Mece ce mashigar Bab al-Mandab da Iran ke barazanar sake rufewa?

Asalin hoton, Gallo Images via Getty
Barzanar da Iran ta yi na rufe wata hanyar ruwa mai muhimmanci a Tekun Maliya ta janyo fargaba, kan yadda hakan zai ƙara kawo tsaiko ga kasuwanci a duniya.
Tuni Iran ɗin ta riga ta rufe mashigar Hormuz, inda ta hana zirga-zirgar jiragen ruwa, a yanzu kuma tana barazanar janyo tsaiko ta mashigar Bab al-Mandab tsakanin mashigin Gulf da Tekun Maliya, har ya dangana da mashigar ruwan Suez.
Iran ta ce za ta iya karkata "wani ɓangaren" a yaƙin idan aka tura sojojin Amurka ta ƙasa zuwa ƙasar.
"Ana kallon mashigar Bab al-Mandab a matsayin ɗaya daga cikin masu muhimmanci a duniya, kuma Iran na da damar yin barazana a kai," a cewar wani jami'in sojin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim da ke alaƙa da dakarun huyin juya-hali ya ruwaito.
Iran ta yi barazanar rufe mashigar idan Amurka ta kai hari kan tsibirin Kharg, wanda yake ɗauke da ɗimbin mai. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana son "mallakar man Iran" kuma yana duba yiwuwar ƙwace iko da tsibirin.
Me ya sa Bab al-Mandab ke da muhimmanci?

Bab al-Mandab yana tsakanin Yemen a ɓangaren Larabawa a tekun Maliya, sai kuma Djibouti da Eritrea a ɓangaren Afirka.Dole ne jiragen ruwa da ke tahowa daga tekun Indiya da kuma mashigin Gulf su bi ta wurin domin kai wa ga mashigar Suez.
Mashigar mai nisan kilomita 115 da kuma faɗin kilomita 36, ta zama mai muhimmanci wajen harkar kasuwanci a duniya lokacin da aka buɗe mashigar Suez a 1869, abin da ya sa aka samu hanya mafi sauki kuma gajere tsakanin Turai da Asiya.
Tekun Maliya ta ya kasance ɗaya daga cikin wadda aka fi hada-hada a duniya, kuma kusan rabin jiragen ruwa da ake da su a duniya na bi ta hanyar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mashigar Hormuz wadda aka riga aka rufe tun soma yaƙi, na da kashi 20 na man da ake fitarwa zuwa duniya. Rufe mashigar Bab al-Mandab zai sake janyo cikas na kashi 12 na mai da ake kai wa ƙasashen duniya.
Aƙalla ganga miliyan biyar na mai da ya fito daga ƙasashen Gabas ta Tsakiya da kuma Asiya zuwa ƙasashen yamma na bi ta mashigar a kowace rana, a cewar hukumar lura da makamashi ta Amurka.
Sannan kashi takwas na iskar gas (LNG) na bi ta mashigar, abin da ya sa yake da muhimmanci ga samar da makamshi a duniya.
Tun bayan rufe mashigar Hormuz, tekun Maliya ya ƙara zama mai muhimmanci a kasuwancin duniya. Saudiyya ta fara amfani da Bab al-Mandab a matsayin wurin yada zango bayan dauko mai daga tashar jirgin ruwa ta Yanbu. Riyadh na aika miliyoyin gangar ɗanyen mai a kowace rana zuwa duniya.
Ba ya ga ɗanyen mai da iskar gas, mashigar Bab al-Mandab yana cikin sahun hanyoyi da suka haɗa Gabas ta Tsakiya da kuma ƙasashen yamma, inda dubban jiragen ruwan dakon kaya ke bi ta ruwan a kowace rana.

