Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da likitoci da masana suka gano kan 'gicciye Yesu'
- Marubuci, Edison Veiga
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brazil
- Lokacin karatu: Minti 6
Wasu al'umma sun yi imanin cewa Yesu, wato Annabi Isah ya rayu shekara 2000 da suka gabata a yankin da a ayanzu ake kira Isra'ila.
Ana masa kallon Bayahude wanda ya fanɗare wa hukumomi tare da wasu mabiyansa, kuma hakan ya ɓata wa jagororin daular Romawa rai.
Hakan ne ya sanya suka azabtar da shi, sannan suka kashe shi a ranar Easter.
Amfani da tsarin gicciye wajen kashe mutane a wancan lokacin abu ne da ya zama ruwan dare.
Bayan shuɗewar Yesu, sai wasu mabiyansa suka rungumi aikin yaɗa koyarwarsa, kuma daga lokacin ne aka samu labarai daban-daban game da shi.
Bayanan da aka samu daga farko-farko sun fito ne daga wani babban marubuci, wanda ke gaba-gaba wajen ɗabbaƙa Kiristanci, kuma shi ne wanda ya rubuta sassa daban-daban na littafin injila.
Wannan mutumi shi ne ake kira Paul, wanda aka haifa a garin Tarsus da ke kudancin Turkiyya a yanzu.
Cikin shekaru 20 bayan shuɗewar Yesu, Paul ya rubuta surori bakwai na littafin injila, waɗanda ake kira 'Seven letters', da ake amfani da su har zuwa yau ɗinnan.
Wani masani kuma farfesan tarihi Andre Leonardo Chevitarese ya ce "surori bakwai ba su yi bayani dalla-dalla kan tarihin Yesu ba, sun yi magana ne kan addininsa".
"Tarihin Yesu da muka sani shi ne an kashe shi ne saboda siyasa. Domin a wancan lokacin shugabanni ba sa rarrabewa tsakanin siyasa da addini," in ji Chevitarese.
"Ba iya rarrabewa kan cewa ayyukan Yesu na siyasa ba ne ko na addini. Wannan ya taka rawa sosai wajen fahimtar Yesu a lokacin da yake raye da kuma bayan shuɗewarsa," in ji shi.
Azabar gicciye
Zartar da hukuncin kisa ta amfani da gicciyewa abu ne da ya zama ruwan dare a lokacin.
"Gicciyewa wani nau'i ne na hukunci mai tsanani, wanda Romawa ke zartarwa kan bayi da kuma waɗanda ba ƴan asalin daular Romawa ba ne tun a shekarun 217 kafin zuwan annabi Isa," in ji masanin siyasa da tarihi Gerardo Ferrara, wanda ya ƙware a harkokin Gabas ta Tsakiya.
"Hukunci ne na rashin imani da tozartarwa. Ba su aiwatar da irin wannan hukuncin kan Romawa. Akan lakaɗa wa waɗanda za a zartar wa wannan hukunci duka daidai da darajarsu a cikin al'umma," in ji shi.
Ba Romawa ne suka ƙirƙiro gicciye ba, amma abu ne da ya yaɗu a daular. Amma hukunci ne wanda ake amfani da shi sosai a yankin da a yanzu ake kira Isra'ila," in ji Chevitarese.
Ya ƙara da cewa "kimanin shekara 40 bayan shuɗewar Yesu, sun ci birnin Qudus da yaƙi, inda aka gicciye dubban Yahudawa."
Koyarwar littafin Injila ya nuna yadda Yesu ya sha wahala gabanin gicciye shi. Littafin ya nuna cewa an riƙa kai Yesu wurare daban-daban gabanin gicciye shi.
Sai dai Chevitarese ya ce a tarihince akwai alamun cewa ba haka abin ya faru ba, domin daga bayanai, Yesu ya rasu ne kafin hutun Yahudawa na tunawa da lokacin da suka yi hijira daga Masar domin guje wa bauta.
Masanin tarihin ya ce "Easter hutu ne na hukuma. Rana ce da ake tunawa da ƴancin Yahudawa a Masar."
"Saboda haka ta yaya za a ce an ɗauki wani Bayahude an zagaya da shi cikin gari, cike maƙil da Yahudawa sannan kuma a gicciye shi?"
"In da wannan ne abin da ya faru, da mutane sun yi bore".
Ya ƙara da cewa saboda haka "nan take aka kama Yesu aka gicciye shi".
Chevitarese ya ce bayanin da ake yaɗawa kan yadda aka kama da kuma gicciye Yesu daga safiyar ranar Alhamis zuwa safiyar Juma'a ba ya da tushe a tarihi.
Kwanaki kaɗan kafin nan ne Yesu ya shiga birnin Qudus. A lokacin ne hukumomin suka kama Yesu, tun da bai cika shiga birane ba.
Yadda hukuma ta kama Yesu
"Abin da ya faru shi ne, Yesu ya kasance yana koyar da abubuwan da suka shafi siyasa da addini da tattalin arziƙi da kuma zamantakewa. Babu wani takamaiman layi tsakanin inda yake maganar siyasa ko addini ko zamantakewa, dukkanin abubuwan a cakuɗe suke," in ji Chevitarese.
