Wace dabara ta rage wa jam'iyyar ADC?

Asalin hoton, ADC/BBC
Jam'iyyar adawa a Najeriya ADC ta ƙalubalanci hukumar zaɓe Inec game da tarukan da zata gudanar.
ADC ta shirya yadda zata gudanar da tarukan ta duk da Inec ba ta amince da shugabancin kwamitin ayyuka na riƙon ƙwarya na jam'iyyar ba, ya yin da zaɓen shekara ta 2027 ke gabatowa.
Wannan na zuwa ne bayan ADC ta yi watsi da matakin da Inec ta ɗauka na cire sunan David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar da Ra'uf Aregbesola da kuma sunan sauran membobin kwamitin ayyuka daga jadawalin sunayen da Inec ta amince da su a matsayin shugabannin a jam'iyyar saboda wani hukuncin Kotu.
Hukumar Zaɓe Inec ta sanar da ranar 1 ga watan Afrilu shekara ta 2026 a matsayin ranar daina karɓar ƙorafi ko wata jarjejeniya ko kuma tsari daga jam'iyyar.
Inec ta ƙara da cewa ba ruwan ta da dukkan tarukan da jam'iyyun biyu zasu gudanar har sai babbar kotun tarayya da zartar da hukunci.
Wannan ne ya sanya masu ruwa da tsaki a jam'iyyar suka gana da manema labarai. Masu ruwa da tsakin da suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark da Rotimi Ameachi daga jihar Rivers da Peter Obi daga jihar Anambra da Ra'uf Aregbesola daga jihar Osun da kuma Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso daga Kano.
Ya yin taron wanda David Marka ya jagoranta, ya bayyana cewar zasu ci gaba da tarukansu ko da Inec ba zata halarta ba.
David Mark ya ƙara da cewa ba wata doka a kundin tsarin mulkin Najeriya da ta ce tilas sai Inec ta sanya ido a tarukan jam'iyya kafin taron ya zama halastacce.
David Mark ya kuma tambayi Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC cewar me ya ke fargaba?
Ya yin da ake ci gaba da wannan tataɓurza, jam'iyyar ADC ta shaidawa membobinta cewar abu na gaba shi ne babban taron jam'iyyar wanda tuni suka sanarwa hukumar zaɓe.
''Wannan sanarwa ce ga membobin jam'iyya cewar, duk da matakin da hukumar zaɓe ta ɗauka. ADC zata gudanar da tarukan ta kamar yadda ta tsara saboda ta sanar da Inec tun ranar 27 ga watan fabrairu shekara ta 2026.''
Kamar yadda kakakin jam'iyar ADC Bolaji Abdullahi ya sanar.
Jadawalin Hukumar Zaɓe na shekara ta 2027 da kuma abinda ke gaban jam'iyyar ADC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babbar tambaya a yanzu ita ce, mene ne makomar jam'iyyar ADC a dai dai lokacin da watanni ƙalilan suka rage a gudanar da babban zaɓe.
Sabuwar dokar zaɓe da shugaba Tinubu ya sanyawa hannu bayan amincewar majalisa ranar 18 ga watan fabrairu shekara ta 2026 ta bayar da damar sauya lokacin zaɓe.
Da farko Inec ta fidda lokacin zaɓen shekara ta 2027 amma daga baya ta sauya bayan shugaban ƙasa ya sanyawa dokar zaɓe hannu.
A sabon tsarin zaɓen, jam'iyyun siyasa zasu gudunar da zaɓen fidda gwani tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Mayu, sannan zasu warware duk wata danbarwa cikin wannan lokacin.
Hukumar zaɓe Inec ta sanya lokacin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisar wakilai daga ranar 19 ga watan Agusta shekara ta 2026 ya yin da za a fara yaƙin neman zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar jiha daga ranar 9 ga watan Satumbar shekara ta 2026.
Da wannan tsarin ne jam'iyyun siyasa suka fara taruka har da jam'iyyar ADC wadda ta bi sahun takwarorinta wajen fidda tsare-tsarenta.
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC Bolaji Abdullahi ya ce duk da matakin da Inec ta dauka na ba zata sanya ido a harkokinsu ba har sai kotu ta kammala shari'a, zasu ci gaba da abubuwan da suka tsara.
Kasancewar dukkan jam'iyyun siyasa su na da nan da ranar 30 ga watan Mayu shekara ta 2026 su yi dukkan shirye shiryen zaɓuka da suka haɗa da zaɓen fidda gwani, idan Kotu bata ɗauki wani mataki kan jam'iyyar ADC ba, zai iya shafar su a zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni na 2027 - farawa da jihohin Ekiti da Osun.
Akwai wani tsari na hukumar zaɓe da ya bata damar kula da kuma sanya ido a zaɓukan fidda gwani.
''Ana gudanar da zaɓukan fidda gwani a gaban jami'an hukumar Inec wadanda zasu tabbatar da sahihancin zaɓen kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadi doka ta 2010.''
Idan Inec suka ce ba zasu halarci taron jam'iyyar ADC ba da kuma zaɓen fidda gwani, me zai faru? Ko dai sunan ɗan takarar jam'iyyar ba zai fito a akwatin zaɓe ba ko kuma a sake komawa Kotu.
Jadawalin babban taron jam'iyyar ADC
Hukumar Zaɓe ta Najeriya Inec ta sanar cewar za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar wakilai ranar 16 ga watan Janairun shekara ta 2027 ya yin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar jihohi ranar 6 ga watan Fabrairun shekara ta 2027.
Kakakin jam'iyyar ya ce tuni sun sanar da Inec tsarin su kuma ba abinda zai hana su aywatar da shi.
- Tantance ƴan takara- 7 April 2026
- Ƙorafe-korafe da tantancewa -8 April 2026
- Taron ƙananan hukumomi da mazaɓu - 9 April 2026
- ƙorafe-ƙorafe-10 April 2026
- Taron jam'iyya a jihohi-11 April 2026
- Sauraron ƙorafe-ƙorafe da ɗaukaka ƙara- 12 April 2026
- Babban taron jam'iyya-14 April 2026










