Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 01/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 01 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga AishaBabangida da Haruna Kakangi

  1. Hare-haren Rasha sun yi ajalin mutum huɗu a Ukraine

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ukraine ta ce hare-haren da Rasha ta kai a yankin Cherkasy na tsakiyar kasar sun kashe mutane hudu tare da raunata wasu.

    Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Zelensky ke shirin tattaunawa da Amurka don kokarin sake farfaɗo da tattaunawa da Rasha.

    Moscow ta yi watsi da shawarar da Ukraine ta bayar na tsagaita wuta domin Easter wanda zai kai ga dakatar da hare-haren da ake kai wa kayayyakin samar da makamashi.

  2. Gobara ta kashe mutane da dama a Burundi

    Rahotanni daga Burundi na cewa mutane da dama ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani dakin ajiyar kayayyakin sojoji da ke Bujumbura da yammacin jiya Talata.

    Gobarar ta haifar da fashewar wasu abubuwa, yayin da makaman da ake ajiye da su suka farfashe.

    Jami’an soji da ‘yan sanda sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, lamarin ya shafi unguwanni da dama, inda ɓaraguzai suka yi ta faɗawa kan gidajen alumma.

    Rahotanni na cewa daruruwan mutane sun jikkata. Rundunar sojin Burundi ta ce wutar lantarki ce ta haifar da gobarar.

  3. Hannun jari ya tashi bayan Trump ya ce yaƙin Iran ya kusan ƙarewa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasuwannin hannayen jari na duniya sun tashi sosai bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake nanata cewa yaƙin da ake yi da Iran zai iya zuwa karshe a cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa, ko da kuwa an cimma yarjejeniya ko ba a cimma ba.

    Kasuwannin Frankfurt da Landan da Paris sun karu da kusan kashi biyu cikin dari.

    Tun da farko, Seoul ta ce ta samu karuwar kashi takwas cikin dari, yayin da ta Tokyo ta karu da kashi biyar cikin dari.

    Farashin gwal ma ya karu, yayin da farashin mai kuma ya ragu.

    Farashin mai nau'in Brent ya yi ƙasa da fiye da kashi uku, wanda ya sa ya kai ƙasa da dala 100 na wani ɗan lokaci.

    Trump ya ce Washington ta cimma burinta na yaki, duk da gaza kwace iko da mashigar Hormuz.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya sake musanta cewa suna wata tattaunawa da Washington.

  4. Inec ta ce ba David Mark ne shugaban jam'iyyar ADC ba

    ..

    Asalin hoton, David Mark/Facebook

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC tare da Abdulra'uf Aregbesola a matsayin sakatare janar na jam'iyyar daga na'urarta.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Inec ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi'u Gombe.

    A wani hukunci da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 12 ga watan Maris ɗin 2026, kotun ta nemi dukkannin ɓangarorin da su jira hukuncin babbar kotun tarayya.

    Hukumar ta zaɓe ta ce sakamakon hukuncin na kotun ɗaukaka ƙarar ne ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga lauyoyin ɓangarorin biyu masu taƙaddama da juna a kotu, inda ɓangaren David Mark ya nemi ka da ta amince da ɓangaren Nafi'u Gombe sannan shi ma lauyoyin Gombe suka nemi a cire sunan David Mark daga na'urarta ta jerin shugabannin jam'iyyun da Inec ta amince da su.

    Rikicin dai ya samo asali ne a watan Yulin 2025 lokacin da shugabancin jam'iyyar ta ADC ya yi murabus inda kuma David Mark ya zamo shugaba.

    Sai dai kuma tsohon mataimakin jam'iyyar, Nafi'u Gombe ya ƙalubalanci zaɓen inda ya dage cewa dole ne a samar da shugabanci ta hanyar da kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tsara.

  5. China da Pakistan na shirin shiga tsakani domin kawo ƙarshen yakin Iran

    Ƙasashen China da Pakistan sun miƙa wani daftari mai ƙunshe da buƙatu biyar na ƙoƙarin ganin an kawo ƙrshen yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da suka hada da buƙatar tsagaita wuta da kuma buɗe mashigar Hormuz.

    An samar da daftarin ne bayan ministan harkokin wajen Pakistan ta je Beijing domin neman goyon bayan China wajen shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin.

    Ministan harkokin wajen China ya ce ƙasashen guda biyu na wani shirin samar da sabbin hanyoyin cimma zaman lafiya.

