iran?
Yiwuwar ɗaukar matakin soji na Amurka kan Iran ya kasance wani muhimmin batu da ke matuƙar kawo damuwa a ayyukan diflomasiyyan ƙasashen larabawa, musamman tsakanin ƙasashen da ke ƙungiyar ƙasashen yankin Gulf.
Yadda 'Isra'ila ke ƙara cin wasu yankuna a Gaza' duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
Isra'ila ta ƙara matsar da shigenta - da aka amince da ta tsaya a lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta a matsayin wurin da take iko da shi - zuwa cikin Gaza, wani abu da ya ƙara haifar da fargaba tsakanin Falasɗinawa.
Wani abincin ƴan China da ke sanya mutane gane-gane
Marasa lafiyar kan bayyana wasu alamomin da ba a saba gani ba: ganin wasu mitsi-mitsin mutane da ke taruwa a ƙarƙashin ƙofofi, ko suke hawa bango ko suke mannuwa a jikin kujeru.
Ƴan majalisar dokokin jihar Kano 22 sun fice daga NNPP
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Kun san abin da ya sa ɗan'adam ke yin kuka?
Me ya sa ɗan'adam ke yin kuka, kuma me ya sa wasu ke zubar da hawaye saboda tausayi? Wannan na cikin abubuwan da ba a gama sani ba har yanzu.
Manyan dokokin zaɓen da ake son yi wa gyara a Najeriya kafin 2027
Yanzu haka wannan doka tana a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ake nazari da muhawara a kai da nufin gyara sassan da aka gano cewa suna da matsala ta la'akari da abubuwan da suka faru a lokacin babban zaɓen Najeriya na 2023.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 25 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 25 Janairu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 25 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 24 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
Chelsea na son Mbaye, Arsenal sai ta biya £80m kafin karɓo Alvarez
Tottenham da Liverpool na tattaunawa kan cinikin Andy Robertson, Bournemouth na dab da ɗauko Christos Mandas a matsayin aro, yayin da Arsenal ke shirin lale fam miliyan 80 kan Julian Alvarez.
Arsenal na son Alvarez, Mece ce makomar Alexander-Arnold?
Ɗanwasan baya na Real Madrid Trent Alexander-Arnold ba a shaida masa ya nemi wata ƙungiya ba a bazara, Arsenal na harin ɗanwasan gaba na Atletico Madrid Julian Alvarez, yayin da Liverpool ke shirin hamayya da Bayern Munich kan ɗanwasan RB Leipzig Yan Diomande.
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da suka fi samun kuɗi a duniya
Liverpool ta zama ƙungiyar Premier da ta fi samun kuɗi karo na farko, a cewar kamfanin haraji na Deloitte.
KAI TSAYE, Ƙwallo ɗaya Haaland ya ci a wasa takwas baya, ko yana bukatar hutu?
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 18 zuwa 30 ga Janairun 2026
Kungiyoyin Saudiyya na son Salah da Vinicius, Man U na shirin tattaunawa da Mainoo
Mohamed Salah da Vinicius Jr, sun kasance manyan 'yan wasa biyu da kungiyoyin Saudiyya ke zawarcinsu a bana.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Ko yawan aske gashin al'aura na ƙara haɗarin kamuwa da cutar sanyin gaba?
Wannan sakamakon binciken ya saɓa da wasu binciken da aka yi a baya da suka yi gargaɗin cewa cire gashin al'aura gaba ɗaya na iya haifar da yanka a kan fata, wanda hakan zai bai wa cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i (STIs) damar shiga jiki .
Mece ce makomar NNPP bayan ficewar Gwamna Abba Kabir?
Ana tunanin gwamnan zai tafi da wasu jiga-jigan gwamnatin, waɗanda ƙusoshi ne a tafiyar Kwankwasiyyar.
Mece ce makomar jagoran addinin Iran?
Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei - wanda ke ɓoye a wani wuri na sirri - a ƴan kwanakinnan yana cike da sanin cewa ana sanya idanu a kansa, fiye da lokutan da suka gabata a baya.
Martanin da Harry ya mayar wa Trump kan caccakar NATO
Yarima Harry ya mayar da martani ne kan kalaman Trump cewa ba shi da tabbacin ko sojojin kawancen za su taimaka wa Amurka idan bukatar hakan ta taso.
Abin da ya sa na fice daga jam'iyyar NNPP - Abba Kabir
Ficewar na ƙunshe ne a cikin a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma'a.
Amurka na son Najeriya ta ƙara jajircewa wajen kare Kiristoci
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Waɗanne matakai ya kamata ka ɗauka idan maƙwabcinka na buƙatar taimako?
Galibi a rayuwa irin ta yanzu, ana samun maƙwabta suna zaman doya da man ja, inda har za ka ga maƙwabci yana cikin damuwa amma a nuna halin ko-in-kula.
Abin da ya sa na koma aji biyu a jami'a - Sarki Sanusi II
Ba a Najeriya kawai ba, Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne Khalifan ɗariƙar Tijjaniya a ƙasar na da ɗimbin tasiri a ƙasashe maƙwafta, musamman na yammacin nahiyar Afirka.
'Jini faca-faca a jikina' - matar da ta kuɓuce daga hannun ƴan bindiga a Kajuru
An ƙiyasta cewa har yanzu akwai kimanin mutum 160 a hannun ƴan bindiga waɗanda suka afka wa majami'u uku ranar Lahadi a wani ƙauye da ke jihar Kaduna.
Da gangan majalisa ke jan ƙafa kan gyaran dokar zaɓe - Atiku
Atiku Abubakar ya yi gargadi cewa ci gaba da jinkirin kammala gyaran dokar zaɓen zai iya shafar ingancin zaɓen 2027.
Na'urar ɗakile hare-haren makamai masu linzami da Trump zai ƙaddamar
Shugaba Trump na son ƙaddamar da tsarin kariyar makamai masu linzami na zamani na biliyoyin daloli don kare ɗaukacin Amurka. Amma ta yaya zai yi aiki? nawa ne za a kashe a kansa, kuma menene wasu ƙasashe ke cewa a kai?
Abubuwan da suka kamata ka yi lokacin tashi daga bacci
Abu na biyu da likitar ta ce yana da muhimmanci bayan tashi daga bacci shi ne shan ruwan ɗumi.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






































































