Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/03/2026
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026.
Tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC ya karɓi katin jam'iyyar ADC a hukumance, a ranar Litinin.
A ranar Lahadi ne ya sanar da ficewa daga jam'iyyar APC, tare da jadadda mubaya'arsa ga tsarin Kwankwasiyya.
Bayanai na cewa komawar tasa na da alaƙa da rashin yadda ake zargin mayar da shi saniyar ware a jam'iyyar APC.
Tundai bayan da kotun koli ta Najeriya ta tabbatar wa da Abba Kabir Yusuf kujerar gwamnan Kano, wasu magoya bayan Nasiru Gawuna suka yi ta sa ran shugaba Tinubu zai bai wa mai gidan nasu mukami mai girma.
A ranar Asabar ne Gawuna ya sanar da ajiye mukamin shugaban hukumar gudanarwa na bankin lamunin gidaje na Najeriya da Tinubu ya yi masa.
Jirgin Russia dauke da mai ya isa Cuba
Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgin ruwan dakon mai mallakin kasar Rasha ya isa tashar jiragen ruwa ta Matanzas na kasar Cuba, lamarin da ya sauƙaƙa matakin hana shigar da mai tsibirin da Washington ta yi na tsawon watanni uku.
Jirgin na dauke da gangar danyen mai kimanin ganga dubu dari bakwai da talatin, wanda zai taimakawa ƙasar na ƴan makonni.
Hakan na zuwa ne bayan kalaman da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan cewa ba shi da wata matsala da kasashen da ke aika man fetur zuwa Cuba - sabanin barazanar harajin da ya yi a baya kan kasashen da ke samar da tsibiri mai.
Masu sharhi na cewa za a iya kwashe kwanaki ashirin kafin a sarrafa ɗanyan man zuwa man dizel, sannan a yi amfani da mako guda wajen jigilar man zuwa wuraren da ake buƙata.
Ba za yaki Iran ba sai dai idan ta yake mu - al-Sharaa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya ce kasarsa ba za ta shiga hadakar yakar kasar Iran ba idan dai ba an kai musu hari ba.
Da yake magana a birnin Landan a Catham House, shugaban na Syria ya ce taimakon da Iran ta bai wa tsohon shugaban Syria ya taimaka wajen daidaita al'ummar Syria.
“Ba mu da matsala da Iran a birnin Tehran," amma muna da matsala da Iran a birnin Damascus.”
Ya kara da cewa ba shi da wata alaka da Iran tun bayan barkewar yakin. Kasashen biyu ba su da alakar huldar jakadanci.
Pete Hegseth ya ce Amurka ta kusa kammala samun nasara a kan Iran
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya yi iƙirarin cewa Amurka ta kusa samun nasara a yaƙin da ta ke yi da Iran -- yana mai cewa kwanaki masu zuwa za su kasance masu matuƙar muhimmanci.
Ya ce hare haren da Amurka ke kai wa na karuwa, yayin da Iran ke raguwa, kuma ya bukaci shugabannin Iran da su kulla yarjejeniya bisa sharuddan Shugaba Trump, ko kuma su fuskanci hare-hare masu tsanani.
Ya ce tabbas za su harba makamai masu linzami, amma za mu kakkabo su, za su shige ƙarƙashin ƙasa, amma za mu gano su.
Dakarun juyin juya halin Iran sun fitar da martani, inda suka yi barazanar kai hari kan kamfanonin fasahar Amurka domin daukar fansa kan kisan shugabannin Iran.
Musayar sakonni muke da Amurka ba tattaunawa ba - Araghchi
Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya shaida wa Aljazeera cewa abin da ke faruwa yanzu haka tsakaninsu da Amurka ba tattaunawa ba ne illa dai musayar sakonni da ake yi ta hannun kawayen Iran da ke yankin.
Araghchi ya ce ya karbi sakonni daga jakadan Amurka na Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff kai tsaye sabanin a baya amma wannan ba yana nufin muna tattaunawa ba ne.
Araghchi ya kuma ce Iran ba ta mayar da martani ba dangane da daftarin Trump mai kunshe da bukatu 15.
"Bukatun iran domin kawo karshen yakin nan a fayyace suke@, in ji Araghchi, inda ya tsaya kai da fata cewa Iran tana son samun tabbacin cewa ba za a sake kai mata hare-hare ba sannan a biya ta diyyar barnar da aka yi mata.