  6. Yaƙin Iran zai iya janyo wa Amurka asarar dala biliyan biyu a kullum

    Yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran ka iya janyo wa Amurkar kashe aƙalla dala biliyan biyu a kullum, kamar yadda ƙwararrun da ke bibiyar al'amarin ta fuskar tattalin arziƙi suka shaida wa BBC.

    Stephen Savell, darekta a shirin Kashe Kuɗade a lokacin yaƙi a jami'ar Brown University, ya ce tsakanin makamai da kashe-kashe kan sojoji da asarar kadarorin Amurka da sauran abubuwa, yaƙin kawo yanzu ya laƙume wa Amurka biliyoyin daloli.

    "A kullum yaƙin na ƙara girman yawan bashin da ke kan gwamnati," in ji Savell.

    Hedikwatar tsaro ta Amurka, Pentagon, a farkon watannan ta shaida wa ƴan majalisar dokokin ƙasar cewa kwanaki shida na yaƙin ya janyowa Amurka asarar dala biliyan 11 da miliyan 300, in ji wani rahoton kafafen watsa labaran Amurka.

  7. Mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a kulle ga "maƙiya" Iran - IRGC

    Dakarun juyin juya hali na Iran, IRGC ta ce mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe ga ƙasashe "maƙiyansu".

    Yayin wani jawabi a gidan talbijin na ƙasar, IRGC ta ce mashigar Hormuz na ƙarƙashin ikon rundunar ruwa ta dakarun.

    Kafin nan dai Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Social Truth cewa Iran ta nemi a tsagaita wuta.

    "Za mu duba mu gani lokacin da Hormuz ya zama a buɗe kuma za a iya wucewa. Kafin nan za mu ci gaba da yi wa Iran luguden wuta domin ganin bayanta ko kuma mayar da ita zamanin jahiliyya."

    Sai dai kuma ma'aikatar harkokin waje ta Iran ta musanta ikrarin na Trump cewa Iran ta nemi a tsagaita wuta.

  8. Shugabannin Turai sun dage kai da fata cewa babu ruwansu da yaƙin Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen Turai na ci gaba da jaddada cewa ba babu ruwansu da yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran suna mai dagewa cewa ba za su bari a ja su cikin yakin ba, duk da matsin lamba da ke ƙaruwa daga waje da kuma fargabar rikice-rikicen duniya.

    A lokaci guda, kalaman Donald Trump cewa yana tunanin ficewa daga NATO sun zama babban labari a kafafen yada labarai na Turai, amma shugabannin siyasa a nahiyar na nuna taka-tsantsan tare da yin shiru a bainar jama'a.

    Dalilin haka shi ne tsoron abin da ka iya faruwa idan Amurka ta fice daga NATO. Wannan mataki na iya zama babbar illa ga tsaron Turai, ganin yadda har yanzu ƙasashen nahiyar ke matukar dogaro da Amurka a ɓangarori da dama, musamman tattara bayanan sirri da jagorancin ayyukan soja, da kuma kariyar sararin samaniya.

    Ko da yake ƙasashen Turai, ciki har da Birtaniya, sun sha yin magana kan bukatar ƙarfafa rawar da za su taka a cikin ƙawancen tsaro domin rage dogaro da Amurka, har yanzu wannan buri bai cika ba.

    Amurka ita ce mafi karfi a NATO, kuma tana da gagarumin tasiri a dukkan matakan tsaro na ƙungiyar.

  9. Gwamnatin Najeriya ta ayyana Juma'a da Litinin ranakun hutu

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Juma'a da Litinin a matsayin ranakun hutun Easter.

    Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

  10. Birtaniya za ta tattauna da ƙasashe kusan 35 kan buɗe mashigar Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Birtaniya ta ce za ta karbi bakuncin wani taro na kasashe kusan talatin da biyar a wannan makon, domin tattauna hanyoyin sake bude mashigar Hormuz mai mahimmanci da zarar an kawo ƙarshen yakin da ake yi da Iran.

    Firaminista Keir Starmer ya ce za su duba dukkan matakan da za a dauka don dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tabbatar da tsaron jiragen da suka makale.

    Ya ce wannan ba yaƙin mu ba ne, kuma ba za mu bari a janyo mu cikin shi ba, yin hakan ba zai amfani ƙasarmu ba.

    Iran ta toshe yawancin jiragen da ke fitar da makamashi ta mashigar, lamarin da ya sa farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi.

    Akwai fargabar cewa Shugaba Trump zai iya kawo karshen yakin ba tare da yin nasara wajen sanya Iran ta buɗe mashigar.

