Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Amurka da Iran ke musayar bayanai masu karo da juna kan tattaunawa
Jami'an Amurka da na Iran na bayar da bayanai masu karo da juna kan yiwuwar tattaunawa tsakanin kasashen biyu kan yakin da ake yi.
Shugaba Donald Trump ya ce ya É—age barazanarsa ta kai hare-hare kan tashoshin wutar lantarkin Iran bayan abin da ya kira "tattaunawa mai ma'ana da Tehran."
Sai dai kakakin majalisar dokokin Iran ya musanta cewa an gudanar da tattaunawar, yana mai danganta iƙirarin Trump da "labarin ƙarya."
Masu sharhi dai sun ce ayyukan Trump a ƴan kwanakin da suka gabata sun kasance masu karo da juna musamman ta fuskar diflomasiyya da kuma ƙoƙarin karkatar da hankali.
Tun a ranar Litinin shugaba Donald Trump ya ce ya yi tattaunawa mai ma'ana da jami'an Iran, matakin da gwamnatin Tehran ta ce Trump ya yi hakan ne domin yaudara don farfado da darajar kasuwar makamashi, musamman kafin cikar wa'adinsa na bude mashigar Hormuz ko kuma ya tarwatsa babbar tashar lantarkinta.
Matakin na Trump ya sa farashin danyen mai ya sauka kafin daga bisani kuma ya kara tashi bayan Iran ta karyata cewa ta tattauna da Amurka.
Pakistan ta yi tayin shiga tsakani
Rahotanni daga kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce Pakistan za ta jagoranci tattaunawar kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Amurka da Iran.
Rahotannin sun ce manyan jami'an gwamnatin Amurka da suka ƙunshi manzo na musamman ga shugaba Trump Steve Witkoff da mataimakin shugaban kasa JD Vance za su gana da wakilan Iran a Pakistan.
Fadar White House ba ta musanta rahotannin ba, kuma Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya ce ya zanta da shugaban Iran Masoud Pezeshkian kan mummunan halin da yankin tekun Fasha ke ciki da kuma nuna sha'war Pakistan na taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Sai dai babu wata sanarwa mai kama da haka daga ɓangaren Iran, kodayake ma'aikatar harakokin Iran ta ce ta samu sakwanni daga wasu kasashe amininanta da ke nuna cewa Amurka ta nemi a sasanta domin kawo karshen yakin.