Yadda Boko Haram ke kai hare-hare a kudancin Borno

Boko Haram

Asalin hoton, Boko Haram video

Lokacin karatu: Minti 2

Ana ci gaba da bayyana damuwa game da yadda hare-haren ƴan Boko Haram ke dawowa a yankin kudancin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotannin irin waɗannan hare-hare na baya-bayan nan sun nuna cewa sun yi sanadin mutuwar wasu sojoji da ƴan sa kai da sauransu.

A ranar Alhamis aka tashi da rahoton cewa wasu sun kai hari kan runduna ta 29 ta Operation Haɗin kai, kuma rahoton na cewa harin ya yi muni.

Tuni dai hedikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da aukuwar lamarin, duk da cewa ba ta amsa ko musanta rahotannin da ke cewa maharani sun kashe wani babban hafsan sojin Najeriya ba.

An kai harin ne a tsakar dare, a sansanin sojin da ke Benisheikh, nisan kilomita 75 da Maiduguri babban birni babban.

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya ya shaidawa BBC cewa al'ummar yankin na ci gaba da zama cikin fargaba saboda yadda mayaƙan Boko Haram suka dawo da sabon salon kai hare-hare a ƙauykansu.

Ya ce ''harin nan ai ana yi ba yau bane, musamman ma kamar yadda ka sani, Boko Haram tun 2009 an kasa a daƙile su baki daya, saboda haka ya zama kamar jeji...in ya warke sai ya sake ɓullowa.''

Ya yi bayanin cewa ya daɗe yana ƙorafin cewa sojojin Najeriya ba su da makaman da ya dace domin yaƙi da Boko Haram don haka dole ne a gaggauta wadata su da makamai na zamani domin su iya gudanar da ayyukan su.

Sanata Ndume ya kuma ce baya ga makamai dole a kula da walwalar sojojin ta hanyar inganta albashin su da sauran walwala ta yadda za su sami ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.

''Babbar matsalar, sojojinmu ba su da kayan aiki, kuma wanda suke kawo hari, su ƴan Boko Haram da ISWAP sun fi su kayan aiki kuma a yaƙi, abinda ke determining ko za ka yi nasara shi ne kayan aiki.

A biya su albashin da ya kamata, a basu karfin gwiwa, ya kamata gwamnati ta mayar da hankalin ta bisa tsaro da walwalar jama'a, shi ne aikin ta bisa kundin mulkin ƙasa.'' In ji sanata Ndume.

Sai dai ɗan majalisar ya je duk da fargabar da al'ummar yankin nasa ke ciki, sun sha alwashin cewa ba za su taɓa bari ƴan BokoHaram su sake kafa daula a ƙauyukan su ba.

Ya jaddada cewa ''maganar gudu dai kuwa, ko kuma a tashi gaba ɗaya mun riga mun sha alwashin cewa ba zai yiwu ba, ba za mu sake barin garin mu ga Boko Haram ba, in shaa Allahu.''