Wace riba Najeriya za ta iya samu daga yaƙin Iran da Amurka?

Asalin hoton, Getty Images
Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila a ɗaya gefen na ci gaba da haifar da tashin farashin makamashi a faɗin duniya.
A yanzu haka farashin man fetur ya zarta dala 100 kan kowace ganga.
Iran ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya mafiya arzikin man fetur, sannan take da iko da muhimmayar hanyar jigilar man fetur na yankin Gabas ta Tsakiya, wato mashigar Hormuz.
A matsayin martanin hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata, Iran ta rufe mashigar ta Hormuz, wanda kashi 20 cikin 100 man fetur na iskar gas ɗin duniya ke bi ta wurin.
Ta mashigar ne duka man fetur da iskar gas na ƙasashen yankin Gulf da na Gabas ta Tsakiya ke bi zuwa kasuwannin duniya.
Ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya na da ɗimbin arzikin man fetur, lamarin da ya sa rashin kai man yankin kasuwar duniya, ya haifar da gagarumin giɓi a man da ake tarawa a kasuwar.
Iran ɗin ta kuma riƙa ƙaddamar da hare-hare kan rumbunan ajiyar man fetur na ƙasashe maƙwabtanta.
Ta yaya hakan zai shafi Najeriya?

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya/X
Najeriya kan gaba a yawan arzikin man fetur a nahiyar Afirka.
Ƙasar - wadda ke yammacin Afirka - na samun fiye da kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta daga man fetur da iskar gas da take sayarwa a kasuwannin duniya.
Galibi kuɗaɗen da Najeriya ke amfani da su a kasafin kuɗinta tana samu ne daga arzikin man fetur da take sayarwa
Don haka ne ma a duk lokacin da shugabannin ƙasar ke gabatar da kasafin kudin ƙasar, sukan yi ƙiyasin kuɗin da ƙasar za ta samu daga man da take sayarwa.
A watan Disambar bara, lokacin da shugaban ƙasar, ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2026, ya ƙiyasta shi kan dala 64.85 kowacce gangar mai da ƙasar za ta sayar.
To sai dai a yanzu da farashin kowace gangan ya haura dala 100, masana tattalin arziki na ganin hakan riba ce ga Najeriyar, wadda a yanzu farashin ya zarta ƙiyasinta.
Ta yaya Najeriya za ta amfana da hakan?
Farfesa Ahmed Adamu, ƙwararren masanin tattalin arzikin man fetur da Iskar gas kuma malami a Jami'ar Philomath da ke Abuja, ya ce ƙasar za ta samu gagarumar riba kasancewar an samu ƙari akan abin da aka yi hasashe na farashin kowace ganga.
''A lokacin kasafin kuɗin an ƙayyade farashin mai kan dala 64.85 kowace ganga, amma yanzu ta haura dala 100 ka ga kenan riba mai yawa ƙasar za ta samu'', in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Masanin tattalin arzikin man fetur ɗin ya ƙara da cewa a yanzu kowace ganga da ƙasar za ta sayar za ta samu ribar kusan dala 36.
Kasafin kuɗin ƙasar ya kuma ƙiyasta haƙo ganga miliyan 1.8 a kowace rana.
''Kenan a kowace rana Najeriya a yanzu na samun ribar dala miliyan 64, ƙari a kan abin da ta yi hasashen samu a kowace rana, sanadin sayar da mai'', in ji malamin jami'ar.
Hakan zai sa gwamnati ta rage cin bashi?
A lokacin gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2026, Najeriyar ta yi hasahen samun giɓin naira kusan tiriliyan 23, wani abu da ke nufin ƙasar za ta karɓo bashi domin cike shi.
Don haka ne Ahmed Adamu ya ce ƙasar za ta iya samun raguwar ciyo bashi sakamakon gwaggwaɓar ribar da take samu a kowace rana a yanzu, sakamakon wannan yaƙi na Iran.
''Idan aka tafi a haka kenan kusan kullum tun da ka fara yaƙin nan Najeriya na samun ribar dala miliyan 64 ƙari a kan abin da ta yi hasashen samu a kowace rana''.
"A yanzu kusan kwana 17 tun bayan fara wannan yaƙi, idan aka haɗa wannan riba, kenan ba ƙananan kuɗaɗe take samu ba, wanda kuma hakan zai sa a rage yawan kuɗin da take hasashen karɓo bashin ko ma ta fasa karɓowa'', in ji shi.
Masanin tattalin arzikin ya kuma ce ƙasar za ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga ta yadda jihohin ƙasar da ƙananan hukumomi za su samu ƙarin kuɗaɗen da suka samu daga kasonsu na tarayya.

Asalin hoton, Getty Images
Ta yaya talakawan Najeriya za su amfana?
Farfesa Ahmed Adamu ya ce talakawan Najeriya za su amfana da wannan riba ne kawai idan gwmanatin ƙasar ta yi tsari mai kyau.
''Ribar da talakawan ƙasar za su samu ya dogara ne da irin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya da na jihohin ƙasar suka yi, abin da za su yi da kuɗaɗen'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa in dai gwamnati ta yi amfani da ribar ta hanyar da ta dace, to lallai ƴan ƙasar za su amfani.
''Idan kuma aka sauya akalarsu ta wata hanya daban, kamar ta almundaha to ka ga talakawa ba za su amfana ba'', in ji shi.
Don haka ye ya bai wa gwamnati shawarar gina abub uwan more rayuwa da za su taimaka wa talakawa, musamman samar da hanyoyin sufuri na zamani, wanda na man fetur ba, ta yadda talakawa za su samu saƙin sufuri.
''Musamman yanzu da gwamnati ba ta biyan tallafin man fetur, to ya kamata ta ɓullo da wasu tsare-tsare na rage wa talakawa tsadar man fetur, ko rage dogara da shi a cikin ƙasar'', in ji shi.
Najeriya za ta iya ƙara yawan man da tek haƙowa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A lokacin gabatar da kasafin kuɗin Najeriya na 2026 an tsara cewa ƙasar za ta riƙa haƙo ganga miliyan 1.8 a kowace rana.
To amma yanzu ana samun giɓin a kasuwannin duniya saboda rufe mashigar Hormuz.
Hakan ne ya sa wasu ke ganin Najeriyar mai ɗimbin arzkin man ta samu damar ƙara yawan man da take haƙowa a kowace rana.
Farfesa Ahmed Adamu ya ce Najeriya za ta iya ƙara yawan man da take haƙowar, musamman saboda rufe mashigar Hormuz.
''Kusan ganga miliyan 20 ne ke bi ta mashigar Hormuz zuwa kasuwannin duniya a kowace rana, to yanzu da aka datse manyan ƙasashen da ke sayen man irinsu China da Indiya ba za su so dakatar da sayen man ba''.
Masanin harkokin man fetur din ya ce kodayake ƙasashen biyu za su so fi son man Gabas ta Tsakiya, saboda araharsa a wajensu, amma babu yadda za su yi dole nemi mai tsadar tun da ya zame musu dole sai sun saya.
''Don haka Najeriya na fitar da ganga miliyan 1.8 a kowace rana, idan ka kwatantan da ganga miliyan 20 da ake hana wucewa a kowace rana ta mashigar Hormuz, Najeriyar na buƙatar ƙara man da take fitarwar'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa ya kamata a ce Najeriya a yanzu na fitar da ganga miliyan 2.5 a kowace rana, domin cin ribar wannan dama da aka samu.










