An tabbatar da cewa ba a ga watan Sallah ba a Najeriya, wanda hakan ke nufin za a cika azumi 30 a ƙasar, wadda ke Afirka ta Yamma.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya fitar, inda ya ce gobe Alhamis zai zama 30 ga watan na Ramadan na shekarar 2026.
Hakan na nufin ranar Juma'a, 20 ga watan Maris ce za ta zama ranar Sallah ƙarama a Najeriya, kamar yadda sanarwar ta nuna.
'Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 970 a Lebanon'
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ce ta tarwatsa wasu manyan gadoji biyu da ƙungiyar Hezbollah ke amfani da su wajen jigilar makamai da mayaƙanta.
A baya dai harin Isra'ilan ya fi karkata kan wurare mau cunkoson jama'a a birnin Beirut, inda ta ce tana neman karya cibiyoyin tattalin arziki masu tallafa wa Hezbollah.
Mahukunta a Lebanon sun ce Isra'ila ta kashe mutane aƙalla 970 tun bayan ƙaddamar da hare-haren nata a kan Hezbollah. Lamarin ya kuma tilastawa mutane fiye da miliyan ɗaya yin ƙaura daga gidajn su.
Gobara ta lalata gidaje uku a Kumbotso ta jihar Kano
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta sanar da cewa wata gobara ta tashi a jiya, Talata, 17 ga Maris, 2026, da misalin karfe 11:05 na safe a unguwar Gaida, kusa da gidan brodin Fatima a ƙaramar hukumar Kumbotso.
Sanarwar ta ce wani mutum mai suna Aminu Bello ne ya kira hukumar domin sanar da aukuwar lamarin.
"Nan take aka tura jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar, da tashoshin Sharada da Rijiyar Zaki zuwa wurin domin shawo kan gobarar." in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, "da isarsu, jami’an sun tarar da wata fili mai girman kusan kafa 50 wadda ake amfani da ita a matsayin wajen na’urar lantarki (transformer), na ci da wuta.
Gobarar ta bazu inda ta lalata gidaje uku da ke kusa da wurin.
Hukumar ta bayyana cewa tartsatsin wutar lantarki ne ya haddasa gobarar.
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya buƙaci jama’a da su rika daukar matakan kariya, musamman wajen amfani da kayan lantarki da kuma kauce wa amfani da wuta ba tare da kulawa ba.
Ba a ga watan Sallah a Saudiyya ba
Asalin hoton, Inside the Haramain @insharifain
Hukumomi a Saudiyya sun ce ba a ga jinjirin watan Shawwal ba, wanda hakan ke nufin gobe Alhamis za ta kama 30 ga watan Ramadan.
A wata sanarwa da shafin Inside the Haramain ya fitar, ya ce, "ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya. Don haka za a cike azumu ya zama guda 30. Sannan idin ƙaramar sallah sai ranar Juma'a.
Me zai faru bayan ƙwace kofin Afcon daga hannun Senegal?
Ana ci gaba da muhawara a duniyar ƙwallon ƙafa ta Afirka bayan hukuncin da CAF ta yanke na ƙwace nasarar Senegal a gasar AFCON ta 2025.
Hukumar ta CAF ta ayyana Morocco a matsayin wadda ta lashe kofin, bayan da ta sauya sakamakon wasan ƙarshe.
Wannan mataki ya zo ne bayan sama da wata uku da kammala gasar, inda aka ƙwace nasarar da Senegal ta samu a kan Morocco.
Ga ƙarin bayani a wannan bidiyon.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton domin kallon bidiyon
Iran ta ce za ta kai hari kan matatun mai biyar a ƙasashe uku
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta yi gargaɗin cewa za ta kai hari kan matatun mai guda biyar a ƙasashen Saudiya da Qatar, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) “a cikin ‘yan sa’o’i masu zuwa.”
Gargadin ya ce waɗannan “wurare sun zama abin hari kai tsaye.”
Iran ta fitar da wannan gargaɗin ne awa ɗaya bayan rahotannin da ke cewa Isra'ila ta kai hari ta sama a wani kamfanin samar da iskar Gas da ke filin haƙar iskar gas na South Pars.