Ya kuma ce Iran ba za ta amince da tsagaita wuta ba illa dakatar da yaki kwata-kwata a kan kasar da ma ilahirin yankin Gabas ta tsakiya.
Isra'ila ta ce za ta ruguje wasu kauyuka a Lebanon
Asalin hoton, Getty Images
Ministan tsaron Isra'ila ya ce sojojin Isra'ila za su ruguza dukkanin gidaje a kauyukan Lebanon da ke kusa da kan iyakar Isra'ila.
Isreal Katz ya ce sojojin za su ci gaba da iko da wani yanki mai fadi, har zuwa kogin Litani, ko da an kawo karshen rikicin da suke yi da Hizbullah.
Ministan ya ce za a hana sama da mazauna Lebanon dubu dari shida da suka rasa matsugunansu komawa gida har sai an tabbatar da tsaron mazauna arewacin Isra’ila.
Fira Ministan Canada Mark Carney ya bayyana matakin a matsayin keta haddin iyakokin ƙasar Lebanon.
Trump ya caccaki Birtaniya kan gaza kwato mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya caccaki Birtaniya da sauran kasashen da ke fama da karancin mai saboda yakin da ake yi da Iran.
Ya ce su tashi su ƙwato wa kansu hakki ta hanyar koƙarin buɗe mashigin Hormuz, wadda Iran ta rufe.
Mista Trump ya ce bai kamata su kara tsammanin wani taimako daga Amurka ba, kamar yadda suka ki mara masa baya kan yakin.
Wakilin BBC ya ce fushin da Donald Trump ke yi da ƙawayen ƙasarsa na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta Nato ya kai mataki na ƙololuwa a yau, kan jan kafa da suke yi wajen taimakawa a ƙoƙarin buɗe mashigin.
Har yanzu dai ana samun bayanai masu karo da juna game da ko ana tattaunawa don sake bude mashigin.
Mece ce mashigar Bab al-Mandab da Iran ke barazanar sake rufewa?
Asalin hoton, Getty Images
Barzanar da Iran ta yi na rufe wata hanyar ruwa mai muhimmanci a Tekun Maliya ta janyo fargaba, kan yadda hakan zai ƙara kawo tsaiko ga kasuwanci a duniya.
Tuni Iran ɗin ta riga ta rufe mashigar Hormuz, inda ta hana zirga-zirgar jiragen ruwa, a yanzu kuma tana barazanar janyo tsaiko ta mashigar Bab al-Mandab tsakanin mashigin Gulf da Tekun Maliya, har ya dangana da mashigar ruwan Suez.
Iran ta ce za ta iya karkata "wani ɓangaren" a yaƙin idan aka tura sojojin Amurka ta ƙasa zuwa ƙasar.
"Ana kallon mashigar Bab al-Mandab a matsayin ɗaya daga cikin masu muhimmanci a duniya, kuma Iran na da damar yin barazana a kai," a cewar wani jami'in sojin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim da ke alaƙa da dakarun huyin juya-hali ya ruwaito.
Iran ta yi barazanar rufe mashigar idan Amurka ta kai hari kan tsibirin Kharg, wanda yake ɗauke da ɗimbin mai. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana son "mallakar man Iran" kuma yana duba yiwuwar ƙwace iko da tsibirin.
Sakataren tsaron Birtaniya, John Healey, ya ce kusan dakarun ƙasar 1,000 ne aka girke a yankin Gulf, ciki har da wadanda ke ƙasar Cyprus.
Mista Healey, wanda ke ziyara a yankin, ya ce za a ƙara tsaron sararin samaniya ga ƙawayen Birtaniya da ke yankin.
Ya ƙara da cewa Iran na ci gaba da ''faɗaɗa'' hare-harenta a yankin, kuma ana sa ran yaƙin zai kai ''wasu makonni masu zuwa'' nan gaba.
Sakaten tsaron na Birtaniya ya kuma jaddara muhimmanci buɗe mashigar Hormuz.
''Ƙawayen ƙasashe na duba zaɓin da ake da su na buɗe mashigar'', wanda ya ce na buƙatar martanin ƙasashen duniya, ciki har da Amurka.
Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya ƙara naira tiriliyan 9 cikin kasafin kuɗin 2026
Asalin hoton, Fadar shugaban Ƙasa/FB
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi Majalisar Dokokin Ƙasa ta amince da ƙara naira tiriliyan 9 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda hakan zai ɗaga jimillar kasafin daga naira tiriliyan 58.4 zuwa naira tiriliyan 67.4.
An bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisa na ranar Talata.
Shugaban ya bayyana cewa wannan ƙarin na da nufin buƙasa fayyace kashe kuɗaɗe da kuma aiwatar da wasu manyan tsare-tsaren gwamnati.
A cewarsa, ƙarin zai taimaka wajen ƙarfafa tsarin kasafin kuɗi da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati.
A cikin wasiƙar, Tinubu ya ce akwai muhimman dalilai uku da suka sa aka nemi wannan ƙarin.
Daya daga cikinsu shi ne buƙatar daidaita da kuma biyan wasu haƙƙoƙi na shari’a da suka rage daga tsofaffin kasafin kuɗi, domin kada su hana aiwatar da kasafin shekarar 2026 yadda ya dace.
Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen samun cikakken tsari na kuɗin gwamnati da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da su cikin gaskiya da inganci.
Shugaban Senegal ya sanya hannu kan dokar tsananta haramci auren jinsi a ƙasar
Asalin hoton, Bassirou Diomaye Faye/ X
Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya sanya hannu kan sabuwar doka da za ta ninka tsawon hukuncin ɗauri zuwa 10 ga wanda aka samu da alaƙar auren jinsi a ƙasar.
Sabuwar dokar, wadda majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da ita a ranar 11 ga Maris, 2026, ta sake fasalin gabatar da ƙara yawan abin da tsohuwar dokar ta ƙunsa.
Sashe na 319 na dokar a yanzu ya bayyana cewa dokar ta ƙunshi "duk wata alaƙar jima'i ko yunƙurin jima'i tsakanin mutum biyu masu jinsi iri ɗaya, haɗi da yunƙurin jima'i da gawa ko dabba.
Dokar wadda ta kasance ɗaya daga cikin alƙawuran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye da Firayim Minista Ousmane Sonko, an aike da ita zuwa majalisar dokokin ƙasar bayan da aka kama wasu da ake zargin suna da alaƙar jinsi ɗaya, wadda tuni aka haramta ta a ƙarƙashin dokar Senegal.
A shekarun bayan-bayan nan wasu ƙasashen Afirka sun gabatar da dokoki masu tsauri kan alaƙar jinsi ɗaya.
A watan Satumban shekarar da ta gabata ne majalisar rikon kwarya ta Burkina Faso ta amince da kudirin dokar haramta yin alaƙar jinsi a ƙasar, bayan makwabciyarta Mali a shekarar 2024.
Haka ma a 2023, Uganda ta amince da wasu tsauraran dokokin haramta auren jinsi a ƙasar, inda za a iya yanke wa mutumin da aka samu da laifin hukuncin ɗaurin rai da rai.
'Rikicin yanzu na tuna mana abin da ya faru a baya a Jos'
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Faransa ta hana Amurka amfani da sararin samaniyarta wajen kai wa Iran hari
Faransa ta ƙi amincewa Amurka amfani da sararin samaniyarta domin kai hare-hare kan Iran, a wani mataki da ke nuna yadda rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsanani.
Wannan na zuwa ne yayin da wasu ƙasashen Turai ke ɗaukar matakan kaucewa shiga rikicin kai tsaye.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki matakin na Faransa, inda ya koka kan hana wani jirgi ɗauke da makamai wucewa ta sararin samaniyarta zuwa Isra’ila.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce “Amurka za ta tuna da wannan mataki na Faransa” yana nuna rashin jin daɗinsa kan lamarin.
A gefe guda kuma, Ministan Harkokin Wajen Spain ya sanar a jiya cewa ƙasar ta rufe sararin samanta ga jiragen da ke da alaƙa da yaƙin Iran.
Matakin na Spain ya ƙara nuna yadda ƙasashen Turai ke ƙoƙarin nisantar da kansu daga shiga yaƙin kai tsaye.
Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya ciyo bashin dala biliyan 6
Asalin hoton, Bayo onanuga/X
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da buƙatarsa ta ciyo bashin dala biliyan 6 domin tallafa wa bukatun kashe kuɗin gwamnati.
Buƙatar ta zo ne ta cikin wasiƙu guda biyu da aka aikewa shugaban majalisar, Godswill Akpabio, inda aka karanta su a zaman majalisar na ranar Talata.