Hukumomin Romawa sun ta lura da zirga-zirgar Yesu, sai suka ga cewa daidai lokacin da zai shiga birnin Jerusalem, shi ne lokacin da ya fi dacewa su kama shi.
"Ranar Easter, lokacin da birnin ya cika maƙil da Yahudawa waɗanda suka fito daga yankuna daban-daban, sai suka ga kamar Yesu na ƙoƙarin haifar da ruɗani sanadiyyar wa'azinsa.
"Daga nan ne suka ga cewa ya kamata su kama shi kuma su gicciye shi ba tare da ɓata lokaci ba," a cewar masanin.
"Dukkanin masu da'awa na kiristanci sun amince cewa an kashe Yesu ne a ranar Juma'a, lokacin da ake bikin Easter," in ji Ferrara.
Malamin kirista, mawallafi kuma masanin injila Giuseppe Ricciotti, ɗan ƙasar Italiya ya ce bayanan da ya tattara sun nuna cewa akwai kyautata zaton cewa an gicciye Yesu ne a kwanan wata da ya yi daidai da 7 ga watan Afrilu.
Abin da ya sa Yesu ya rasu
Farfesa Fredrick Thomas Zugibe na Jami'ar Columbia kuma tsohon shugaban sashen ilimin jini a Cibiyar nazarin dokokin likitanci da ke birnin New York ya ce ya gudanar da bincike a farkon shekarun 2000 ta hanyar amfani da wasu mutane, domin gano halin da mutum ke shiga idan aka gicciye shi.
An wallafa rahoton binciken a wani littafi mai taken Binciken ƙwaƙwaf kan Gicciye Yesu (Cruxification of Jesus: A Forensic Inquiry)
Rahoton Dr Zugibe ya ce Yesu ya ɗauki katako ɗaya ne cikin katako biyu da aka haɗa aka gicciye shi.
Ya ce guntun katakon, wanda ake gittawa shi ne Yesu ya ɗauka, wanda ke da nauyin kilo 22.
Katakon biyu idan aka haɗa su za su kai nauyin kilo 80 zuwa 90, saboda haka ba zai yiwu mutum ya ɗauke su gaba ɗaya ba ya yi irin tafiyar da aka ce Yesu ya yi.
An bayyana cewa Yesu ya yi tafiya mai tsawon kimanin kilomita 8.
Dr Zugibe ya ce an yi amfani da wata ƙusa mai tsayin santimita 12.5 wajen buga hannun Yesu a jikin katako, inda ya ce hakan zai sanya ƙusar ta lalata wasu muhimman jijiyoyi tare da haifar da tsananin raɗaɗi.
Yayin da Yesu ke kan katakon an kuma buga ƙusoshi a ƙafarsa aka haɗa da katakon.
"Tsawon wane lokaci mutumin da ke cikin wanna hali zai ɗauka kafin ya rasu? Mutum zai mutu ne bayan ya samu jijjiga. Hakan zai sanya tsokar jikin mutum ta saki sannan za su samu rashin zagayaway iska a jiki," in ji Cevitares.
Ferrara ya ce Yesu ya rasu ne sanadiyyar bugawar zuciya sakamakon azabar da ya sha.
A binciken da ya yi, wani masani mai suna Joukibe ya ce abu uku ne za su iya sanadin mutuwar Yesu: rashin zagayawar iska a cikin jini, ko bugawar zuciya da kuma tsananin rashin jini.
Bincikensa ya haƙiƙance cewa Yesu ya samu bugun zuciya ne sanadiyyar tsiyayewar jini da ruwan jiki a dalilin azabar da aka masa da kuma kakkafe shi a jikin katako.
Saboda haka akwai yiwuwar jininsa ne ya tsiyaye har ya mutu.
Caviteres ya ce "lokacin da za a ɗauka kafin mutumin da aka gicciye ya rasu ya danganta ne ga halin da yake ciki kafin a kafe shi a katako. Idan an yi wa mutum azaba sosai kafin a kafe shi, to zai iya mutuwa cikin sauri.".
"Akwai yiwuwar Yesu ya kwashe wasu ƴan awoyi kafin ya rasu. Wataƙila zai kai kamar awa biyu sanadiyyar jinin da ya rasa," in ji Ferrara.
Ko an binne Yesu?
Cevitares ya ce abin da tarihi ya nuna kan gicciye Yesu ya sha bamban da abin da ke cikin injila. Ya ce an gicciye shi ne a wuri mai nisa, inda babu mutane.
Ya ce yana iya yiwuwa an yi hakan ne domin guje wa boren al'umma, ba kamar yadda aka samu labari a litattafan addini ba.
Ya ce "ba a binne mutanen da aka gicciye. Tsuntaye ne ke zuwa su cinye idanunsu da caccake fuskokinsu."
"Ana barin waɗanda aka gicciye a kan katako har tsawon kwana huɗu. Naman jikinsu zai fara ruɓewa yana zuba ƙasa."
"Daga abin da tarihi ya nuna, ba a binne mutanen da aka gicciye, amma litattafan addini sun ce an binne Yesu sannan kuma ya tashi," in ji masanin.