Filin na South Pars dai shi ne filin haƙo iskar gas mafi girma a duniya, wanda Qatar da Iran ke amfani da shi tare.
Isra'ila ta kai hari kan kamfanin samar da iskar Gas da ke South Pars
Asalin hoton, Getty Images
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa Isra'ila ta kai wani hari ta sama a wani kamfanin samar da iskar Gas da ke filin haƙar iskar gas na South Pars.
Filin na South Pars dai shi ne filin haƙo iskar gas mafi girma a duniya, wanda Qatar da Iran ke amfani da shi tare.
Tuni aka tura jami’an kashe gobara don shawo kan gobarar da ta tashi.
Iran na ci gaba da kai hare-hare ta sama kan Isra'ila da ma yankin baki daya.
Jami'an Isra'ila sun ce an kashe mutane biyu a Tel Aviv a lokacin da ɓaraguzai suka faɗa kansu.
Saudiyya ta ce ta harbo wani jirgi mara matuki wanda ya nufi wani ginin ofishin jakadanci da ke Riyadh babban birnin kasar.
Ƙasashen Kuwait da Qatar su ma sun ce sun kakkaɓo wasu makamai da Iran ta harba ta sama.
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ne zai jagoranci Hawan Idi na bana a cikin shirye-shiryen bukukuwan Sallah.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Waiya, ya fitar a ranar Laraba, gwamnatin ta bayyana cewa za a fara Hawan Idi daga filin Sallar Kofar Mata, kafin a bi hanyoyin da aka tsara zuwa fadar Sarkin Kano.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnati ta ƙara tsaurara matakan tsaro, inda ta yi gargaɗin yiwuwar wasu su tayar da rikici a yayin bukukuwan.
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta jaddada cewa, duk da ƙoƙarin kare al’adun gargajiya na Kano, tabbatar da zaman lafiya da tsaro shi ne abin da ya fi muhimmanci.
A sabbin matakan da aka ɗauka, za a gudanar da Hawan Nasarawa amma ba tare da dawaki ba, yayin da aka dakatar da Hawan Daushe da Hawan Fanisau da kuma Hawan Dorayi a wannan lokaci domin dalilan tsaro.
Haka kuma, an umarci hukumomin tsaro da su ƙara sanya ido tare da tabbatar da bin dukkan ƙa’idojin da aka shimfiɗa kafin da kuma bayan bukukuwan Sallah.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu bin doka, su ba jami’an tsaro haɗin kai, tare da guje wa yaɗa jita-jita, tana mai tabbatar da cewa za a gudanar da bukukuwan cikin lumana.
'Yan wasan ƙwallon ƙafar matan Iran sun fara komawa gida daga Turkiyya
Asalin hoton, Getty Images
Tawagar 'yan wasan ƙwallon ƙafar matan Iran ta fara komawa gida daga Turkiyya, bayan saukarta a garin Igdir a gabashin ƙasar a ranar Laraba, inda ake kai su zuwa bakin ƙasar Iran a Gurbulak.
Tawagar matan ta isa Istanbul a ranar Talata bayan dogon tafiya daga Australia ta hanyar Malaysia da Oman.
Bayan sun kammala rajistar shige da fice da binciken fasfo, rahotannin kafafen labaranTurkiyya sun ce an kai su otel ƙarƙashin tsaron ‘yan sanda a daren ranar Talata.
Wannan na zuwa ne bayan mata bakwai daga cikin 'yan wasa wanda suka fara neman mafaka a Australia bayan ƙin raira waƙar ƙasar Iran kafin wasan farko na Gasar kofin Asiya, amma daga baya mata biyar daga ciki suka canza ra’ayi suka yanke shawarar komawa Iran tare da sauran 'yan wasa.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan Adam sun nuna damuwarsu kan cewa ko an matsa musu lamba ne ta hanyar barazana ga iyalansu kafin suka yanke shawarar komawa ƙasar.
Isra’ila ta ce ta kashe ministan sashen tattara bayanan sirrin Iran, Esmail Khatib
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce an kashe ministan ma'aikatar tattara bayanan sirri na Iran, Esmail Khatib.
