Wane mai tsaron raga ne ya fi tashe a wannan lokaci?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Marissa Thomas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
- Lokacin karatu: Minti 5
Masu tsaron raga sun haska a wasannin gasar zakarun Turai ta Champions League a wannan mako.
Wasu ƴan wasan Arsenal sun bayyana David Raya a matsayin gola "mafi ƙwarewa" a duniya bayan rawar da ya taka a karawar da ƙungiyarsa ta yi nasara da ci ɗaya tsakanin ta da Sporting.
A ɓangare ɗaya kuma hazaƙar da Manuel Neuer ya nuna ce ta taimaka wa Bayern Munich wajen samun nasara a kan Real Madrid, lamarin da ya kai ga wasu kafafaen yaɗa labarai a ƙasar Jamus na kiraye-kirayen komawar mai tsaron ragar yi wa tawagar ƙasarsa wasa.
Wannan ya buɗe muhawara kan wane mai tsaron raga ne ya fi hazaƙa, musamman a yayin da ake tunkarar gasar cin kofin duniya.
Sashen wasanni na BBC ya yi Nazari kan wasu da ake ganin suna gaba-gaba a wannan batu.
David Raya - Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
A karawar Arsenal da ta yi nasara da ci 1-0 da ƙungiyar Sporting, Raya ya kaɓe ƙwallaye huɗu masu kyau, ciki har da wadda ya tunkuɗe ta daki ƙarfen raga daga Maxi Araujo, wanda hakan ya sa aka ci gaba da wasa 0-0 kafin Kai Haverts ya jefa ƙwallon da ta bai wa Arsenal ɗin nasara.
Tun daga kakar da ta gabata, Raya ya tsare raga a wasa 23 a gasar ta Champions League kuma ƙwallo 12 ne kacal aka zura a ragarsa, sannan ya tare ƙwallaye 9.0.
Raya ne yake da mafi yawan wasannin da ba a zura masa ko ƙwallo ɗaya ba, a tsakanin masu tsaron raga na manyan gasannin ƙwallon ƙafa a ƙasashen nahiyar Turai, inda ba a zura masa ƙwallo ba a wasa 22 a dukkanin gasanni.
An sanya sunansa cikin masu Takarar kyautar mai tsaron raga mafi hazaƙa da ake bayarwa duk shekara a lokacin bikin Ballon d'or na 2025, said ai bai samu shiga cikin ukun farko ba.
To amma yana cikin masu tsaron raga ƙalilan da suka shiga jerin waɗanda ba su ne manyan masu tsaron raga ba a tawagogin ƙasashensu.
Manuel Neuer - Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa ya yi ritaya daga kama wa tawagar ƙasarsa ƙwallo a watan Agustan 2024, har yanzu da yake da shekara 40 a duniya, Manuel Neuer na cikin masu hazaƙa.
Ya buga wasa na 136 ke nan ga ƙungiyar Bayer a gasar zakaru ta Champions League a lokacin da ƙungiyar ta kara da Real Madrid, inda kuma ya nuna hazaƙa sosai.
Ba taɓa sanya sunan Neuer cikin masu takarar lashe gola mafi hazaƙa ba a bikin Ballon d'Or amma ya lashe kofin Bundesliga 12, da Champions League 2 da kuma lashe kofin duniya tare da tawagar Jamus.
Iker Casillas ne kawai golan da ya yi wa ƙungiya ɗaya wasa mai yawa kamar Neuer, inda yak ama wa Real Madrid sau 149.
Bayan ƙwarewar da ya nuna a karawa da Real, ana ta kiraye-kirayen ya koma kama wa tawagar Jamus wasa, inda a yanzu Oliver Baumann ne babban mai tsaron raga.
Thibaut Courtois - Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Ana kewar Thibaut Courtois wanda a halin yanzu ba ya kama wa Real Madrid wasa sanadiyyar rauni da ya samu a ƙafarsa.
Ya buga wasanni 23 a gasar Champions League tun daga kakar da ta gabata, inda tun daga lokacin ya tare ƙwallo 105.
Sai dai an zura masa ƙwallo 29, ƙwallo 17 ke nan fiye da waɗanda aka zura wa Raya a kwatankwacin lokacin.
Golan na tawagar ƙasar Belgium, wanda ya haska sosai a ƙungiyar Chelsea gabanin komawa Real, ya lashe kyautar mai tsaron raga mafi hazaƙa a shekarar 2022.
Emiliano Martinez - Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron ragar da ya lashe kofin duniya tare da tawagar Argentina a 2022, Emiliano Martinez ya lashe kyautuka da dama sanadiyyar nasarar da ya samu.
Ya lashe kyautar mai tsaron raga mafi hazaƙa a shekarar 2023 da 2024 kuma an zaɓe shi a matsayin golan tawagar ta maza a shekarar 2022 da kuma 2024.
Martinez ya kama gola a wasa 12 a gasar zakarun Turai ta Champions League a kakar wasa da ta gabata, inda ya tare ƙwallaye 49.
Alisson - Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Akwai dalili ɗaya da ya sanya Liverpool ta iya yin nasara da ci 1-0 a kan ƙungiyar PSG a zagayen ƴan 16 na gasar zakaru ta Champions League a kakar da ta gabata.
Wannan dalili kuwa ba kowa ba ne sai Alisson.
Tun daga farkon kakar wasa da ta gabata a gasar Champions League, Alisson ya tare ƙwallaye 37 a wasanni 12.
Shi ne ya lashe kyautar mai tsaron raga mafi ƙwazo a shekarar 2019, ya ƙara lashewa a 2022 sannan ya sake lashe a 2025, kuma Alisson ya burge a lokacin da Liverpool ta lashe gasar Champions League a 2019.
Gianluigi Donnarumma - Manchester City

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan komawa ƙungiyar Manchester City a watan Satumba, Gianluigi Donnarumma ya kasance zaɓin farko ga mai horaswa Pep Guardiola.
Sai dai duk da ƙwarewarsa, wani lokaci amfani da ƙarfi da ake yi a gasar Premier League, musamman a lokacin bugun ƙusurwa ko na tazara yana haifar masa cikas.
Tun daga farkon kakar wasan Champions League da ta gabata – wadda aka lashe tare da shi a ƙungiyar PSG – an zura masa ƙwallo 25 a karawa 24, sannan ya yi wasa 9 ba tare da an zura masa ƙwallo ba.
Ya lashe kyautar mai tsaron raga mafi hazaƙa a 2021 da 2025, amma har yanzu bai buga gasar cin kofin duniya ba tare da tawagar ƙasarsa ta Italiya, bayan sun gaza samun tikitin gasar karo na uku a jere.
Mike Maignan - AC Milan

Asalin hoton, Getty Images
Mutumin da yam aye gurbin Donnarumma a ƙungiyar AC Milan a lokacin da ya koma PSG, shi ne Mike Maignan – kuma ya nuna kansa a matsayin ɗaya daga cikin masu tsaron raga mafi ƙwarewa a duniya.
Ya buga wasa a ƙungiyoyi irin su PSG, to amma tauraruwarsa ta fara haskawa ne a lokacin da yake a ƙungiyar Lille.
A kakar wasansa ta farko a Milan, ya kasance mutumin da ya fi yawan wasanni ba tare da an zura masa ƙwallo ba.