Asalin hoton, Suez Canal Authority via European Pressphoto Agency
Rufe mashigar zai iya janyo irin tasirin da aka gani a shekara ta 2021, lokacin da wani jirgin ruwa na Ever Green ya rufe mashigar Suez.
Lamarin ya janyo matsala wajen samar da mai a duniya, inda aka fuskanci hauhawar farashi da kuma tsaiko wajen samar da mai da kuma wasu kayayyaki.
Rawar da ƴan Houthi ke takawa
Ƴan Houthi za su iya kai duk wani hari da za a kai kan mashigar Bab al-Mandab, ƙungiya da ta kasance tana samun goyon bayan Iran.
Da yake tattaunawa da Reuters, wani jagoran Houthi da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce ƙungiyar "a shirye take" ta kai hari kan mashigar Bab al-Mandab don nuna goyon baya ga Tehran.
A ranar 28 ga watan Maris, Houthi ta kaddamar da hari kan Isra'ila, karo na farko da suka shiga yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.
Isra'ila ta ce ta kakkaɓe makaman linzami biyu da suka fito daga Yemen.
Ƙungiyar na iko da bakin ruwan tekun Maliya kuma ta far wa mashigar Bab al-Mandab lokacin yaƙin Gaza.
Houthi ta kai hari kan jiragen ruwa n kasuwanci sama da 100 ta hanyar amfani da makaman linzami da kuma jirage marasa matuki, inda ta nutsar da jiragen ruwa biyu da kuma kashe ma'aikata huɗu.

Asalin hoton, Houthi Military Media via Reuters
A watan Nuwambar 2023, ƙungiyar ta yi amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen ƙwace wani jirgin ruwan dakon kaya a tekun Maliya.
Duk da cewa ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa tana afka wa jirage da ke da alaƙa da Isra'ila kaɗai, amma an yi ta Alla-wadai da hare-harensu, abin da ya janyo kamfanonin jigilar kayayyaki ta ruwa da kuma na mai dakatar da zirga-zirga ta yankin.
Waɗannan hare-hare sun ragu a daidai lokacin da Amurka ta ce ƴan Houthi sun miƙa wuya, sannan ita ma ta ce Amurka ce ta janye, sai dai masu sharhi sun ce akwai fargabar cewa waɗannan hare-hare za su sake dawowa.
"Da ma ana sa ran cewa ƴan Houthi daga Yemen za su shiga wannan yaƙi idan aka kasa dakatar da shi," a cewar wakiliyar BBC Lyse Doucet.
Ta ƙara da cewa: "Zuwa yanzu ƴan Houthi waɗanda ke iko da yankin arewa maso yammacin Yemen, ba su shiga afka yaƙin ba - inda shigarsu zai saka su janyo tsaiko a mashigar Bab al-Mandab, wanda ta haɗa tekum Maliya da sauran wuraren kasuwanci a duniya."
A ranar 26 ga watan Fabrairu, hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Amurka ta ce: "Duk da cewa Houthi ba ta kai hari kan jiragen ruwa ba tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Gaza a watan Oktoban 2025, sna ci gaba da zama barazana ga kadarorin Amurka, ciki har da jiragen ruwan kasuwanci a yankin."
Sufurin jiragen ruwa a duniya na tsaka mai wuya

Asalin hoton, Getty Images
Bab al-Mandab yana nufin "ƙofar hawaye" ko "ƙofar tsoro" a Larabci. Sunan yana nuna hatsarori, daga magudanar ruwa mai ƙarfi da iska zuwa fashin teku da kuma rikici.
Tsakanin 2008 da 2012 mashigar Bab al-Mandab da ruwan da ke ƙewaye da shi ya fuskanci hare-haren 'yan fashin teku da dama - wanda galibi ƙungiyoyin Somaliya ke kai wa, inda suke garkuwa da ma'aikatan jirage don neman kuɗin fansa.
Hakan ya sa ƙasashen duniya da kamfanonin sufurin jiragen ruwa ƙarfafa tsaro a yankin.
Toshe mashigar a yau zai ƙara dagula matsalar da kasuwar makamashi ke ciki, wanda tuni rufe mashigar Hormuz ya taɓarɓara.
Katse jigilar kayayyaki a yankin Gulf ya sanya farashin ɗanyen mai sumfurin Brent tashi daga kusan dala 70 kan kowace ganga kafin rikicin zuwa sama da dala 115.
Kasuwancin duniya a fanni daban-daban - daga kayayyakin masarufi zuwa kayan amfanin gona - na jin tasirin ba kaɗan ba.
Wani sabon tsaiko ga wata hanyar ruwa na iya ƙara janyo tashin farashi da kuma durkusar da tattalin arziki a rikicin da ake yi.