A wasiƙa ta farko, shugaban ya nemi izinin ciyo bashin dala biliyan 5 daga bankin Abu Dhabi, domin cike giɓin kasafin kuɗi da kuma biyan wasu basussukan gwamnati. Ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da daidaito a harkokin kuɗin ƙasar.
A wasiƙa ta biyu kuma, Tinubu ya nemi amincewar majalisar domin karɓar bashin dala biliyan 1 daga bankin Citibank da ke birnin London. An ce za a yi amfani da kuɗin ne wajen gyaran manyan tashoshin jiragen ruwa, ciki har da tashoshin jiragen ruwa na Lagos da tashar jiragen ruwa ta Tin Can.
Shugaban ya ce aikin gyaran tashoshin jiragen ruwan na da nufin magance matsalolin da ke akwai da inganta yadda ake gudanar da ayyuka da ƙarfafa matakan tsaro, da kuma bunƙasa kasuwancin da ba na mai ba. Haka kuma, ya ce hakan zai taimaka wajen ƙara ƙarfin Najeriya a matsayin cibiyar kasuwanci a yankin.
Bayan gabatar da buƙatun, shugaban majalisar dattawa ya miƙa wasiƙun ga kwamitin majalisa kan basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko, domin nazari da gaggauta yanke hukunci.
Jami'an tsaro sun sake kama El-Rufai bayan fitowarsa daga kotu - Iyalinsa
Asalin hoton, El-Rufai/X
Rahotanni daga iyalin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun ce jami’an tsaro sun sake kama shi jim kaɗan bayan fitowarsa daga kotu a yau, Talata.
Wata majiya daga cikin iyalinsa ta shaida wa BBC cewa an kama shi ne a wajen harabar kotun, lamarin da ya jefa iyalansa da magoya bayansa cikin damuwa.
Majiyar ta kuma ce bayan kammala sauraron buƙatar ba da belinsa ne aka yi awon gaba da shi, inda suka sa ran Abuja za a kai shi.
Har yanzu ba a bayyana cikakken dalilin sake kamen nasa ba, amma ana zargin yana da alaƙa da binciken da hukumomi ke ci gaba da yi a kansa.
Sai dai har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke bayani kan lamarin ba.
Najeriya ta zargi Mozambique da take haƙƙin ƴan ƙasarta bayan fitar da su
Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Najeriya ta zargi gwamnatin Mozambique da take haƙƙin ‘yan kasarta bayan kama su tare da tsare su, sannan daga bisani ta fitar da su daga ƙasar.
Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCOM) ta ce an kama mutanen tare da korarsu ba tare da bin ƙa’idojin doka ba, inda ta bayyana yadda aka yi musu a matsayin take haƙƙin ɗanadam da kuma karya dokokin ƙasa da ƙasa da ke kare baƙi.
Hukumar ta kuma ce jami’an Mozambique ba su tuntuɓi ofishin jakadancin Najeriya da ke Maputo ba, duk da ƙoƙarin da jami’an diflomasiyya suka yi na shiga tsakani.
Jami’an Mozambique sun ce kamen wani ɓangare ne na aikin yau da kullum na kula da shige da fice a babban birnin ƙasar, Maputo, amma ba su fitar da cikakken bayani kan zargin da Najeriya ke yi wa ƙasar ba.
Najeriya da Mozambique na da kyakkyawar alaƙar diflomasiyya tun shekaru da dama, inda suke haɗin gwiwa a ƙarƙashin ƙungiyar Tarayyar Afirka kan harkokin kasuwanci da gudun hijira da zaman lafiya a yankin.
Sai dai irin waɗannan al’amura na iya haifar da tsaiko a dangantaka, musamman ganin yadda Najeriya ke ƙoƙarin kare haƙƙin ‘yan kasarta a ƙasashen waje.
NiDCOM ta tabbatar da cewa daga cikin ‘yan Najeriya 42 da aka kama a farkon watan nan, an riga an fitar da 40 zuwa gida yayin da mutum biyu ke ci gaba da zama a Mozambique.
Mai magana da yawun NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya ce an kama mutanen ne a wuraren kasuwancinsu ba tare da la’akari da cewa suna da ingantattun takardun zama da aiki ba.
Ana sa ran ma’aikatar harkokin wajen Najeriya za ta ɗauki batun ta hanyoyin diflomasiyya, yayin da ake kira da a samar da kariya mai ƙarfi ga ‘yan Afirka da ke rayuwa da aiki a wasu ƙasashen nahiyar.