  11. Iran ta musanta iƙirarin Trump na neman tsagaita wuta

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Shugabannin Iran sun ƙaryata iƙirarin da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi cewa Iran ta nemi a tsagaita wuta a rikicin da ke ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya

    Iran ta bayyana wannan ikirarin a matsayin "ƙarya mara tushe" kuma ba shi da wata hujja, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya fadi a yau.

    Trump ya ce shugaban Iran na “zaɓaɓɓe” ne ya nemi a dakatar da yaƙin, amma Iran ta ƙaryata hakan gaba ɗaya.

  12. Me ke faruwa a Jos?

    Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

    Asalin hoton, X/Caleb Mutfwang

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

    Ana zaman ɗarɗar a birnin Jos na jihar Filato bayan wasu rahotanni da ke cewa an samu hargitis bayan sassauta dokar hana zirga-zirga ta kwana biyu da aka ƙaƙaba sanadiyyar wani mummunan hari da wasu ƴan bindiga suka kai.

    A ranar Lahadi ne wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari a Unguwar Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, inda hukumomi suka ce hakan ya yi sanadiyyar rayukan aƙalla mutum 20.

    Wasu faya-fayen bidiyo da aka riƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda tururuwar mutane ke guje-guje, inda wasu suka bayyana hakan a matsayin wani sabon tashin hankali a safiyar yau Laraba.

    Sai dai a tattaunawarta da BBC, kwamishinar yaɗa labaran jihar Filato, Joyce Ramnap ta ce an shawo kan ƴar hatsaniyar da ta so ta tashi a safiyar ta Laraba bayan ɗage dokar hana zirga-zirga.

    Ta ce: "Abin da ya faru shi ne wasu ɓata-gari ne da suka ga an ɗage doka suka so su shiga kasuwa su yi fashi, to masu shaguna a kasuwar sai suka fara gudu domin tsare dukiyarsu a cikin kasuwa, to amma da aka ga suna ta gudu sai aka fara yaɗa jita-jita, hakan ne ya kawo wani ɗan tashin hankali da safiyar yau".

    Sai dai ta ce jami'an tsaro sun hanzarta wajen daƙile duk wani abu da zai iya haifar da ƙazancewar lamarin.

    Ta ƙara da cewa a yanzu hankula sun kwanta a garin na Jos, babban birnin jihar Filato.

    Amma kwamishinar ta bayyana cewa jami'an tsaro na nazari, domin ganin ko akwai buƙatar a sake mayar da dokar hana zirga-zirga domin daƙile duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali.

    Filato na cikin jihohin arewa ta tsakiyar Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro mai nasaba da addini da ƙabilanci a tsawon shekaru da dama.

  13. Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila da makwabtanta na yankin Gulf

    Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka zuwa Isra'ila da makwabtanta na yankin Gulf, a matsayin martani ga hare-haren Amurka da Isra'ila.

    An ji kararrakin makamai masu linzami guda hudu a Isra'ila a safiyar yau kuma an samu rahotannin cewa lamarin ya rutsa da mutane da dama, kuma ya yi ɓarna a birnin Tel Aviv.

    Mutum daya a Hadaddiyar Daular Larabawa ya mutu bayan ɓaraguzai sun faɗa kan shi.

    Kuwait ta bayar da rahoton gobara a wani wurin ajiyar mai na filin jirgin sama, ita kuma Bahrain a wata cibiyar kasuwanci.

    Saudiyya ta ce ta kakkabo jiragen sama marasa matuki daga Iran.

  14. Rasha ta yi allawadai da harin sama da ya lalata cocin Orthodox a Tehran na Iran

    ....

    Asalin hoton, Russian Embassy in Iran

    Ofishin jakadancin Rasha da ke Tehran ya bayyana cewa wani harin sama da aka kai a ranar Laraba ya lalata wani ginin cocin Orthodox na Rasha a babban birnin Iran, ba tare da samun rahoton asarar rayuka ba.

    A cikin sanarwar da ofishin jakadancin ya wallafa a shafin sada zumunta na X, ya ce an kai hare-hare guda biyu a kusa da Cocin St. Nicholas da ke Tehran.

    Sanarwar ta ce harin ya lalata babban ginin cocin da gidan baƙi na agaji da kuma wasu kayan aiki na fasaha.

    Hotunan da ofishin jakadancin ya fitar sun nuna yadda wani ɓangare na rufin cocin ya rushe, tare da gilashin tagogi da suka fashe.

