Bahaushen da ya doke Turawa 7 don zama kansila a Faransa

Lokacin karatu: Minti 3

Nan gaba a yau ne ake sa ran rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin da suka yi nasara a zaɓukan ƙananan hukumomin ƙasar Faransa da aka yi a kwanan baya.

Sakamakon zaɓen dai ya jan hankalin ƴan Afrika sosai ganin yadda rahotanni suka ce an samu baƙaƙen fata da yawa da suka lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomin da kansiloli fiye da kowane lokaci a baya.

Daga cikin waɗanda aka zaɓar har da Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Sirajo Jankado, wanda ya lashe zaɓen kansila a yankin birnin Paris.

A tattaunawarsa da BBC, Alhaji Sirajo Jankado ya bayyana yadda ya ji da samun nasara a zaɓen na Faransa.

Faransa na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Turai da baƙaƙen fata ke rayuwa a cikinsu.

Yadda baƙaƙen fata ke shiga takara a Faransa

Sarkin Hausawan na Turai ya ce an samu ƙaruwar baƙaƙen fata da suka shiga takara a zaɓukan ƙananan hukukomin na Faransa da aka gudanar ranar 15 ga watan Maris da muke ciki.

''Akwai ƴan Afirka da dama da suka tsaya takara a wannan karo, kuma da dama cikinsu sun samu nasara'', kamar yadda ya bayyana.

Alhaji Jankado ya ƙara da cewa a yankin Faris an samu ƙananan hukumomi 12 da baƙaƙen fata suka lashe zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi, ciki har da yankin Santeny, birnin na biyu mafi girma a yankin Faris.

''Kansiloli kuwa sun fi a ƙirga, sunan nan babu adadi, saboda ko a kudancin Faris, yankin da Turawa suka fi yawa nan bai hana baƙaƙen fata mu samu kansiloli da yawa ba'', in ji shi.

'Yadda na tsaya takara har na lashe zaɓe'

Sarkin Hausawan na Turai ya ce ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Palaiseau ne ya nemi ya shiga takarar kansila a mazaɓar da yake zaune.

''Shi da kansa ya neme ni, sannan ya ba ni gunduma ya ce in tsaya takara a cikinta, hakan kuma aka yi har na samu nasara a wannan zaɓe'', in ji shi.

Ya ce ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar kan ziyarci shugabannin al'umma haka su ma sukan ziyarci.

''Musamman a lokacin azumi mukan gayyace shi shan ruwa a masallacinmu, haka shi ma yakan gayyace mu shan ruwa a gidansa, to da haka muka saba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Alhaji Jankaɗo ya ce ya fatata takarar ne da Turawa bakwai, inda kuma ya samu nasarar doke su.

''Na lashe zaɓen ne da kashi 51 cikin 100 na duka ƙuri'in da ka kaɗa a zaɓen kansilar gundumar tamu'', in ji shi.

Mene ne aikin kansila a Faransa?

Sabon kansilan na gundumar Filoi a ƙaramar hukumar Palaiseau ta ce matsayin kansila, muhimmin muƙami ne mai alaƙa kai tsaye da talakawa.

''Shi ne matsayin da kai kai-tsaye talaka ke da alaƙa da gwamnatin ƙasar Faransa'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya ci gaba da da cewa duk abin da talaka ke buƙata daga ɓangaren gwamnati, akmar mallakar gida da buƙatar sanya yaro a makaranta dole sai an bi ta kansiloli.

''Akwai ayyukan tituna da samar da tsaron unguwanni, ko haihuwa aka yi maka dole sai ka bi ta kansiloli domin samun takardar haihuwa'', in ji shi.

'Abin da za mu bai wa fifiko bayan kama aiki'

Alhaji Jankaɗo ya ce da zarar sun kama aiki, babban abin da ke gabansa shi ne yin muhawara kan kasafin kudin ƙaramar hukumar, domin amimcewa da shi.

''Daga nan kuma sai mu mayar da hankali kan ƙorafe-korafen da muka ji daga bakunan al'umma lokacin da muke yaƙin neman zaɓe, domin magance musu'', in ji shi.

Sannan ya ce zai riƙa janyo hanakali matasa baƙaƙen fata, domin su riƙa shiga harkokin gwmanati a Faransa.

''Abin da na lura shi ne matasanmu daga Afirka suna ɗari-ɗarin shiga harkokin siyasa a nan Turai, to zan yi amfani da wannan dama wajen janyo domin wayar musu da kai su riƙa shiga'', in ji shi.

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata a riƙa damawa a ƴan Afirka a siyasar Turai.

Tsawon wa'adin shugaban ƙaramar hukuma da kansila a Faransa dai shekara shida ne.