An kashe masu biki aƙalla 13 tare da sace wasu da dama a jihar Kaduna
Asalin hoton, Uba Sani/X
Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa aƙalla mutum 13 ne suka mutu, yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari a wajen wani bikin aure.
An kai harin ne da daddare a ranar Lahadi a kauyen Kahir, da ke karamar hukumar Kagarko a jihar. Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun dira wurin bikin da misalin karfe 11:47 na dare, inda suka buɗe wuta kan mutanen da suka taru domin shagalin bikin.
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida, sun ruwaito mazauna yankin, suna cewa maharan sun zo da yawa kuma suna ɗauke da manyan makamai inda suka yi ta harbe-harbe ba tare da gaggautawa ba kafin daga bisani suka tsere daga wurin.
Mutane da dama sun jikkata, yayin da har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka yi garkuwa da su ba.
‘Yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan, ya shaida wa BBC cewa: “Eh, lamarin ya faru kuma ana bincike a kai.” Sai dai bai bayyana adadin wadanda suka mutu ko wadanda aka sace ba.
Har yanzu babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.
Sai dai rahotanni sun ce iyalan wadanda aka sace na jiran yiwuwar kiran neman kudin fansa.
An yi jana'izar wani babban jami'in Iran da iyalensa a Tehran
Asalin hoton, Saberin_ir
An gudanar da jana’izar Mohammad Reza Ishaqi, mai bai wa babban hafsan rundunar sojin Iran shawara, a birnin Tehran a yau, inda za a binne shi a maƙabartar “Hawan Shahidai”.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Iran sun ce mutane shida daga cikin iyalan Ishaqi sun mutu sakamakon harin Isra’ila da Amurka, ciki har da wasu yara, kuma an yi musu jana’iza a yau.
Ba a fitar da cikakken bayani kan lokaci da wurin da suka mutu ba.
Brigadiya Janar Ishaqi ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan ‘yan sanda a jihohin Kerman, Khuzestan da Gilan, sannan ya ya kasance babban jami'in rundunar ‘yan sanda.
Za mu hukunta waɗanda suka yi kashe-kashen Filato da Kaduna - Tinubu
Asalin hoton, Tinubu/X
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sha alwashin hukunta waɗanda suka yi kashe-kashen Filato da Kaduna a yayin da yake allawadai da aukuwar lamarin.
Shugaban ya umurci jami’an tsaro da su bi sahun waɗanda suka aikiata waɗannan laifukan.
‘Yan bindiga ne suka kashe mutane kusan 28 a Angwan Rukuba ta Jos da ke jihar Filato a ranar Lahadi yayin da kuma wasu mahara suka kai hari a ƙauyen Kahir da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutane yayin da aka sace wasu.
A sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya ce kashe-kashen da sace baƙi a wurin bikin aure a Kaduna ya saɓawa dukkan abin da Najeriya ke tsaye a kai.
Ya umurci hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen bi sahun waɗanda suka aikata wannan aika-aikar da kuma masu yaɗa ƙarya da za su iya haifar da tashin hankali.
Tinubu ya jaddada cewa hukumomin tsaro na aiki kafada da kafada wajen magance lamarin, inda ya ce haɗin kai da jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen kiyaye zaman lafiya da kare rayuka da dukiya.
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya ce jihar ba za ta tsorata ba, kuma za ta fito da ƙarfi da haɗin kai wajen tabbatar da zaman lafiya.
Hukumar leƙen asirin Iran ta kama mutum 62 da ta bayyana da maƙiya
Asalin hoton, Tasnim news agency
Hukumar leƙen aisirin Iran ta sanar da kama mutum 62 da ta bayyana da 'maƙiya' da take zarginsu da aikawa da bayanai da hotuna zuwa ga ga wata kafar yaɗa labarai da ke wajen Iran.
A cikin sanarwar hukumar, an ce an kama mutum 41 a lardin Tehran bisa zargin aika wuraren da bayanan shingayen bincike da bayanan unguwanni a matsayin na soji ga wata kafar yaɗa labarai da ke wajen Iran.
Haka kuma, an kama mutane biyar a lardin Fars kan zargin kasancewa mambobi a cikin ƙungiyoyi da ke haifar da matsalar tsaro guda biyu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an kama mutane takwas a lardunan Gilan da Kermanshah bisa zargin alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, sannan an ƙwato bindigogi biyu daga hannun su.