A cikin wata sanarwa, Katz ya ce, “a daren jiya ma an kashe ministan sashen tattara bayanan sirrin Iran, Khatib.”
Har zuwa yanzu, Iran ba ta mayar da martani kan wannan batu ba.
An naɗa Khatib a matsayin ministan ma'aikatar tattara bayanan sirri ne a shekarar 2021 ta hannun tsohon shugaban ƙasar, Ebrahim Raisi.
Ya yi karatu a fannin fikihun Musulunci karkashin manyan malamai, ciki har da jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.
Kafin wannan matsayi, ya riƙe manyan muƙamai a ma’aikatar tattara bayanan sirri da kuma ofishin jagoran ƙasa.
Rahotanni sun ce ya shiga rundunar juyin juya halin Iran tun a shekarar 1980, jim kaɗan bayan juyin juya halin Musulunci na 1979.
Isra’ila ta ce harin Iran ya jikkata mutum 192 cikin sa’o’i 24
Asalin hoton, Reuters
Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce mutum 192 ne suka jikkata cikin sa’o’i 24 da suka gabata a harin da Iran ta kai ƙasar inda a halin yanzu an kai su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa daga cikin waɗannan mutane da suka jikkata, mutum huɗu na cikin matsakaicin hali, yayin da mutane 177 ke samun kulawa saboda ƙananan raunuka.
Ba a bayyana halin sauran mutane 11 ba.
A cewar ma’aikatar, jimillar Isra'ilawa da suka jikkata tun bayan fara yaƙin Iran ya kai 3,727.
A cikin wasu sa’o’i da suka gabata kuma, rundunar juyin juya halin Iran ta ce harin da ta kai Isra'ila ya katse wutar lantarkin wani ɓangare na Tel Aviv, tare da kiyasin cewa harin ya ya kashe ko jikkata fiye da Isra'ilawa 230.
Za a yi jana’izar Larijani da manyan jami’an Iran da aka kashe a Tehran
Asalin hoton, Getty Images
A yau ne ake sa ran za a gudanar da jana’izar manyan jami’an tsaron Iran da aka kashe a hare-hare a birnin Tehran.
Rahotanni daga kamfanin dillancin labaran Tasnim mai alaƙa da rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) sun ce za a yi jana’izar babban jami'in tsaron ƙasar, Ali Larijani da kuma shugaban rundunar Basij, Gholamreza Soleimani.
An tsara fara bikin jana’izar ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana agogon ƙasar a dandalin Enghelab da ke Tehran.
Haka kuma, za a haɗa da jana’izar ma'aikatan jirgin ruwa 84 da suka mutu bayan da Amurka ta nutsar da jirgin ruwan yaƙin Iran mai suna Iris Dena da makami mai linzami a ranar 4 ga watan Maris.
Iran ta sanar a ranar Talata cewa Larijani da Soleimani sun mutu ne sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai kan ƙasar.
Bayan faruwar hakan, babban hafsan sojin ƙasar, Amir Hatami, ya yi barazanar ɗaukar matakin ramuwar gayya mai tsauri.
Tinubu ya umarci masu muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara su yi murabus
Asalin hoton, Baya Onanuga/X
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci duk masu muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen 2027 da su soka daga muƙamansu kafin ko a ranar 31 ga watan Maris.
Shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Dewan Goshit ne ya sanar da hakan a ranar Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa matakin shugaban ƙasar ya yi daidai da sashe na 88(1) na dokar zaɓe ta 2026, da kuma jadawalin da hukumar zaɓe INEC ta fitar domin shirye-shiryen zaɓen fidda gwani kafin babban zaɓen 2027.
Umarnin ya shafi dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da shugaban ƙasa ya naɗa waɗanda ke shirin shiga zaɓen fidda gwani ko neman tikitin tsayawa takara.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da ministoci da masu ba shugaban ƙasa shawara da manyan mataimaka na musamman da masu taimaka wa shugaban ƙasa kai tsaye, da kuma shugabanni da daraktoci na hukumomi da dai sauransau.
Sanarwa ta kuma ce Tinubu ya buƙaci duk waɗannan jami’ai su miƙa takardun murabus dinsu ta ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya kafin wa’adin da aka gindaya.
Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasan ya jaddada cewa wannan mataki na da muhimmanci wajen tabbatar da bin dokokin zaɓe da inganta gaskiya a harkokin siyasa, da kuma samar da daidaito ga duk masu neman takara kafin zaɓe.
Haka kuma, ya buƙaci duk waɗanda abin ya shafa su bi umarnin yadda ya kamata, yana mai cewa gwamnatinsa na da ƙuduri wajen tabbatar da sahihancin zaɓe da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar.
An kai sabon hari kan ofishin jakadancin Amurka a Baghdad
Kamfanonin dillancin labaran Faransa AFP da Reuters sun ruwaito cewa an kai sabbin hare-hare a wajen ginin ofishin jakadancin Amurka a Baghdad.
Rahotannin sun ce an ji ƙarar fashe-fashe da dama a kusa da ofishin jakadancin a safiyar Laraba.
Majiyoyin tsaro da ‘yan jaridan AFP da ke wurin sun tabbatar da lamarin.
Ofishin jakadancin yana cikin yankin da ake ƙarfafa tsaro sosai wanda aka fi sani da “Green Zone” a Baghdad, inda ake samun cibiyoyin diflomasiyya da ƙungiyoyi na duniya.
An kai hare-hare kan ofishin jakadancin Amurka sau da dama tun farkon fara yaƙi da Iran kuma alamu na nuna cewa irin waɗannan hare-hare na ci gaba.
Tinubu zai gana da Sarki Charles III a yau
Asalin hoton, Baya Onanuga/X
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai gana da Sarki Charles III a yau ranar Laraba domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da gano damar ƙarin zuba hannun jarin ƴan kasuwa.
Duk da cewa Tinubu ya ziyarci Britaniya sau da dama a lokacin mulkinsa, wannan ce a ziyarar aiki ta farko tsakanin ƙasashen cikin kusan shekaru 37.
Shugaban da matarsa, Oluremi Tinubu, sun isa filin jirgin saman Stansted ranar Talata inda Sarki Charles zai karɓi Tinubu a gidan sarauta na tarihi na Windsor Castle kafin ya shirya liyafar ƙasa da ƙasa da yamma.
Birtaniya da Najeriya na da kyakkyawar alaƙa ta diflomasiyya, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniya ta haɗin kai a Nuwamba 2024 don ƙarfafa tattalin arziki da shige da fice da kuma tsaro.
Ziyarar Tinubu na zuwa ne bayan harin bam ɗin kunar bakin wake da ake zargi ya kashe aƙalla mutane 23 a Maiduguri ranar Litinin da yamma inda ya ba da umarnin tura manyan jami’an tsaro zuwa jihar don “ɗaukar ragamar al’amura.”
Najeriya dai ta kasance cikin rikicin masu iƙirarin jihadi tun a shekarar 2009.
An tsara cewa ranar Alhamis, Tinubu zai gana da Keir Starmer da ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje.
Amurka ta kai hari kan sansanonin makaman Iran a mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta sanar da kai hari kan sansanonin makaman Iran da ke bakin tekun mashigar Hormuz da manyan bama-bamai masu ƙarfi da ake kira da "barrier-busters."
Kwamandojin rundunar ƙasar sun ce an yi amfani da bama-baman da aka yi amfani da su wajen kai harin suna da nauyin fam 5,000 wato kilogram 2,200 kenan.
Sanarwar rundunar ta bayyana cewa: “Makaman Iran na harbin jiragen ruwa a waɗannan wurare na iya kawo barazana ga harkokin sufuri na duniya a mashigar.”
An ce waɗannan bama-baman suna iya ratsa karkashin ƙasa, kuma kowanne na da tsadar kimanin dala $288,000.
Mashigar Hormuz, wacce ke ɗaukar kashi 20 cikin 100 na jigilar man fetur na duniya, ta sami tangarda sosai saboda matakan Iran na rufe ta wanda ya ƙara haifar da tashin farashin mai a duniya.
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Isra’ila bayan kisan Larijani
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar juyin juya halin Iran ta IRGC, ta ce ta ƙaddamar da jerin hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila domin ɗaukar fansa kan kisan babban jami’in tsaron ƙasar Ali Larijani.
