Ministocin Bola Tinubu da suka ajiye aiki 'don tsayawa takara'

Asalin hoton, FB/Multiple
Zuwa yanzu ministoci uku ne suka yi murabus, tun bayan umarnin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar, ga masu sha'awar takarar siyasa a ƙasar, na su ajiye muƙamansu na gwamnati kafin 31 ga watan Maris, wa'adin da ya ƙare a ranar Talata.
Sai dai har yanzu akwai wasu ministocin da aka yi tsammanin za su ajiye muƙaman nasu, amma ba a ga sun yi hakan ba, duk kuwa da cewa an ga alamun suna da sha'awar yin takara a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Amma baya ga ministoci, akwai kuma wasu mashahuran masu riƙe da muƙaman siyasar da suka yi murabus daga gwamnatin ta Tinubu gabanin cikar wa'adin na ranar Talata.
Shin waɗanne ministoci da kuma masu riƙe da muƙaman siyasa ne suka ajiye muƙaman zuwa yanzu?
Yusuf Tuggar - Bauchi
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya sanar da ajiye muƙamin nasa ne a ranar Litinin, inda ya bayyana aniyarsa ƙarara cewa yana son ya yi takarar gwamnan jihar Bauchi ne.
Masu magana da yawun ministan Kimiebi Ebienfa da Alkasim Abdulkadir, sun tabbatar da cewa mai gidan nasu, ya ajiye muƙamin.
"Minista yana son yin takarar gwamnan jihar Bauchi ne," in ji Abdulkadir.
An haifi Tuggar ne a shekarar 1967, a ƙaramar hukumar Gamawa a jihar Bauchi.
Mahaifinsa Abubakar Tuggar, tsohon ɗanmajalisa ne da ya wakilci Gamawa a majalisar wakilai ta Najeriya a jamhuriya ta biyu.
Tuggar, na da digiri a fannin hulɗar ƙasa da ƙasa daga jami'ar Amurka, ya kuma yi karatun digirinsa na biyu a jami'ar Cambridge duk a wannan fannin.
Kafin ya riƙe muƙamin minista, Tuggar ya wakilci ƙaramar hukumar Gamawa a majalisar wakilai ta tarayya tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011, ya kuma taɓa zama jakadan Najeriya a Jamus tsakanin 2017 zuwa 2023.
Ya yi takarar gwamnan jihar Bauchi har sau biyu amma bai samu nasara ba, inda yanzu zai sake yi a karo na uku.
Yusuf Sununu - Kebbi
Tinubu ya fara naɗa Yusuf Sununu a matsayin ƙaramin ministan ilimi a Najeriya ne, kafin daga bisani ya koma ƙaramin ministan jin ƙai.
An haife shi a ƙaramar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi, kuma ƙwararren likita ne da ya yi karatu a jami'ar Maiduguri.
Sununu ya fara siyasa ne a shekarar 2019, bayan ajiye muƙaminsa a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke jihar Kebbi.
Ya yi takarar ɗanmajalisar tarayya a mazaɓar Ngaski/Shanga/Yauri a shekarar 2019 kuma ya ci zaɓen, inda ya sake yin nasara a shekarar 2023 kafin daga baya Tinubu ya naɗa shi minista.
Ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin lafiya na majalisar wakilai ta tarayya.
Zuwa yanzu ba a bayyana kujerar da yake son takara ba.
Sanata Saidu Alkali - Gombe
Ministan sufurin Najeriya, Sanata Sa'idu Alkali ya ajiye muƙaminsa ne a ranar Talata, inda ya zama minista na uku da ya ɗauki irin wannan matakin kafin ƙarewar wa'adin da shugaba Tinubun ya bayar.
Alƙali, haifaffen jihar Gombe ne, kuma ya ce ya ɗauki matakin ne bayan ganawa da shugaba Tinubu a Abuja, kamar yadda kakakin shugaban ya bayyana.
Alƙali tsohon Sanata ne da ya wakilci mazaɓar Gombe ta tsakiya, kuma ana sa ran zai yi takarar kujerar gwamnan jihar a 2027, domin ya gaji Gwamna Inuwa Yahaya da wa'adinsa zai ƙare a watan Mayun 2027.
Wasu masu riƙe da muƙamai da suka yi murabus a gwamnatin Tinubu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Baya ga ministoci akwai wasu masu riƙe da muƙaman siyasa da suka ajiye aikin domin takara a shekarar 2027. Daga cikinsu akwai:
Nasiru Gawuna: Ɗantakarar gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna ya ajiye muƙaminsa na shugaban gudanarwar bankin bayar da lamuni na Najeriya, da Tinubu ya naɗa shi.
Gawuna ya kuma fice daga jam'iyyar APC, inda ya koma jam'iyyar adawa ta ADC, inda ake hasashen zai yi takarar gwamnan jihar, bayan da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ma ya shiga ADCn.
Abdulrazak Namdas: Tinubu ya naɗa Namdas, ɗan jihar Adamawa a matsayin mamba a kwamitin zartaswar raya yankin Neja-Delta da ke wakiltar arewa maso gabas.
Namdas ya ce ya ajiye muƙamin ne saboda yana son yin takara a shekarar 2027.
Kafin wannan muƙamin, ya shafe shekaru a matsayin ɗanmajalisar tarayya, inda har ya taɓa neman muƙamin kakakin majalisar a shekarar 2019, inda daga baya ya janye wa Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayyar ƙasar.
Wasu rahotanni sun ce Namdas, yana son yin takarar gwamnan jihar Adamawa ne.
Nasir Ja'oji: Babban mataimaki na musamman ga shugaba Tinubu kan harkokin ƴanƙasa da shugabanci, Nasir Bala Ja'oji ya yi murabus a ƙarshen satin da ya gabata, inda ake sa ran zai yi takarar majalisar wakilai ta tarayya.
A cikin wasikar ajiye aikin, ya miƙa godiyarsa ga shugaba Tinubu.