    Ofishin jakadancin ya jaddada cewa wannan hari ya faru ne a lokacin da Kiristoci ke gudanar da ɗaya daga cikin muhimman bukukuwansu, wato Easter, yana mai cewa sakamakon wannan hari na soji daga Amurka da Isra’ila, mabiya addinin Orthodox a Iran sun rasa damar gudanar da ibadarsu a cocin.

    An bayyana cewa ginin Cocin St. Nicholas ɗin wani ɗan asalin Rasha, Nikolai Markov, ne ya zana tare da tsara ginin kuma yana cikin jerin gine-ginen al’adun ƙasa na Iran.

    Haka kuma, ofishin jakadancin Rasha ya ce yana yin allawadai da abin da ya kira ci gaba da hare-haren Amurka da Isra’ila a Iran, waɗanda ya ce suna ƙara kai hari kan cibiyoyin fararen hula da wuraren addini da al’adu.

  15. Kotu ta ƙi bayar da belin El-Rufai a yau Laraba

    ....

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kaduna ba ta yanke hukunci kan buƙatar beli da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya gabatar ba inda ta ce za ta sanar da matsayarta a ranar 14 ga watan Afrilu.

    Wannan na zuwa ne bayan da kotun ta saurari hujjoji daga ɓangaren masu kare El-Rufai da kuma ɓangaren masu ƙara inda kowanne ɓangare ya gabatar da dalilansa kan ko ya dace a bayar da beli ko akasin haka.

    Bayan kammala sauraron, alƘalin ya bayyana cewa akwai buƘatar ƙarin nazari kan bayanan da aka gabatar kafin yanke hukunci na karshe.

    Abin da ya ja hankalin masu lura da al’amuran siyasa shi ne yadda ranar da aka sanya domin yanke hukuncin ta zo daidai da lokacin babban taron jam’iyyar ADC na kasa.

    Haka kuma, kotun ta shirya cigaba da sauraron ƙara tsakanin El-Rufai da Gwamnatin Tarayya a ranar 23 ga Afrilu, 2026.

    A makon da ya gabata ne hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban mai shari’a Rilwan M. Aikawa kan tuhume-tuhume guda 10 da suka haɗa da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma halasta kuɗaɗen haram

  16. Ministocin Bola Tinubu da suka ajiye aiki 'don tsayawa takara'

    ....

    Asalin hoton, FB/Multiple

    Zuwa yanzu ministoci uku ne suka yi murabus, tun bayan umarnin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar, ga masu sha'awar takarar siyasa a ƙasar, na su ajiye muƙamansu na gwamnati kafin 31 ga watan Maris, wa'adin da ya ƙare a ranar Talata.

    Sai dai har yanzu akwai wasu ministocin da aka yi tsammanin za su ajiye muƙaman nasu, amma ba a ga sun yi hakan ba, duk kuwa da cewa an ga alamun suna da sha'awar yin takara a babban zaɓen ƙasar na 2027.

    Amma baya ga ministoci, akwai kuma wasu mashahuran masu riƙe da muƙaman siyasar da suka yi murabus daga gwamnatin ta Tinubu gabanin cikar wa'adin na ranar Talata.

    Shin waɗanne ministoci da kuma masu riƙe da muƙaman siyasa ne suka ajiye muƙaman zuwa yanzu?

  17. Trump ya ce yana duba yiwuwar ficewar Amurka daga NATO - Rahoto

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana nazarin yiwuwar janye Amurka daga ƙungiyar tsaro ta NATO, kamar yadda ya bayyana a wata hira da ya yi da jaridar The Telegraph.

    Jaridar ta ruwaito cewa Trump ya bayyana ƙungiyar a matsayin 'kyanwar lami' yana mai cewa ba ta da ƙarfi kamar yadda ake tsammani. Haka kuma ya yi iƙirarin cewa Britaniya ba ta sojojin ruwa masu ƙarfi

    Da aka tambaye shi ko zai sake duba matsayar Amurka kan kasancewa cikin NATO bayan rikicin Gabas ta Tsakiya, Trump ya ce: “Eh, zan iya cewa ya wuce ma a sake tunani...”

    Ya ƙara da cewa: “Ban taɓa yarda da NATO ba. Na daɗe da sanin cewa ƙungiyar ba ta da ƙarfi, kuma shugaban Rasha, Vladimir Putin ma ya san haka.”

    Trump ya kuma soki Birtaniya, yana cewa: “Ba ku da rundunar ruwa mai ƙarfi. Kun tsufa, kuma kuna da jiragen da ba sa aiki yadda ya kamata,” yana nuni da halin da rundunar ruwan ƙasar ke ciki.

