Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammad Ghalibaf: Mutumin da ke jagorantar tattaunawar zaman lafiya da Amurka
- Marubuci, Pouria Mahrouyan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
- Lokacin karatu: Minti 4
Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf na ƙara taka muhimmiyar rawa kuma an ɗora masa alhakin tattaunawa da Amurka a daidai lokacin da ake ci gaba da yaƙi.
An cire sunan Ghalibaf tare da ministan harkokin wajen Iran Abbas Aragchi daga jerin waɗanda Isra'ila ke son kashewa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami'in Pakistan na faɗa.
"Isra'ila ta shirya afka musu da kuma kashe su, mun faɗa wa Amurka cewa muddin su ma aka kashe su to babu wanda za a tattauna da shi, don haka Amurka ta buƙaci Isra'ila ta janye kudurinta," in ji jami'in. Pakistan na ɗahya daga cikin masu shiga tsakanin Iran da Amurka.
Ghalibaf ya nemi takarar shugaban ƙasa sau da dama a baya amma bai samu nasara ba. Sai dai yayin da aka kashe manyan jagororin Iran a yaƙin da ake yi, alaƙarsa da rundunar juyin juya-hali ta IRCG, ƙwarewarsa a fannoni da dama na aikin gwamnati da kuma kallonsa da ake yi a matsayin mai tsaurin ra'ayi, zai iya ƙara masa ƙarfin iko.
'Ina alfaharin amfani da sanda'
An haifi Ghalibaf a cikin wani iyali mai akin gwamnati da ke birnin Torghabeh a arewa masom gabashin Iran, a cewar gidan talabijin na Al-Alam mallakin gwamnatin Tehran.
Garin mahaifarsa na kusa da Mashhad, inda sanannun jagororin rundunar IRCG suka yi rayuwa.
Ya fara zuwa ɗaukar darussa daga manyan malamai yana da shekara 16 - ciki har da Ali Khamenei, a manyan masallatai a birnin Mashhad.
Jim kaɗan bayan juyin juya hali na 1979, Ghalibaf ya yi faɗa a lokacin yaƙi da Iraki, inda ya shiga rundunar juyin juya-hali a shekaru 20. Bayan shekaru biyu, ya zama kwamandan ɗaya daga cikin rundunoni - mukami da ya rike har sai bayan kawo karshen yaƙi a 1988.
Ghalibaf ya yi aure a shekarar da ya zama kwamandan IRGC, kuma jagoran addini Ruhollah Khomenei ne ya jagoranci bikin, a cewar gidan talabijin na Al-Alam. Yana da ƴaƴa uku.
Ya ci gaba da samun ɗaukaka da kuma karɓuwa bayan yaƙin inda ya zama kwamandan sojojin sama na rundunar IRGC a 1997.
A watan Yulin 1999, zanga-zangar ɗalibai ta mamaye Jamhuriyar Musulunci, wanda ya fara sakamakon rufe wata gidan jarida.
Hukumomi sun yi wa masu zanga-zangar dirar miƙiya, abin da ya janyo mutuwar da dama, kuma ana yaƙinin cewa akwai hannun Ghalibaf a ciki.
"Akwai hoto a kan babura kusan 1,000 a yanzu ina riƙe da sanda... Duk inda ya kamata a fito a rike sanda a tituna, mun yi hakan kuma muna alfahari da shi," kamar yadda ya faɗa a cikin wani bidiyo da aka fitar.
Bayan zanga-zangar, kwamandojin IRGC 24 sun rubuta wasika zuwa Mohammed Khatami wanda shi ne shugaban Iran a lokacin, inda suka yi barazanar cewa za su kawo ɗauki.
Ghalibaf na cikin kwamandoji biyu da suka tsara rubuta wasikar da kuma saka hannu.
Mutane da dama na ganin cewa wannan wasika ta nuna yunkurin IRGC na shiga harkokin siyasa - wanda abu ne kuma da ya ƙaru tun bayan lokacin.
Daga shugaban ƴansanda zuwa Magajin birnin Tehran
Shekara ɗaya bayan zangar-zangar ɗalibai, an naɗa Ghalibaf a matsayin shugaban ƴansanda yana shekara 39.
Lokacin jagorancinsa na shekara biyar, ya kirkiro wani layin waya na gaggawa na ƙasa baki ɗaya, wanda aka tsara don masu shigar da ƙorafi kan ƴansanda.
Ya kuma samarwa ƴansanda da ababen hawa na zamani daga ƙasar waje, wanda yana cikin abubuwan da ya cimma a ofis, sai dai masu suka sun ce kuɗin da aka sayi motocin ya yi tsada.
A 2005, Ghalibaf ya yi murabus a matsayin shugaban ƴansanda inda ya yi takarar shugaban ƙasa.
Bayan shan kaye, an zaɓe shi a matsayin magajin birnin Tehran. Ya riƙe matsayin har na tsawon shekara 12, kuma shi ne ya fi daɗewa a matsayin.
An yaba masa bisa kokari wajen faɗaɗa tashar jirgin ƙasa da kuma inganta harkokin sufuri kamar babbar hanyar Sadr a birnin Tehran da ke yawan samun cunkoso.
Sai dai Ghalibaf ya fuskanci tuhuma a 2016, inda hukumar birnin ta zarge shi da sayar da ɗaruruwan kayayyaki ga jami'ai da kuma jami'an tsaro a farashi mai rahusa - kusan ragin kashi 50 da farashin kasuwa.
Watanni kafin ya bar ofis, wani daɗaɗɗen gini mai hawa 17 ya rufta a Iran bayan kamawa da wuta, inda lamarin ya hallaka masu kashe gobara aƙalla 20.
Batun ya nuna yadda aka yi watsi da harkoki a birnin karkashin jagorancin Ghalibaf.
Sai dai, lamarin bai saka an kori Ghalibaf ba ko kuma tsige shi, kuma ya tsallake duka zarge-zargen.
A 2020, ya lashe kujerar zama ɗan majalisa inda ya zama kakakin majalisar ƙasar.
Shan kaye a takara da zama kakakin majalisa
Ghalibaf ya sha saka idonsa a kan kujerar shugaban ƙasa, sai dai bai yi nasara ba a dukkan takara huɗu da ya yi - a 2005, 2013, 2017 da kuma 2024.
A takara ta farko, ya nanata ƙwarewar da yake da shi a fannin aikin soja, sai dai daga baya ya sauya akala ta hanyar bayyana matsayinsa a siyasa da kuma matukin jirgin sama.
Ya kuma ayyana kansa a matsayin "shugban ƴan jihadi".
A zaɓen shugaban ƙasa na 2024, wasu gungun masu ra'ayi sun yi adawa da takararsa inda suka nemi ya janye aniyarsa.