Jami’an ƙasar sun ce mutum biyu sun mutu a kusa da Tel Aviv bayan tarkacen makami mai linzami sun faɗa kansu.
Haka ma makaman sun lalata wurare da dama a tashar jirgin ƙasa ta birnin.
An kashe Larijani ne wanda ake zargin yana jagorantar yaƙin Iran, tare da ɗansa da wani mataimakinsa a wani harin Isra’ila.
Ana kallonsa a matsayin mai sassaucin ra’ayi, kuma masu aiko da rahotanni sun ce za a iya maye gurbinsa da wani mai tsaurin ra’ayi, abun da ka iya ƙara dagula lamur.
Muna son a kawo ƙarshen yaƙi gaba ɗaya, ba tsagaita wuta ba - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta neman tsagaita wuta, sai dai tana maraba da kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya kuma na dindindin.
A wata hira da ya yi da Al Jazeera a birnin Tehran, Araqchi ya ce: “Ba tsagaita wuta mu ke nema ba, domin ba ma son wannan yanayi ya sake maimaituwa nan gaba. Muna son a kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya kuma na dindindin.”
Ya kuma zargi Amurka da shiga yaƙin bisa ƙarfafawar Isra'ila in da ya ce,
“A yau waɗanda suka nemi mu miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba, su ne ke neman taimakon abokan hamayyarsu domin buɗe mashigar Hormuz,” in ji shi.
Dangane da lafiyar jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, Araqchi ya ce: “Gwargwadon abin da na sani, raunin da ya samu sama-sama ne, kuma yana cikin koshin lafiya, yana kuma da cikakken iko kan al’amura.”"
Wace riba Najeriya za ta iya samu daga yaƙin Iran da Amurka?
Asalin hoton, Getty Images
Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila a ɗaya gefen na ci gaba da haifar da tashin farashin makamashi a faɗin duniya.
A yanzu haka farashin man fetur ya zarta dala 100 kan kowace ganga.
Iran ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya mafiya arzikin man fetur, sannan take da iko da muhimmayar hanyar jigilar man fetur na yankin Gabas ta Tsakiya, wato mashigar Hormuz.
A matsayin martanin hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata, Iran ta rufe mashigar ta Hormuz, wanda kashi 20 cikin 100 man fetur na iskar gas ɗin duniya ke bi ta wurin.
Ta mashigar ne duka man fetur da iskar gas na ƙasashen yankin Gulf da na Gabas ta Tsakiya ke bi zuwa kasuwannin duniya.
Ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya na da ɗimbin arzikin man fetur, lamarin da ya sa rashin kai man yankin kasuwar duniya, ya haifar da gagarumin giɓi a man da ake tarawa a kasuwar.
Iran ɗin ta kuma riƙa ƙaddamar da hare-hare kan rumbunan ajiyar man fetur na ƙasashe maƙwabtanta.
Iran ta kashe mutumin da take zargi da yi wa Isra'ila leƙen asirin
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin ƙasar Iran sun sanar da kashe wani mutum mai suna Kourosh Keyvani, bisa zargin yi wa Isra'ila leƙen asiri.
Kamfanonin dillancin labaran cikin gidan Iran sun ce an aiwatar da hukuncin ne a safiyar yau, ranar Laraba, 17 ga Maris.
Sai dai ba a fitar da cikakkun bayanai game da shari’ar ko yadda aka gudanar da ita ba.
Kamfanin dillancin labaran Fars, wanda ke da alaƙa da rundunar juyin juya hali ta ƙasar, ya ce an kama Keyvani ne a ranar 16 ga Yuni, a lokacin da yaƙin tsakanin ƙasar da Isra'ila da Amurka ta kai kwanaki 12.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na ci gaba da zargin gwamnatin Iran da take haƙƙin waɗanda ake tuhuma, inda suke cewa ba a ba su cikakkiyar damar kare kansu a kotu ba.
Sun kuma yi zargin cewa ƙasar na ƙara yawan hukuncin kisa ne domin tsoratar da masu adawa da kuma takaita ‘yancin faɗar albarkacin baki a cikin al’umma.