  18. 'Birtaniya ba za ta shiga yaƙi da Iran ba duk da matsin lambar Trump'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce ƙasarsa ba za ta shiga yaƙi da ƙasar Iran ba, duk da matsin lambar da yake fuskanta daga shugaban Amurka, Donald Trump.

    Da yake magana a wani taron manema labarai a yau, Starmer ya bayyana cewa akwai matsin lamba mai yawa a kansa domin ya sauya matsayinsa kan shiga yaƙin, amma ya jaddada cewa ba zai canza wannan matsaya ba.

    Ya ƙara da cewa a matsayinsa na Firaminista, zai ci gaba da yanke shawara ne bisa muradun ƙasar Birtaniya.

    Lokacin da aka tambaye shi ko yana ƙara kusantar Turai sakamakon dangantakar da ta yi tsami da Trump, Starmer ya ce ba zai zaɓi tsakanin Amurka da Turai ba.

    Ya ce, “Yana da muhimmanci a gare mu mu ci gaba da samun kyakkyawar alaƙa da Amurka da kuma Turai baki ɗaya.”

    A nasa ɓangaren, Trump ya shaida wa jaridar The Telegraph cewa yana duba yiwuwar ficewar Amurka daga ƙungiyar NATO da muhimmanci.

    Trump ya sha sukar NATO da kuma Birtaniya kan rashin shiga yaƙin da Amurka ke yi da Iran.

  19. As sake mayar da El-Rufai kotu don sauraron neman beli

    ...

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya sake gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna domin ci gaba da sauraron buƙatarsa ta neman beli.

    Tsohon gwamnan ya isa kotun da misalin ƙarfe 9 na safe a ranar Laraba, cikin tsauraran matakan tsaro.

    Ci gaba da sauraron shari’ar ya biyo bayan ɗage zaman da mai shari’a, Rilwan Aikawa ya yi a ranar Talata, sakamakon wasu sabbin matakan shari’a tsakanin ɓangaren masu kare shi da kuma masu gabatar da ƙara.

    Lauyoyin El-Rufai, ƙarƙashin jagorancin Ubong Akpan, sun fara shigar da buƙatar neman mai shari’ar ya janye daga shari’ar bisa zargin nuna son kai, amma daga baya suka janye wannan buƙata, lamarin da ya janyo jinkiri a tafiyar da shari’ar.

    A ɓangaren masu gabatar da ƙara kuwa, sun shigar da hujjar da ke adawa da bayar da belinsa wanda ya bar ɓangaren masu kareEl-Rufai da ƙarancin lokaci na mayar da martani, abin da ya sa aka ɗage shari’ar zuwa Laraba domin ci gaba.

    A makon da ya gabata ne hukumar ICPC ta gurfanar da shi a gaban mai shari’a Rilwan M. Aikawa kan tuhume-tuhume guda 10 da suka haɗa da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma halasta kuɗaɗen haram

  20. An sassauta dokar hana zirga-zirga a unguwar Rukuba da ke Jos

    ....

    Asalin hoton, X/Caleb Mutfwang

    Gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana zirga-zirga da aka sanya a Unguwar Rukuba ta Jos ta arewa bayan harin ranar 29 ga Maris da ya kashe aƙalla mutane 27.

    “An fara wannan sassautawar ne daga ranar 1 ga Afrilu, 2026, inda ake ba da damar zirga-zirga daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa 3:00 na yamma a kullum. An yi kira ga mazauna unguwar da su yi amfani da wannan lokacin wajen gudanar da ayyukan da suka dace da doka tare da bin ƙa’idojin tsaro,” in ji kwamishinan labarai na jihar, Joyce Ramnap.

    Gwamnatin jihar ta ce jami’an tsaro za su ci gaba da gudanar da sa ido da sintiri don tabbatar da zaman lafiya da hana ɓarkewar tashin hankali.

    Da farko dai, gwamnati ta sanar da sanya dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 48 bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a Angwan Rukuba.

    Sai dai mazauna unguwar, cikin fushi, sun karya dokar hana zirga-zirgar inda suka fita kan tituna don zanga-zangar nuna rashin jin daɗi da kuma neman gwamnati ta ɗauki mataki kan tashin hankali da ake fuskanta a jihar a kai a kai.

    Filato, wanda ke tsakiyar Najeriya, na fuskantar rikice-rikice akai-akai tsakanin makiyaya da manoma kan haƙƙin amfani da ƙasa da ruwa.

Trending Now