Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyi 5 da za ku rage wa yaranku kallon waya
- Marubuci, Emer Moreau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
- Lokacin karatu: Minti 3
Idan kai magidanci ne, ka amince da hukuncin da wata kotu a Amurka ta yanke cewa kamfanin Meta da Google suna ƙirƙiro shafukan sada zumunta da kuma saka musu abubuwa da suka yi wa lafiyar ƙwakwalwar wata budurwa lahani.
Lauyoyin matashiyar, wadda aka fi sani da Kaley, sun kalubalanci cewa an tsara wasu abubuwa a Instagram don janyo hankalin.
Duk da cewa an yi maraba cewa hukuncin kotun zai kawo sauyi ga shafukan sada zumunta, sai dai hakan ba wani abu bane ga iyaye a faɗin duniya da ke son rage yawan lokaci da yaransu ke shafewa a shafukan sada zumunta.
Mun tambayi wasu ƙwararru kan ɓangaren iyali kan shawarwari da za su ba da na yadda za a karɓe wayoyi daga hannun yara - ko da na karamin lokaci ne.
1. Ka fara kaɗan-kaɗan kuma da gaske
Iyaye da dama da suka riga suka ba yaransu wayoyi, za su yi tunanin cewa ko karɓe su shi ne abin da ya fi dacewa.
Sai dai hakan ba zai kasance zaɓin da ya dace ba, in ji ƙwararriya kan halayyar yara Dakta Jane Gilmor.
"Sauya ɗabi'a abu ne mai wuya," in ji ta.
Maimakon haka, ta ba da shawarar aiwatar da sauye-sauye da suka kamata, ba cikin fushi ba na yawan kallon waya da yaro ke yi. "Ƙwakwalwa nitsattsiya ta fi tuna abu mai kyau."
Hanya ta farko ta fara rage yawan kallon waya ita ce tsara wani waje a gida, watakila wuri na musamman.
"Ka samu wuri ɗaya na saka cajoji... wadda idan wayar ta tafi, za ta wuce kai-tsaye zuwa wurin caji daga nan shikenan."
2. Yin aiki tare
Yaran da suka manyanta za su iya cin alfanun tattaunawa da su kan yawan kallon waya, maimakon saka musu dokoki, a cewar masaniya kan halayyar yara, Dakta Maryhan Baker.
Magana da yara ta yadda ya dace na yanda suke amfani da shafukan sada zumunta zai taimaka, in ji ta, kamar faɗa musu:
"Na fahimta cewa ta nan kake haɗuwa da abokai. Na kuma san yanda za ka ji idan ba ka hau shafukan sada zumunta ba. Na fahimta matuka.
"Don haka mu tattauna kan yanda za mu iya samar da lokaci a rana, kuma ranar da ba ka riƙe waya ba."
Wata kwararriya kan harkar zamantakewar iyali Olivia Edwards ta ƙara da cewa kulla alaƙa mai ƙarfi da yaronka zai yi sauki wajen jan ra'ayinsu su rage kallon waya.
"Ya kamata mu gina alaƙa mai ƙarfi da ƴaƴanmu saboda hakan shi zai ba mu haɗin kai da kuma aiki tare."
Wannan zai kunshi nuna sha'awa kan irin abubuwan da yaronka ke kallo a shafukan sada zumunta.
3. Amfani da waya wajen koyo
Iyaye da dama na jin cewa ba sa iya tafiya da zamani kan irin sauye-sauyen da ake samu a shafukan sada zumunta.
Sai dai akwai damarmaki ga yara da kuma manya wajen koyo tsakaninsu ta hanyar tattaunawa kan yawan kallon waya.
Olivia ta ce: "Za ka iya faɗan abu kamar haka: 'Ta yaya kake tunanin shafukan sada zumunta ke aiki?
Ta yaya kake tunanin shafukan ke aiki don janyo hankalin mutane? Shin ka san cewa suna samun kuɗi kan irin yawan lokaci da mutane ke shafe wa a kansu?"
Jane ta kuma ce iyaye kan koyar da yaransu darusa kan sanin hanyoyin intanet.
"Akwai irin abubuwa da za ka kalla sannan ka ce, 'Shin wannan gaskiya ne? Ta yaya zan gane idan hakan gaskiya ne ko kuma karya?"
4. Ɗabi'u masu kyau
Ba wani ɓoyayyen abu bane cewa yara na kwaikwayon iyayensu, don haka ƙarfafa wa yara rage yawan kallon waya ya kamata ya fara ne daga iyayen.
Wayoyin hannu sun samarwa mutane daga kowane na'ui na shekaru nishaɗi, sai dai Jane ta ce manya da yara za su ci alfanu idan suka yi amfani da wayoyin yanda ya dace.
"Kasancewa da waya, yana saka mu kallon yadda faɗin duniya take. Kuma hakan yana ba mu damar tunanin abin da ya faru a baya, da tunanin ya gaba za ta kasance.
"Don haka idan yaranka na ƙorafin cewa babu abin yi, kawai suna kallon wani wuri ne – kuma hakan abu ne mai kyau saboda ta haka za su iya tunanin fara rage kallon waya."
5. Kada ku yi fargaba
Zama uba ko mahaifiya bai taɓa zama abin sauki ba, amma girmar da yara a lokacin da wayoyin salula suka yawaita, abin damuwa ne.
Dakta Tony Sampson, malami a jami'ar Essex, ya ce kada lamarin ya saka iyaye firgita ko shiga ruɗani.
"Mun karanta hanyoyi da dama na yadda kafofin sada zumunta ke janyo hankali," in ji shi.
"Ba sa janyo hankali kaɗai. Suna saka mutane mu'amala da wasu harkoki musamman tallace-tallace.
"Amfani da fasahohin zamani yadda ya dace kan inganta ilimin ƙirkire-ƙirkire, sanin abubuwa da kuma koyo."
Are you a parent who is concerned about screen time? Have you taken steps to address the issue with your children?